Bismillahi Rahamani Rahimi, Goɗiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya bamu ikon taruwa a yau don muyi bukin Sallah Ƙarama (Sallar Azumi) kamar yadda muka saba yi kowane shekara.
To jama'a ina gargaɗinku da ku ƙara koƙari wajen Yaƙi da Jahilci don ku sami damar sanin abinda Duniya ke ciki, kuma ku ƙara ƙoƙarin Yaki da Lalaci don ku sami ishashshen abinci da abin buƙata, kuma ina so ku daina almubarzaranci da ɓarnata kuɗin jama'a ba ta hanyar da ya kamata ba, mutumin da aka sameshi da irin wannan laifi shima za'ayi masa horo mai tsanani. Har yanzu dai jama'a ina gargaɗinku da ku kiyaye zaman lafiya da haɗa kai domin sai da haɗa kai sannan zamu sami damar ciyadda ƙasarmu gaba. Daga ƙarshe jama'a ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya bamu lafiya , zama lafiya tare da wadata. Kuma ina roƙon Allah ya kaiku gidajenku lafiya ku sami iyalinku lafiya, amin.
Kafin na gama jawabina jama'a ina roƙonku da cewa daga yanzu ina so ku kwantadda hankalinku ku zauna lafiya ba tare da wani hargitsi ba. Daga nan ba da daɗewa ba wannan sabon Gwamna na Gwamnatin Soja ta Nigeria ta Arewa tare da Sakataransa zasu bi dukan N.A don su baiyanawa jama'a halin da ake ciki na wannan hali.
No comments:
Post a Comment