Saturday, 27 May 2017

DAN AMAR ALHAJI USMAN GINSAU ALIYU 1919 -1997

An haifi Malam Ginsau a shekarar 1919 a cikin garin Hadejia. Ya yi karatun Elementary School a Hadejia daga 1/4/1934 - 31/3/1938. Ya zama Malamin Sarkin Auyo Malam Umaru ran 1/4/1941 har zuwa 31/3/1945.

Daga nan sai ya zama babban Malamin Ofishin Galadiman Hadejia Malam Yusufu ran 5/1/1945. Ya zama Store Keeper na Hadejia Native Authority (H. N. A)  Works ran 13/11/1946 a Ofishin Wakilin Sana'a Malam Sambo.

Shi ya fara rike mukamin Development Secretary na H. N. A ran 1/6/1961. Ya na Development Secretary H. N. A ta tura shi yawon bude ido kasar Ingila (England)  ran 25/4/1963 ya dawo ran 18/5/1963.

Ya bar aikin hukuma ya yi ritaya a shekarar 1981. Allah ya ma sa sarautar Dan Amar Hakimin Kafin Hausa ran 16/12/1983, aka nada shi. Har zuwa rasuwar sa ran 19/3/1997.

Allah jiqan Dan Amar Malam Ginsau.

No comments:

Post a Comment