Wednesday, 3 May 2017

Tarihin Yakin Hadejia da Gumel a 1872

A zamanin yake-yaken kasar hausa duk gabas da sokoto babu wata kasa mai karfi da yawan rundunar mayaka da sadaukai kamar kasar Hadejia, wannnan dalili yasa sauran kasashe suke shayin kasar Hadejia domin a wannan lokaci kasar Hadejia ta zama Dodo.

A lokacin Sarkin Hadejia Haru mutanan kasar Gumel suke zuwa garuruwan da suke makwabtaka da Hadejia suke kwacewa mutane kaya sannan suna kaiwa wasu kyauyuka hari, har abin yayi yawa da Sarkin Hadejia Haru yaji wannan labari sai ya aikawa Sarkin Gumel Abdu Jatau amma basu dena.

Mai makon ma su bari sai Sarkin Gumel yayi katobara ya aikowa Sarkin Hadejia cewa ba kai hari ba, Sarkin Hadejia ka shirya ganin zuwa da kaina, da Sarkin Hadejia yaji wannan magana ta Sarkin Gumel sai yace a mayarmasa da amsa cewa "bai isa karo dashi ba wannan dalili ne ma yasa duk irin hare-haren da yake kawowa kyauyukan Hadejia bai kulashi.
To amma tinda ya ga zai iya fada da Hadejawa to ga Galadiman Hadejia nan ma ya ishehi fada harma yafi. Aka tada jakada yakai wannan amsa zuwa ga Sarkin Gumel"

Da jin wannan amsa ta Sarkin Hadejia sai Sarkin Gumel ya shiga shirin yaki da Hadejia, bayan ya kwashe wasu kwanaki yana shiri, sai da ya gama shirin sa kaf sai yasa rana ya fito ya nufo Hadejia.

Da Sarkin Hadejia Haru ya sami labari cewa Sarkin Gumel Abdu Jatau ya taho Hadejia da yaki sai ya cewa Galadiman Hadejia Yakuba ya shirya da jama'arsa yaje ya tari Sarkin Gumel ya yi fada dashi, idan kuma bai fito ba to ya wuce har gidan sa can Gumel ya yake shi sannan kuma ya ci garin da yaki, sannan ya nuna masa fifikon dake tsakanin Hadejia da Gumel.

Da Sarkin Hadejia Haru ya bawa Galadima Yakuba wannan yakin nan da nan Galadima Yakuba ya shirya ya fita da rundunarsa ya nufi Gumel yana cikin tafiya ya je dai-dai kan hanyar da take zuwa wani gari da ake kira Mukaddari da Kaugama da Kudna a dai-dai bakin ruwan Kudina sai ga Sarkin Gumel da mutanansa da gamuwarsu batare da wani bata lokaci ba sai suka kaure da yaki.

Wannan yaki tsakanin Galadiman Hadejia Yakuba da Sarkin Gumel Abdu Jatau yaki ne mai zafi mai tsanani sosai, nan take Galadiman Hadejia Yakuba suka ci Gumulawa da yaki suka yi musu ba dadi suka kure su fata-fata korar har Kaugama har Zuburan har Kanya garin nan na iyaka da Madana.

A wannan yakin ne Galadiman Hadejia Yakuba ya kashe Sarkin Gumel Abdu Jatau sannan yasa Takobi ya sare kan Sarkin Gumel, sauran mutanansa da jama'ar Sarkin Gumel suka tsira da kyar.

Bayan an kashe Sarkin Gumel Galadiman Hadejia Yakuba yasa akawo masa dokin da Sarkin Gumel ya hau da Sirdin sa da Takobin sa da Mashin sa Rawanin sa ya taho dasu zai bawa Sarkin Hadejia. Daga nan Galadiman Hadejia ya gama hada komai, sai suka hau dawakan su suka taho Kaugama suka sauka domin su huta. Taskar Suleiman Ginsau

Ashe bayan Galadiman Hadejia ya yi shiri ya fita shima Sarkin Hadejia Haru sai yasa akayi Tambari aka busa Fare da Kugen yaki sai Sarki ya hau tare da mutanan fada ya fita ya bi bayan Galadima, sabida maganar da ya fadawa Galadima cewa "idan bai sami Sarkin a Hanya ba to ya wuce har Gumel ya sameshi a acan ya yakeshi kuma ya kama garin da yaki".

Sarkin Hadejia Haru yana zuwa Kaugama sai ya tarar da Galadima ya sauka yana hutawa da mutanansa, shi kuma Galadima yana jin kade-kaden Sarki sai suka hau dawakai sukaje suka tari Sarki Haru a bayan gari, da isowar Sarki sai Galadima ya fadi yayi gaisuwa sai Sarki ya cewa Galadima yaya na tarar da kai a Kaugama? Sai Galadima yace a cikin albarkacin Sarki ai na gama aikinka tin safe sai dai inda wani yanzu ma muci gaba, Galadima yasa aka kawo Kan Sarkin Gumel da Dokin Sarkin Gumel da Sardin sa da Takobin sa da Mashin sa da Rawanin sa aka nunawa Sarki. Anan Sarki ya nuna farin cikin sa sannan ya yi godiya ga Galadiman Yakuba.

Daga nan Sarkin Hadejia Haru ya bawa Galadiman Hadejia Yakuba Mashin da Takobin da Rawani. Doki da Sirdin kuma aka bawa Muhammad Damaturu, nan take Galadima da mutanansa suka yi godiya ga Sarki, gaba daya suka juyo gida suna annashuwa da farin ciki. Taskar Suleiman Ginau

Tin daga wannan lokacin wannan Mashi da Takubi da Rawanin suka zama abin gado a sarautar Galadiman Hadejia kuma haryanzu akwai wadannan kayan a gidan Galadiman Hadejia. An yi wannan yakin tsakanin Galadiman Hadejia Yakuba da Sarkin Gumel Abdu Jatau a shekara ta 1872.

A duk lokacin da ake wani bikin hawan Sallah ko wani babban biki Galadiman Hadejia wannan Mashin yake rikewa sannan ya rataya Takobin. Taskar Suleiman Ginsau

Sarkin Hadejia Haru ance yayi ta kawo Malaman Addini yana aji yewa a yawancin garuruwan kasar Hadejia domin a kara yada Ilmin Addini a kasar. A zamanin hasken makaranta ya karu dayawa sosai. Sannan mutane da yawa sun karu da karatun Kur'ani da Ilmin Addini sosai.

Sarki Hadejia Haru yana cikin irin wannan taimako nasa har Allah ya kawo masa Ajalinsa a shekara ta 1885.  Bayan mutuwar Sarkin Hadejia Haru sai aka nada babban dansa wato Sarkin Marma Muhammadu ya gajeshi.

Sarkin Marma Muhammadu ya dau wannan matsayin tin lokacin da Sarkin Hadejia Buhari ya kashe sarautar ba'a nada kowa ba sai shi. Amma shi Sarkin Marma Muhammad baije Marma ya zauna ba, ubansa Sarkin Hadejia Haru ya nadashi wannan sarauta domin mushimmancinta ne kawai a mai makon sarautar Chiromanci. Ba a bashi kasar Marma ya mulketa ba kamar yadda Sarkin Marma Larymore ya mulketa kuma ya zauna a cikin kasar tare da mutanansa. Taskar Suleiman Ginsau

Sarautar Chiromanci kuma aka nada Sarkiyo Sarki na Goma Muhammadu an nadashi sarauta a shekarar ta 1885. daga rasuwar mahaifinsa an ce Sarkin Hadejia Muhammadu manyan hakiman mahaifinsa da sauran mutanan fada ne suka nadashi kamar yadda mutanan "Sarkin Hadejia Buhari suka nadashi a farkon sarautarsa bayan sun nadashi sannan suka aika aka kirawo Galadima da sauran hakimai da manyan gari da zuwansu fada sai suka manyan bayin Sarki kuwannan su yana tsaye rike da Takubba duk wanda ya shigo fada sai yaga an nada Sarki gashi a zaune bisa gadon sarauta sannan sai ance dashi ya yi gaisuwa ya yi mubaya'a ga Sarki"

Duk da anyi haka a nadin Sarkin Hadejia Muhammadu amma ba'a su wani tashin hankaliba domin mutanan gari suna kaunarsa sosai. Taskar Suleiman Ginsau

Mu hadu a kashi na biyu. 2



No comments:

Post a Comment