Na kirkiri wannan dandali domin tinawa da abubuwan Tarihin Kasar Hadejia, da Mutanan ta da raya Al'adun Gargajiya Kasar Hadejia. Da bunkasa ADABIN Hausa...
Tuesday, 31 December 2019
GALADIMAN HADEJIA ALH. YUSUF USMAN, MON
Tuesday, 12 November 2019
HAUSA LANGUAGE
Tuesday, 17 September 2019
Labarin Rayuwata
Dama ce kawai...!
Ma'anar Dama itace "wani lokaci ko wasu jerin al’amura da kan yi dalilin faruwar wani abu."
Rayuwata gaba d'ayanta labari ne na damarmaki wanda ke sanya fata da karfafa zuciya. Wadannan damarmaki sun kasance da iznin Allah mad'aukaki tamkar wata fitila ce da ta haskaka mini tafarkin rayuwa na zama duk abunda na zama.
Dacewa da samun wad'annan damarmaki, da kuma amfani da su a lokutan da su ka bijiro, shine dalili da kuma matakin dagowata daga tsukun yankin mahaifata a Hadeja, Jihar Jigawa, arewa maso yammacin Najeriya, inda ya kaini zuwa madaukakan wurare kamar ofisoshi da d'akunan taron Majalisar ‘Dinkin Duniya da ke birnin New York na k'asar Amurka da kuma dukkan nahiyoyin da ke fadin wannan duniya.
Babbar dama ta farko a gareni ita ce ta samun mahaifi irin wanda Allah ya azurta ni da shi (Mallam Muhammad Adamu UNIK), jajirtaccen malamin makaranta kuma Hedimasta da ya shahara kan gaskiya da rikon amana da kuma aiki tukuru. Malam ne ya fara cusa min ak'idar sanin darajar ilmi da maida hankali a kan aiki, tare da nusar da ni kyawawan dabi’u na rayuwa irin su: gaskiya da rik'on amana, hak'uri da juriya, karfin hali, sanin darajar d'an adam, fin k'arfin zuciya, tausayi, da kuma uwa uba, ya dasa min ginshik'in tsoron Allah a zuciyata.
Wannan Damar dai ita ce ta ingantaccen ilimin da na samu k'yauta a makarantun gwamnati (tun daga makarantar firamare ta unguwa zuwa sakandaren yanki, jami'a da kuma k'ololuwar mataki na karatun aikin likita. Karatu, tarbiyya da kuma jajircewa su ne dai ta hanyar da Ubangiji ya d'aukaka Nura ya koma Dakta Nura a yau.
Dama ce bud'e ido da na yi da wuri akan harkokin siyasa na gane yadda ake gudanar da ita, a inda na fahimci tasiri ko k'arfi na tarayyar jama'a a karkashin wata manufa guda idan aka yi amfani da shi wajen yad'a ak'idar da za ta amafanar da daukacin al'umma, musamman bangaren talakawa.
Babbar Dama ita ce da Allah (SWT) ya had'ani da Dr Sule Lamido, wanda ya gano wad'ancan halaye nawa, da tarbiyya, da karatu, da kuma bibiyar siyasa, ya gamsu da su, sannan kuma ya ci alwashin sarrafa su. Shine dai sanadiyyar da ta kai ni can k'ololuwar gwamnati ina matashi d'an shekara 34 kacal, inda a gefe daya na san maza kuma maza su ka san ni, amma kuma a wani gefen na gane cewa duniyar nan fa ba komai ba ce face wani yanayi na k'ank'anin lokaci.
Ba komai ba ne face Dama ta jawo min yabo da girmamawa daga shugabannin k'asashe, manyan jami'an difilomasiyya da siyasa, fitattun shugabannin al'umma, hamshak'an ‘yan kasuwa da kuma y'an uwana likitocin da na samu dacewar yin gogayya da su, kuma Allah ya ba ni damar nuna musu kokari da jajircewata ta ganin na kai gaci a duk wani al’amari da na sa a gaba ko kuma duk wani aiki da aka sanya ni.
Babbar tambaya a nan ita ce, ta ya ya wani matashi marar gata a sama, wanda ya fito daga arewacin Nijeriya, yankin da miliyoyin ‘ya’yan talakawa irinsa su ke rasa makomar rayuwa tun suna ‘yan kasa da shekaru 10, ya zama Ministan Najeriya ma fi k'arancin shekaru tun bayan dawowar mulkin damokirad'iyya a kasar a 1999, k'wararre a aikin likitanci, gogagge a harkar diflomasiyya, kuma har ya taka rawa a harkokin siyasar al'ummarsa, a k'asar da samun irin wannan tagomashi sai ‘yan tsiraru, masu uwa a gindin murhu??!
..... Amsar dai mai SAUK'I ce!!...
Alhamdulillah... DAMA CE KAWAI!!!
Sanin da na yi cewa, ba dan wad'annan damarmaki da na samu a rayuwata ba, da kuwa ni ma zan iya shiga kowane irin hali, shine babban k'aimin da ya sanya na yi tunanin kafa wannan Gidauniya ta Unik Impact (www.unikimpact.foundation). Ita dai wannan Gidauniya tamkar wani dandamali ne na yi wa al'umma, musamman 'yan uwa matasa, kokarin samun dama a rayuwa ta hanyar bayar da tallafi ga harkokin ilminsu, tattalin arziki da kiwon lafiya, har ma da inganta muhallinsu. Sannan da yi musu jagoranci bisa sanin muhimmancin ilimi da kuma rungumar dabi’un kirki irin su: jajircewa a kan aiki, gaskiya da rik'on amana, fin k'arfin zuciya da kuma nuna tausayi ta hanyar yi wa al’umma hidima da taimakon na kasa.
Babban burin wanna Gidauniya shine tarairayar zukatan matasanmu da d'ora su a kan tafarkin samun d'aukaka da cin nasara a rayuwarsu. Idan har ni zan sami irin wannan d'aukaka, to a cikin ikon Allah kowa ma zai iya samun irin ta, ko sama da hakan ma idan ya sami dama.
Hakika tarbiyya ce, da kuma karatun da duniya ta koya min, su ka ganar da ni cewa, d'aya daga cikin hanyoyin da mutum zai nuna godiya a bisa ni'imomin da Allah ya yi ma sa, shine, shi ma ya yi sanadiyyar samun dama ga wasu. Ta haka ne kawai zamu yi tunanin gyara al'ummar nan; ko da kuwa a sannu sannu ne.
Wani k'wararre da na yi aiki tare da shi, ya ta6a yi min tambaya cewa ya ya na ke hangen wannan Gidauniya ta Unik Impact a cikin zuciyata?... sai na amsa masa da cewa:
"Kamar gungu ne na wasu mutane da Allah ya bai wa Dama a rayuwa inda su ma su ke k'ok'arin ganin wasu da yawa sun sami irin wannan damar."
Hausawa dai su kan ce: ‘Yi wa wani, yi wa kai....’
Monday, 26 August 2019
RANAR HAUSA TA DUNIYA (26-08-2019)
A matsayina na Bahaushe kuma Ɗan Hausa wanda yake alfahari da harshen Hausa, na ga ya dace a irin wannan rana in yi hoɓɓasa domin ganin na bijiro da wasu muhimman batutuwa waɗanda suka shafi BAHAUSHE
Ina son a wannan rubutun zan yi tsokaci a kan wasu abubuwa domin tunawa da RANAR HAUSA TA DUNIYA kamar haka:-
1. HAUSA
2. WANE NE BAHUSHE
3. A INA ƘASAR HAUSA TAKE?
4. SHAHARAR HARSHEN HAUSA
1. HAUSA:- Mahadi A. (1978) cewa ya yi, 'Hausa na nufin sunan da ake kiran wata ƙabila ko ƙasarsu'. Misali wani ya ce, 'Za ni Hausa'. Wato, zai tafi ƙasar Hausa ke nan.
Muhammad: 'Hausa suna ne da yake da ma'anar harshe da mutanen da suke magana da shi da kuma ƙasar da ake magana da shi'.
Abdullahi S. (1978), Ya ce. 'Asalin Hausawa daga cikin harsunan CADI yake, waɗanda suka samu nasu tushen daga (Proto Language). wato, harshen Hausa ya fito ne daga iyalan harsunan Cadi, waɗanda suka haɗa da: Ngizim da Shirawa da Mobber da Auyokowa da Badde da Montol da Bambara da Yiwom da Riyom da sauransu.
A dunƙule ana iya cewa, 'Harshen Hausa, harshe ne da Hausawa suke yin magana da shi, da shi suke gudanar da dukkan abubuwan da suka shafi rayuwarsu, da harshensu suke rubutu da karatu da kasuwanci tare da sarrafa shi wurin zantukansu na azanci da suka shafi, waƙa da zambo da habaici da karin magana da zaurance da sauransu.
Dangane da asali kuwa, masana sun fi karkata kan cewa, harshen Hausa yana daga cikin harsunan iyalan Cadi
2. WANE NE BAHAUSHE: Mahadi A. (1978), 'Bahaushe shi ne, wanda aka haifa a ƙasar Hausa, kuma mahaifinsa Bahaushe ne, ko da kuwa baƙo ne, a kuma same shi, yana gudanar da al'adun Hausawa da ɗabi'unsu yana kuma magana da Hausa'.
Adamu cewa ya yi, 'Hausa harshe ne na Hausawa, su kuwa Hausawa wasu al'umma ne da suke zaune a ƙasar Hausa a cikin yankin Afirka ta Yamma. Kuma su Hausawa mutane ne baƙaƙe, wato baƙar fata ba farare ba, ko da yake akan samu ƴan jefi-jefi musamman idan aka samu auratayya da wata ƙabila'.
Duba da wannan, ashe, kai da ni da ke da ku da su duk Hausawa ne, matuƙar mun samu kammu a cikin matakan da aka ambata na zama Bahaushe a sama. Sai dai idan ya ka sance mahaifinka ko mahaifiyarka ba Hausawa ba ne ba, to fa ka saɓa lamba.
3. A INA ƘASAR HAUSA TAKE:- Za a iya lalubo ƙasar Hausa a cikin Afirka ta Yamma, wato farfajiyar nan da take tsakanin dazuzzukan da suke kurkusa da gaɓar tekun Atilantika daga Kudu cikin Nijeriya, zuwa hamadar sahara a Arewa cikin ƙasar Nijer. Wasu kuwa na ganin ƙasar Hausa tana nan, daga abin da ya kama tsakanin tafkin kogin Cadi daga Gabas, zuwa guiwar kogin Kwara a can Yamma, don haka, ne ma suke kiranta da (Sudan ta Yamma).
Idan aka duba tasiwirar Afirka, za a samu ƙasar Hausa a tsakanin layi na (15N) zuwa na (18N) na Arewa da Ikwaita (equator). Kuma ƙasar tana tsakanin layi na (18E) da na (12E) a Gabas da layin Girinwich (Greenwhich).
A nasa ra'ayin Tahir Adamu (2003) ya ce, 'Ƙasar Hausa a yau, tana nan cikin Afirka ta Yamma a Arewacin Nijeriya, kuma a kwance ta taɓo har cikin ƙasar Nijer wajen su Maraɗi da wasu ƴan garuruwa, haka kuma, daga Gabas ta yi iyaka da ƙasar Borno, daga Yamma kuma, ta yi iyaka da wani yanki na ƙasar Dahomi (Dohomey) a gaɓar kogin Kwara, daga Kudu, ta yi iyaka da ƙabilun Gwari, da kuma ƙabilun Kudancin Zariya da na Kudancin Bauchi'.
Tirƙashi! To kun ji fa, inda ƙasar Hausa take da iyakokinta.
4. SHAHARAR HARSHEN HAUSA:-
Harshen Hausa ya shahara ya tumbatsa ta yadda kafatanin harsunan Afirka idan ka cire harshen Laraɓci (Arabic) babu wani harshe da ya kai harshen Hausa tumbatsa har da kuwa harshen Ki Swahili ko Swahili, musamman ta fuskar yawan masu magana da harshen da yawan karantar da harshen da yawan amfani da harshen a kafafen yaɗa labarai.
Zan iya bugun gaba, ba tare da jin ɗar! Ko shamaki ba, in bayyanawa duniya cewa, kafatanin harsunan Afirka babu harshen da ya kai harshen Hausa tara Gwanaye (Professors), haka nan, babu harshen da ya samu gata irin yadda Hausa ta samu ta yadda jami'o'in duniya suke karantar da harshen Hausa musamman irin su:
Ahmadu Bello Univesirty da Bayero University da Udus da Umyuk da Kadsu da University of Sebba, Libya da Versity of Logon, Ghana da Versity of Poland da King Sa'ud University, Riyadh da SOAS University of London da Colombian University, New York da UCLA University of Los Angeles, U.S.A da University of Khartum, Sudan da dai sauransu... Haka nan, ya samu gata ta ɓangaren kafafen yaɗa labarai da suka ƙunshi gidajan rediyo da mujallu da gidajan talabijin na duniya kamar irin su: Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da Jaridar Aminiya da Jaridar Nijeriya Ta Arewa da Jaridar Ƴancin Ɗan Adam da Jaridar Himma da Haske da Bazazzaga da Suda da Gamzaki da sauransu. Ɓangaran gidajan rediyo kuwa akwai irin su: Rediyon R.F.I (France) da Rediyon Cairo da Rediyon Misira da Kamaru da S.A Makka da na Ghana da na Moscow da Damagaram da Kolon (Jamus) da Beijing (China) da Rediyo D.W da na V.O.A America da na B.B.C Hausa da sauransu....
A taƙaice, a wannan ɗan rubutun, mun bayyana asalin harshen Hausa da ma'anar Hausa har ma da bayani akan wane ne Bahaushe da kuma bagiren da ƙasar Hausa take tare da fito da ƙima da kuma shaharar da harshen Hausa ya yi.
Hausa mai ban haushi na Kande mai kan bashi. Lallah Hausa ta ciri tuta, Hausa ta tumbatsa, sai dai kash! Har yau har gobe ina kuka, dangane da yadda samarimmu suka yi fatali da yawa daga cikin al'adummu musamman ta fuskar tufiafi da mu'amala.
Daga Ɗan Hausa
Wednesday, 21 August 2019
NEW DG, NITDA, MALAM INUWA KASHIFU ABDULLAHI
Mr Inuwa Kashifu Abdullahi, is a Massachusetts Institute of Technology - MIT Sloan - trained strategist with 14+ years of experience in IT operations, business transformation and solution architecture, across both private and public sectors. He attended Leadership and Management courses at Harvard University in the USA, University of Cambridge in the UK and IMD Business School in Switzerland.
As the 1st Cisco Certified Internetwork Expert (CCIE) in Nigeria's Public Sector, he is also a certified project manager and Solution architect. With so many professional certifications in networking, telecommunications, service management and Solution design such as: Huawei telecommunications engineer, Cisco design professional, ITIL, Prince2 etc.
Mr Inuwa is a graduate of Computer Science from the prestigious Abubakar Tafawa Balewa University, Bauchi. He was born on 21st February, 1980 and hails from Hadejia Local Gov't of Jigawa State.
He has worked in Galaxy Backbone as Network Engineer , IP Network Field Engineer, Senior Network & Lead, IP Operations Team, and Senior Solution Architect & Lead, Technical Solution Design Team between 2004 to 2013.
In 2014 he joined Nigeria's Apex Bank (CBN) as a Technology Architect, where he dedicated his time to developing Technology Architecture Repository that gives 360 view of the Bank’s IT infrastructure and easy decision on new IT investment. He was part of the team that executed software license rationalization which has increased cost savings for the Bank in license annual subscriptions. Mr. Inuwa was a key resource in the development of IT standards for the Bank which has reduced mean time to deploy/integrate new system by over 20%. One of his major achievement as a Technology architect was the production of 7 Solution Architectures for critical IT initiatives that helped in achieving cashless society in Nigeria.
He went to NITDA in 2017 as Technical Assistant to the Director General/CEO. Being the IT regulatory body in Nigeria mandated to implement National ICT policy, he;
-Managed execution of strategy which has increased ICT contribution to Nigerian GDP by over 13% in Q2 2018.
• Coordinated Local Content initiatives that has increased ICT local production by over 200% in 2017.
• Overhauled IT clearance process and encouraged shared services among agencies. This has helped Federal Government saved over 16Bn NGN from IT projects.
• Oversaw procurement process that has reduced cost of major projects by over 5% in two consecutive annual procurement cycles.
• Managed project execution that has implemented over 300 IT infrastructure intervention.
Mr. Inuwa is a member of both British Computer Society (BCS) and Nigeria Computer Society (NCS) in addition to many memberships to his credit.
He is a recipient of 100 Leading Telecom and ICT Personalities in Nigeria – By Association of Telecommunications Companies of Nigeria (ATCON).
He is married with children.
Tuesday, 20 August 2019
MUHIMMANCIN AIKIN SA KAI A TSAKANIN AL’UMMA DOMIN INGANTA MUHALLI
Jawabin
Dr. Nura Muhammad
A Taron
Gangamin Kaddamar Da Dashen
Bishiyoyi Da Inganta Muhalli
A Garin Hadeja
Lahadi 18 ga Agusta, 2019
A'uzubillahi Minash shaid'anir rajim. Bismillahir rahmanir raheem.
Maimartaba Sarkin Hadeja, kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa; Alhaji (Dr) Adamu Abubakar Maje Haruna (CON)
Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa; Alhaji Umar Namadi
‘Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar yankin Arewa maso gabas na Jihar Jigawa; Sanata Ibrahim Hassan Hadeja (Shattiman Hadeja II)
Babban Sakatare a Ma'aikatar kula da Muhalli ta Jihar Jigawa; Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa
Shugaban Hukumar Talabijin ta Jihar Jigawa; Alhaji Ishaq Hadeja
Shugaban K'ungiyar Gangamin Tsabtace Garin Hadeja da Shuka Bishiyoyi (HGPE); Mallam Ahmad Ilallah
Wakilan Kungiyar Inganta Muhalli da Shuka Bishiyoyi ta garin Gumel (GCIGCE)
Shugabannin Kungiyoyin sa kai na al'ummar Hadeja
Sauran manyan bak'i da aka gayyata
'Yan Jarida na rediyo, da talabijin, da jaridu, da kuma kafafen sada zumunta na zamani
Y'anuwana maza da mata
Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu....
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Mad'aukakin Sarki, mai kowa mai komai, da ya bamu ikon taruwa a yau domin gudanar da wannan gagarumin aiki na alheri. Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon tsira Annabi Muhammad (SAW), fiyayyen halitta kuma mafificin masu tsabta da inganta muhalli.
Daga farko, zan fara da godiya maras adadi ga shugabannin wannan gamayya ta matasa domin tsabtacewa da kuma inganta garin Hadeja da suka bani wannan muhimmiyar dama har kashi biyu.
Ta farko ita ce kasancewa babban mai gabatar da jawabi a matsayina na d'an uwansu matashi - Dr Nura. Domin a ba mutum damar yin magana gaban irin wannan gangami, musamman idan a ka yi la'akari da irin mutanen da aka tara a wannan wuri, to ba k'aramar dama ba ce da kuma girmamawa.
Maudu'in da a ka ce na yi magana a kansa shine 'Muhimmancin Aikin Sa kai a Tsakanin Al'umma Domin Inganta Muhalli'.
Dama ta biyu kuwa ita ce, ta alfarmar da aka yi wa Gidauniyar da na k'irk'ra, wato Gidauniyar Unik Impact (ko Unik Impact Foundation a turance) ta yin tarayya a wannan aikin alheri da suka assasa ta hanyar ba da gudunmuwar d'aruruwan irin mad'aci da kuma mangwaro na zamani. Babban abin godiya ne a ba ka damar shiga cikin wani aikin alheri na al'umma.
Shuka bishiya abu ne mai matuk'ar muhimmanci a garemu ba wai kawai ta fuskar kariya da inganta muhalli ba, a'a, har ma ta fuskar addininmu, tattalin arzik'inmu, da kuma walwalarmu.
Tun farko, shi dai addinin musulunci, a matsayinsa na tsarin wayewa na gabadayan rayuwa, ya yi tanadin tsare-tsare da ka iya magance matsaloli na muhalli da ke yi wa d'an adam barazana a wannan lokaci. A bisa tarbiyya irin ta addinin musulunci, wasu magabatan na kallon cewa hatta shi kansa muhallin wani nau'ine na amana da Allah (SWT) ya mallaka a hannun bayinSa. Akwai ayoyi da dama na Alkura'ani mai tsarki da su ke tsawatarwa ga mumunai akan almubazzaranci, yad'a 6arna da kuma fasadi a bayan k'asa. Lalatawa da kuma wofintar da muhalli, tamkar wani nau'ine na almabozaranci da kuma 6arna a bayan k'asa.
Saboda matukar muhimmancin da addinin musulunci ya dora kan amfanin itatuwa a muhallin dan Adam shi ya sa ma ya yi hani da sare bishiyoyi da sauran nau'in shuke- shuke ba tare da wani kwakkwaran daliliba.
Manzon Allah Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, ya kwadaitar a cikin ingattattun hadisansa akan falala da kuma fa'idar inganta muhalli, da daraja shi, da kare shi ta hanyar shuka bishiyoyi. D'aya daga cikin hadisan shine wanda mazon ya ke cewa; "ita duniyar nan koriya ce shar k'yak'yk'yawa, kuma Allah (SWT) ya dank'a muku ita a matsayin amana".
Ko da a yanayi irin na yak'i, Manzon tsira ya kan gargadi kwamandojin rundunonin musulmi da su guji sare bishiyoyi da kuma amfanin gona na abokan gaba. Ma'aikin dai ya kasance a lokacin rayuwarsa yana bada muhimmanci da karfafa guiwa kan amafani da k'asa mai d'orewa, rage tara shara, da kuma jin k'ai ga dabbobin daji. Cikamakin annabawan, ya samar da 'Hima' a kudancin birnin Madina, inda ya haramta yin farauta a cikin tsawon kusan murabba'in kilomita bakwai (7). Ya kuma hana sare bishiyoyi a cikin tsawon kusan murabba'in kilomita ashirin (20). Allahu Akbar. Allah muna k'ara gode maka a bisa ni'imar addinin musulunci da ka yi mana.
Shuka bishiya wani nau'i ne na sadaka, kamar yadda ya zo a hadisi. Imamu Bukhari ya rawaito a wani hadisi a cikin littafinsa cewa Manzon Allah (SAW) ya ce; "Duk wani musulmi da ya shuka bishiya, kuma wani bil adama ko dabba ta ci daga jikin wannan bishiyar, to za a saka ma sa ne tamkar ya ba da sadaqa" (Sahih Bukhari Vol. 8, Book 73, No. 41)
Wad'annan ayoyi da kuma hadisai na Mazon tsira na nuni da cewa, shi dai wannan addini na mu na musulunci, shine tsarin wayewa na farko a duniyar nan da ya fara rubutawa da kuma zaburar da d'an adam akan tanade tanaden Kimiyyar muhalli, da inganta shi, da kuma kare dabbobin daji. Kula da muhalli dai na mu ne musulmai ba wai na wani bature ba ne ko iliminsa. Tun dai kafin a haifi magabatan mai sabulu balbela ke da farinta tas-tas!
A kimiyyance kuwa, bishiya ce ke bamu sinadarin Oxygen (O2) na iskar da mu ke shak'a. Sannan ita kuma ta janye na Carbon dioxide (CO2) da mu ke fitarwa. Bishiya ce ke rage abubuwa ma su wari da kuma gur6ata yanayin iska kamar sinadaran nitrogen oxide, ammonia, sulfur dioxide da kuma ozone. Bishiya ta na k'arfafa k'asa ta rage zaizayewarta. Bishiya ta na sanyaya tituna da gidajenmu su zama masu ni'ima. Bishiya tana taimkawa wajen rik'e lema a cikin k'asa. Bishiya na kare yara daga hasken rana na ultra violet mai cutar da fatarsu. Bishiya tana samar da abinci ga mutane da dabbobi.
Bishiya na kawo waraka a wasu nau'o'in rashin lafiyar jiki da kuma k'wak'walwa. Yawan Bishiyoyi na rage tashe-tashen hankula a tsakankanin al'umma. Bishiya tana bun'kasa tattalin arzik'in al'umma. Bishiya tana samar da makamashi. Bishiya tana k'ara darajar kadarar gida, ko gona, ko kuma fili a lokacin sayar da shi.
Kuma sare bishiyoyi ne ke jawo karuwar d'umamar yanayi, kwararowar hamada, zaizayar k'asa, rashin albarkar noma da yawan ambaliyar ruwa, ga kuma rashin muhallin zama ga namun daji, da wahalar ruwan sha.
A kowace shekara, hamada na k'ara kwarara zuwa kudu daga arewa da nisan kusan kashi shida na kilomita d'aya. Kamar dai, a bisa misali, hamadar na tafiyar nisan da ya kai daga nan zuwa garin Mallam Madori a cikin kowane shekaru talatin (30). Kwararowar hamada kuwa na daga gaba gaba a cikin abubuwan da ke kawo tsadar abinci, k'arancin ruwa na sama da na k'asa, tashe-tashen hankula a kan guraben noma da kiwo, tilastawa mutane yin k'aura, da kuma k'aruwar talauci a tsakanin al'umma.
Jiharmu ta Jigawa na d'aya daga cikin jihohi uku a Najeriya da su ke a kan gaba wajen fuskantar barazana ya kwararar hamada.
Amma kash, duk da wad'annan fa'idodi na shuka bishiya da kuma kare muhalli da addini ya nusar da mu akan su, da kuma ta fuskar tattalin arziki da zamantakewarmu, sai ga shi cewa, mu dai an shuka bishiya ba mu shuka ba. Mun kuma sare bishiya ba mu shuka ba!
Jama'a, mecece mafita a nan?
MafIta dai ta farko ita ce cigaba da wayar da kan al'ummarmu akan amfanin shuka bishiya da tattalinta, da kuma maida hankali wajen kokarin dakatar da kwararowar hamada. Wadanda ke da alhakin gabatar da wannan aiki na wayar da kan jama’a dai ba su wuce gwamnati ba, da maluman addini, da kuma k'ungiyoyi na al'umma ma su zaman kansu. Wato tamkar dai irin abin da mu ke yi a yau d'in nan.
Mafita ta biyu kuwa ita ce samar da makamashi mai sauk'in kud'i da samu ga al'umma. Abu ne da kowa ya sani cewa babban abin da ya ke kawo yawan sare bishiyoyi a wannan 6anagare na mu ita ce bukatar itace don yin makamashi. A saboda haka, da alama fa mutane za su iya ci gaba da cinye dazuzzukan nan idan har ba a samar mu su da wani makamashi a madadin itacen ba. Itace dai kusan shine makamashin da a yau bai fi k'arfin da yawa daga cikin al'ummarmu ba, kuma a kan same shi ba da wata wahala ba. A gaskiyar magana, har sai an samarwa da al'umma wani makamashi kwatankwacin irinsa ne za a iya yin wata tabbatacciyar magana akan hana saran bishiyoyi domin yin makamashi da su.
Mafita ta uku kuwa ita ce al'umma su tashi tsaye a d'aid'aiku da kuma a k'ungiyance ko kuma a gwamnatance su shuka bishiyoyi. Ina matuk'ar farin cikin cewa wannan shine dalilin taruwarmu gaba d'aya a wannan fili.
Shi fa wannan mataki na tattara kan al'umma su yi ta shuka bishiyoyi ba bak'on abu bane a cikin al'ummar nan. Mun bud'i ido a garin nan mun ga ana yin irin wad'annan gangami. Mun kuma tashi mun ga garin nan gaba d'ayansa a kewaye da rukunin bishiyoyi daban daban da ake kira plantation, gwanin ban sha’awa. Don haka, yanzu ne lokacin da za a komawa baya a yi karatun ta-nutsu, ba wai gobe ko jibi ba.
Saboda a daidai lokacin da mu ke yin wannan zancen, wa su k'asashen fa, hatta a nan nahiyarmu ta Afrika, tuni sun yi nisa a cikin wannan al’amari. A cikin watan Yulin da ya gabata, K'asar Habasha (wato Ethiopia), wadda ke da yawan jama’a kimanin miliyan tamanin (80), wato kwatankwacin kaso d'aya bisa uku kenan na yawan al’ummar Najeriya, ta yi wa al'ummarta k'aimi su ka shuka bishiyoyi kimanin miliyan d'ari uku da hamsin da uku (353). K'asar ta samu nasarar shuka wad'annan bishiyoyi masu dimbin yawa ne a rana d'aya tak a k'ark'ashin wani shiri na musamman na korar hamada da matashin Fira-Ministan k'asar, Abiy Ahmed Ali, ya jagoranta da kansa.
Babu abin da zai hanamu irin wannan yunk'uri anan Najeriya koma a gida Jihar Jigawa. Domin shi fa shuka bishiyar nan,
nagge ne dad'i goma; ga lada, ga samar inuwa, ga hana k'wararowar hamada, ga kuma, uwa uba, arzik'i.
Allah ya ja zamanin Sarki, manyan bak'i, ina da masaniya akan wani nazari mai ban al'ajabi da wani kamfanin bincike na k'wararru da ke birnin London mai suna Price WaterHouse Cooper ya ke gudanarwa a halin yanzu. Shi dai wannan nazarin bincike ana gudanar da shi ne kacokam akan irin arzikin da ke mak'are a jikin bishiyar charbi ko kuma maina. A binciken, wanda har yanzu ba a fito da shi ba, k'asar India ta na da irin wannan bishiya guda miliyan ashirin (20) kacal. Amma wannan bishiyoyi ta na samarwa da k'asar kud'ad'en shiga kusan dalar Amurka biliyan shida (6Billion) a kowace shekara.
Binciken ya cigaba da nuna cewa, k'asar Najeriya mai bishiyar maina miliyan d'ari da talatin da hud'u (134), ita ce ta fi kowace k'asa albarkar wannan bishiya a fadin duniya. Jihar Jigawa kuwa ita ce a kan gaba a fad'in Najeriyar da yawan bishiyoyi miliyan talatin da hud'u (34). Wato jihar Jigawa ita kad'ai ta na da bishiyoyin maina sama da d'aya da rabin na k'asar India. Amma babban abin tak'aici a nan shine, ita Najeriya kwatankwacin dalar Amurka miliyan d'ari hud'u da arba'in (440) kawai ta ke iya samu a jikin wad'annan bishiyoyi a duk shekara!
Ni dai a guna romon wannan bincike shine, idan mu ka dage, jiharmu ta Jigawa za ta iya samun ak'alla dalar Amurka biliyan d'aya (wato kusan Naira biliyan 360 kenan a kowace shekara) daga jikin wad'annan bishiyoyi da Allah ya albarkacemu da su. Naira biliyan 360 dai ya fi kwatankwacin duka kud'in da jihar ke samu a cikin shekara daga gwamnatin tarayya. Haka dai irin wannan gara6asa da sirri ke a cikin bishiyar k'aro, wanda namu na nan Jigawa da Yobe shine giredin farko a duk fad'in duniyar nan.
Za mu iya zage dantse kamar k'asar Habasha mu shuka miliyoyin wad'annan bishiyoyi. Za su yi mana maganin kwararowar hamada, sannan, uwa uba, su azurta al'ummarmu da arzik'i mai d'orewa.
Da alama dai niyyar irin wannan zage dantse ne samari matasa su ka fara yi a yau d'in nan. Yunk'uri ire iren wannan daga bangaren matasanmu, wad'anda kuma su ne gobe, ya sa na ke cike da fatan cewa in Allah ya yarda goben ta mu a bisa ga dukkan alamu za ta kasance mai k'yau.
K'ungiyoyi ne biyu masu zaman kansu, na samari (d'aya a garin Gumel d'aya kuma a Hadeja), su ka yi tarayya a kan muradi na kula da kuma inganta muhalliasu, ba tare da cewa kowace d'aya ta san da zaman d'ayar ba. Ni kuma ta hanyar kafar sada zumunta ta facebook na yi muwafak'ar haduwa da su har mu ka k'ulla zumunta mai ak'ida da manufa iri d'aya. D'aya daga cikin manufofi da ak'idun Gidauniyar da na k'irk'ra (wato Unik Impact) shine taimakon al'umma ta ji6intar harkokin ilminsu, kiwon lafiya, tattalin arziki da kuma inganta muhallinsu. To a wannan ga’bar ne k’udiri da manufofinmu su ka zo d'aya.
Wannan ita ce goben da mu ke fatan samarwa a tsakanin al'ummarmu. Kuma ita ce goben da a kullum iyayen k'asa sarakuna ke jan hankulanmu a kai. Sannan ita ce goben da a cikinta mu ke fatan al'umma gaba d'ayanta za ta gina siyasarta kacokaf a kan doron cigaba, ba tare da yin la'akari da wasu bambance bambance na ra'ayin jama'iyya, ko 6angare ko kuma na jinsi ba.
Babu shakka dole ne sai al'umma ta kawar da duk wani nau'i na son rai, ta kuma ci gaba da yin irin wannan tarayyar akan muhimman abubuwan da su ka shafe ta, musamman na harkar ilminta, da lafiyarta, da kuma tattalin arzik'inta ne kawai, za ta iya gamon da katar da ci gaba mai dorewa
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dai ya ce: "Mafi alkhairi a cikin al'umma shine wanda ya amfani al'ummar."
Allah ka sa mu ci gaba da zama masu amfani ga al'ummarmu baki d'ayanta
Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu...
Sunday, 18 August 2019
HAWAN ZIYARA
Kamar yadda aka sani ƙasar Hadejia tana gabatar da Hawa guda uku a kowace shekara, wato Sallar Azumi, Sallar Layya da kuma Maulidi. Sannan kuma a kowace Sallah ana gabgaba da hawa guda biyu... Hawan sallah da Hawan Bariki, Sannan rana ta uuku yara suyi Hawan daushe da La'asar.
Kamar yadda Tarihi dai ya nuna Sarkin Hadejia Mallam Abdulkadir shine ya kirkiro Hawan Bariki, a wata fira da mukayi da Galadiman Jauje ya tabbatar mana cewa Sarki Abdulkadir mutum ne Mai son nishadi, hakan yasa a zamanin sa aka kirkiri Hawan Bariki. Sarki yaka je washegarin sallah da hakimansa da Dagatai su kaiwa D.O. Ziyara.
Ranar Laraba 20/April/2005 Mai martaba sarkin Hadejia Alh. Adamu AbuAbuba Maje ya kirkiro Hawan Ziyara kokuma Hawan Mai Bubban Daki, wannan hawa an fara yinsa ne a sallar Mauludi, wadda kuma za'a rinka yinsa ko wace sallah da yamma. Wato za'a hau washe garin Hawan Bariki.
Ranar Juma'a 22/April/2005, Mai martaba ya hau da yamma. Inda yabi ta tudun mabudi Har zuwa Tudun Barde ya shiga yayi ziyara ga Mai bubban Daki, Bayan ya fito sai yabi ta makera ta Dubantu ta Ganuwar kofar yamma, sannan sai yabi ta bakin kasuwa ta Makwallah ta kofar Jarma sannan In yazo kofar Fada sai ya Tsaya Hakimai kuma su Fara zuwa daya bayan daya suna Jafi. Bayan sun Gama sai ya shiga Gida ya sauka.
Ismaila A Sabo
Thursday, 28 March 2019
KADAN DAGA CIKIN IRE-IREN CUTUTTUKA DA YUNWA DA AKAYI A KASAR HADEJIA, A WANCEN ZAMANIN.
1. An samu bulluwar wata cutar Dabobi a Kasar Hadejia a 1898 wadda tayi sanadiyar mutuwar dabobi da dama a wancen lokacin.
2. Anyi wata Yunwa a Kasar Hadejia a 1908 a lokacin Sarki Haru Mai Karamba, bayan kammala Yakin Turawan Mulkin Mallaka wadda tayi sanadiyyar mutuwar Jama'a da dama tare da Dabobin su. Mutanan Hadejia suna mata lakabi da (Yunwar Biri).
3. Anyi wata karamar Girgizar Kasa a Kasar Hadejia a 1909.
4. An samu bulluwar wata Cuta (Epidemic Disease) a Kasar Hadejia a 1909 wadda tayi sanadiyyar mutuwar Jama'ar gari da yawa, ta sanadiyar wannan cuta ne Allah ya yiwa Sarki Haru Mai Karamba rasuwa.
5. A zamanin Sarkin Hadejia Abudulkadir a 1914 Farkon Yakin Duniya a Farko anyi wata Babbar Yunwa a Kasar Hadejia wadda sanadiyar mutuwar Jama'a wasu kuma sukayi hijira zuwa wasu garuruwa.
6. An samu bulluwar wata Cuta (Community Disease) a 1917 a Kasar Hadejia wadda mutane suke mata lakabi da (MARISUWA) wannan Cuta ta kama Mutane da Dabobi.
7. Anyi wani Zazzabin Gari mai Zafin gaske a 1925 a Kasar Hadejia wanda yayi sanadiyar mutawar Jama'ar Gari da dama, ta sanadiyyar wannan Zazzabi ne Sarkin Hadejia Abdulkadir Allah ya masa rasuwa.
8. A Zamanin Sarkin Hadejia Usman a 1927 anyi wata Yunwa a Kasar Hadejia wadda mutane suke mata lakabi da (MAI BUHU).
Wanda ba'aga anan insha Allahu za'a gani a kashi na biyu
KASHI NA BIYU NA NAN TAFE
Monday, 18 March 2019
SOME CONTRIBUTIONS OF THE EMIR OF HADEJIA ALH. HARUNA ABDULKADIR DURING HIS REIGN.
He was born in Hadejia in 1908, he was installed as the new Emir at the age of 42 in 1950. Not long he become the Emir of Hadejia that he went to Saudi Arabia, he was the first Emir of Hadejia to go to Holy pillgrime to Mecca in 1952. He would however be remembered for his numerous contributions to the progress and the vast development of his people and the entire Emirate. During his reign noted for his relentless effort and activitism in fostering growth, peace, and development in his domain.
It was during his 34 years reign that such noble and tramendous Economic, Social, Political, administrative developments become so visible in Hadejia Emirate. Hadejia Water Supply was commissioned in 1955. The construction of the new Emir Chamber commence in 1953 and that the new Emir's Gate in 1959.
The first landed Aircraft was said to have taken place at Hadejia in 1959. And School of Agriculture in 1972 at Malam-Madori, a 24 hour electricity supply also become the lot of the generality of the people of Hadejia during his reign. It was also during his reign that agriculture was revolutionised and given a boost in the Emirate.
For a large production of grain crops which Hadejia is noted for the FG established Hadejia Jama'are River Basin and Rural Development Authority. So the government Multi-Million Naira Irrigation Scheme under Hadejia Jama'are, since been contributing to the mass harvest of Wheat, Rice, Millet, and Guinea-Corn by the farmers in Hadejia.
The new Hadejia Juma'at Mosque was commissioned for use in 1962 in recognition of his contribution to the development of his Emirate Alh. Haruna Abudulkadir was Awarded O.B.E Medal in 1963. He also the paid a visit to England on Medical ground in 1971 as the first the First Emir of Hadejia to travel to Europ.
In spite of the turbulent political pandemonium and confusion of the first and the second republicts that ravaged the whole country as a result of election rigging, thuggery, intolerance and economic crunch, Hadejia was able to witness an unpertured atmosphere of peace and tranquility.
This might not be unconnected with the counsel of the able rularship of the Emir Alh. Haruna Abudulkadir who was able to control his subject. The energetic Emir, as a result of his deterioriating condition. He dead on 23rd August, 1984 at the age 70.
SULEIMAN GINSAU
See More... Part 2 Coming Soon...
Tuesday, 5 March 2019
FIRST EMIR'S CAR ARRIVED AT HADEJIA IN 1921
...Also there was the a outbreak of community diseas in 1917 known as (Marisuwa). The means of transportation had been animal such as Donkeys, Camels, and Cattles, but at this own time foreign ideas in form of Technology and modernization ware brought to Hadejia in 1931.
The first Emir's Car thus arrived at Hadejia in 1921 also the establishment of commercial firms commenced in Hadejia in 1917. There was also the construction of the present Hadejia Local Government Authority Prison in 1922. This time Sir Hugh Clifford the Governor of Nigeria had paid a visit to the Emir of Hadejia in 192. He was nickenamed by the Hadejia people (Gwamna Mai Baza). For the first time there was also the introduction and consolidation of Western Education which brought about some changes, in the Traditional and Islamic Administration and of course progress in the Emirate as people began to send their children to school to have Western Education at Hadejia Elementary School that was declared open in 1924.
In 1912 the old Hadejia Market was transfered from outside to the center of the town. The distribution of District Administration areas and their Headquarters took place in 1913.
The industrious Emir of Hadejia Abudulkadir, dead in 1925 at a tender age 37 his death might not be unconnected with the community fever (Zazzabin Duk Gar) that broke up in 1925 in which a lot of people died. Ha was succeeded in 1925 by Usman.
Source:- Haghen and Kirk-Greene (1966)
Monday, 14 January 2019
MA'AJI KAFIN ZUWAN TURAWAN MULKIN MALLAKA KASAR HADEJIA.
Kalmar Ma'aji a kasar Hadejia tsohuwar kalmace wacce aka dade ana amfani da ita, wannan kalma tana nufin Ajiya, a lokacin yake-yake a kasar Hadejia Sarakunan Hadejia suna fita yake-yake kuma su kama bayi. A duk lokacin da suka fita irin wannan yake-yake suna tahowa da bayi masu yawan gaske wanda suka hada maza da mata ga kuma ganima mai tarin yawa. Suleiman Ginsau
A wannan lokaci Sarakuna sai su sami wani amintacce daga cikin Yaransu sai su bashi Ajiyar wannan bayi da aka kama a wajen yaki domin yana kula da su wajen Ci da Sha da kuma aikace-aikace da-ban-da-ban to wannan mutumin da aka bawa Ajiyar wannan bayi sai mutane suke masa lakabi da sunan Ma'aji. To a wannan zamani shi wannan Ma'aji bashi da wani gida ko wani waje da inda zai wannan bayi ya kulle sai da kawai ya taho dasu Unguwar da yake ya dauresu a bakin kofar gidansa wasu kuma ya daure su a wurare da ban a cikin Unguwa. Ta hake ne aka samu sunan Unguwar Ma'aji a Hadejia. Wannan Unguwa a halin yanzu tayi rassa wanda hakan yasa aka samu wasu Unguwanni a jikinta kamar irinsu:-
Unguwar Sabon Garu
Unguwar Dukawa
Unguwar Maga Hudu
Unguwar Madaki
Da dai sauransu kuma duk wadannan uguwanni suna da tarihi na abin mamaki.
Amma bayan zuwan Turawan mulkin mallaka sai suka karawa abin armashi sannan suka sake fitowa da wani sabon tsari na MATAWALLE. Yana da mutukar alfanu a fadi aiyukan Ma'aji da aiyukan Matawalle sannan a fadi ban-banci tsakanin Ma'aji da Matawalle. Sai babu lokaci. Ga sunayen wasu daga cikin Ma'aji:-
1. Ma'aji na Farko a Hadejia (Mal. Hassan)
2. Ma'aji na Biyu a Hadejia (Mal. Khaila)
3. Ma'aji na Uku (Mal. Kasim)
MATAWALLE.
1. Mal. Usman
2. Mal. Amadu
3. Mal. Saleh
Suleiman Ginsau