Saturday, 27 May 2017

JAWABIN MAI GIRMA SARKI USMAN HARUNA II RANAR BASHI LAMBAR GIRMA TA SARKIN TURAI RAN LITININ 10/4/1941 DA ƘARFE 10 NA SAFE.

Aunika yami ana wabika wabihi nasta'inu

Godiya ta tabbata ga Allah, ya ku jama'a ta wannan taro ku saurara kuji jawabina Ni Sarkin Haɗejia Usman ɗan Sarkin Haɗejia Malam Haruna na II. Ina godiya ga Allah da ma'aikinsa ina kuma godiya ga Sarkin Turai, Joji na shidda tare da murna bisa ga samun wannan Lamba wanda ake kira (KING'S MEDAL for AFRICAN CHIEFS) ta girma daya sa aka bani, na godewa Gwamnan Nigeria da chifkamashena, tare da Rizidant Kano da kuma D.O na Haɗejia, saboda kokarin da sukayi mana na samun wannan lamba ta girma, abin farin cikine ƙwarai gareni ni da jama'ata duka muna fata Allah ya inganta mulkin Sarkin Turai ya kuma samun nasara bisa wannan uƙuba dake gudane, wadda Hittiler ya tadda tsakaninsu Jamus da Mulkin Turai, da sauran ƙasashen cikin duniya, Allah ya kiyayemu da jama'ar adalci muga bayan mazaluntane nazi Jamus Iyalin Hittiler. Allah ya kiyayemu ya bamu alheri Allahu amin.

No comments:

Post a Comment