Saturday, 27 May 2017

DANGANTAKAR HAUSAWA DA KABILAR YARBAWA A KASAR HADEJIA

A duk lokacin da aka sami mu'amala a
tsakanin mutane ko da ta dan takaitaccen lokaci ne dole a fahimci juna ta fuskar halaye ko dabi'u. Irin wannan fahimta ce ke haifar da mu'amala a tsakanin al'ummomin har ta kai ga kulla auratayya
a tsakaninsu. Haka kuma ana samun akasin haka.
Wato idan aka sami mummunar fahimta tsakanin al'ummomin biyu. Duk wadannan suna faruwa ne ta la'akarin da jama'a ke yi da halaye ko dabi'u na mafi yawan mutanen da suka kusanta da su.
Yawancin lokuta, halaye marasa kyau sun fi fitowaa fili, ba don komai ba sai don dan Adam ya fi saurin hango illa ko laifi fiye da abin yabo.
Hausawa sun ce, “laifi tudu ne.”

KABILAR YARBAWA A KASAR HADEJIA

Yarbawa dai kabila ce da ke amfani da
harshen Yarbanci wurin yin magana. Sukan kira kan su “Yoruba”. Hausawan Kasar Hadejia kuma suna kira su da Yarbawa. Namiji akan kira shi Bayarabe, mace kuma a kira ta Bayarba. Yarbawa dai mutane ne da ake samu galibi a kudancin kasar Nijeriya.

TARIHIN HADUWAR HAUSAWA DA KABILAR YARBAWA A KASAR HADEJIA.

Domin tabbatar da dugadugan kyallaro
wannan tarhin, ya zama tilas a waiwayi irin. hanyoyin da suka kawo Yarbawa Kasar Hadejia, Yarbawa sun shigo Kasar Hadejia a lokacin Sarkin Hadejia Usman a shekara ta 1925, sun shigo ne ta hanyar Jirgin Kasa dake garin Malam Madori a Kasar Hadejia. Dalilin shigowarsu kuwa shine kasuwanci, wasu daga cikinsu sun shigo da Goro Kasar Hadejia wasu kuma sun shigo da Na'urar daukar Hoto wato (Camera) wasu kuma sun ahigo da (Typewriter) wasu kuma da dama sun shigo ne neman aikin Birkilanci wato aikin Siminti.  Wasu kuma aikin Kafintane ya shigo dasu, harda masu gyaran Radio. Sannan Yarbawa suna siyan kayan abinci daga Kasar Hadejia zuwa Kasar su kamar Gishiri, Barkono, Alkama, Dawa, Gero, Masara, da dai sauransu. Wannan kenan a bangaran Kasuwanci. Dangantakar tsakanin Hausawan Kasar Hadejia da Yarbawa ta yadda har hausawan suka amince dasu amatsayin wadan da za suna yiwa hausawan aiki sannan su zama abokan kasuwancin su na yau da kullum.

A wani kaulin kuma Masana tarihi sun yi rubuce-rubuce da dama dangane da tarihin dangantakar Hausawa da Kabilar Yarbawa a kasar Hadejia Atuwo (1987) ya nuna cewa, ana iya kasa dalilan haduwar Hausawa da Yarbawa zuwa kashi hudu. Wadannan kuwa su ne: Gaba, da cinikayya, da addini.

ZUWAN TURAWA

Tun akarni na 13 zuwa na 18 sarakunan kasashen Hausa sun yi ta kai hare-hare a kasashen da Yarbawa suke zaune. Da yake al'adar kai hari ta tanadi kamo bayi don a sayar, "an sami shigowar Yarbawa kasar Hadejia" a matsayin bayin da aka
kamo. Duk wadannan abubuwan dai yaki ya haifar da su.
Ta haka ne Musulmi masu rinjaye da wadanda ba Musulmi ba marasa rinjaye mazauna kasar Hadejiya kafin mulkin mallaka suna ganin Sarkin Hadejiya nada mutukar kima kuma shugaba ne babba duk da yake suna da hakimai da dagatai masu jagorancinsu. Wanda kowa ce Kabila suna da Sarakunan su masu wakiltarsu a Majalissar Sarki, A Hadejia a kwai Sarkin Yarbawa wanda shine wakilin Yarbawa a Fada kamar yadda ko wace kabila take irin wannan Sarakunan masu wakiltarsu kuma suna karkashi umarnin Sarkin Hadejia. Mutanen Hadejiya da duk kabilun sukan hadu a kowace shekara su gudanar da bukukuwan Sallah karama da Sallah babba a Hadejiya. Ta haka al'ummar Hadejiya take cudanya da juna cikin walwala, farin cikin, nishadi, jindadi da annashuwa da sakin fuska. Kuma bisa dukkan alamu, kabilun da suke zaune a Hadejiya sun shiga juna sosai. Harma wani lokacin Sarakunan Yarbawan suna bawa Sarki shawarwari masu anfani. (Ginsau S. Ruwan Atafi 2015).
Bayan da aka fara barin yaki, irin wannan
kasuwancin ya koma kasuwancin “gwanja” a tsakanin Yarbawa da Hausawa a Kasar Hadejia. Daga cikin kayayyaki da Hausawa suke kasuwanci da Yarbawa
a Kasar Hadejia akwai kayayyakin sake sake kamar Riguna, da kere-kere, da kayan adon mata kamar Mundaye, da kayan kyalkyali iri-iri. Domin samun daurin gindi da kuma kwarjinin gudanar da kasuwancin, 'yan kasuwa Hausawa Kasar Hadejia sukan ba Sarakunan Yarbawa
kyautar Rigunan da suka ga sun dace da su. Wurin dawowa kuma sukan sawo bayi da Goro da dai sauransu. Haka dai akayi ta tafiya ana samun ci gaba ta fuskar abin saye ko sayarwa da dabarun kasuwancin har aka wayi gari Hausawa da Yarbawa a Kasar Hadejia suke cudanya da junansu suka zama abu daya ta yadda da wuya dan kallo ya iya rarrabe su in ba lafazinsu ya ji ba. Kabilar  da ba Musulmi ba suna karkashin kariya ta wannan masarauta, amma su kuma suna bayar da jizya.
Tun daga farkon kafuwar daular, Sarkin Hadejiya Malam Sambo ya dora kowace kabila daga cikin kabilun kasar a kan wani mukami na sarauta. Wannan tsari da aka ci gaba da aiwatar da shi, ya sanya jama'ar kasar sun zauna a dunkule tamkar tsintsiya domin kowace kabila ta san tana da wakilci a majalissar wannan masarauta.  (Ginsau S. Ruwan Atafi 2015).

TA FUSKAR ADDINI

Hadejiya tana da kabilu daban-daban, amma duk da haka, masarautar a cure take a waje daya. Addinin Musulunci shi ne ya dada hada su da kuma harshen Hausa wanda suke magana da shi a matsayin harshen kasa, amma Kabilar Yarbawa suna suna yin yaransu na Yarbanci a tsakaninsu. Babu ta baba cewa Addinin Musulunci shi ne Addinin da mafi yawan jama'a suke bi a wannan masarautar ta Hadejiya. Ka'idoji da dokoki da hukunce-hukunce Musulunci su ne suke tafiyar da rayuwa da ayyukan mutanen wannan kasa. Addinin Musulunci ya hada kan jama'a kuma ya samar da hanya madaidaiciya ta zaman al-umma.

TA FUSKAR AURATAYYA

No comments:

Post a Comment