Monday, 26 August 2019

RANAR HAUSA TA DUNIYA (26-08-2019)

A matsayina na Bahaushe kuma Ɗan Hausa wanda yake alfahari da harshen Hausa, na ga ya dace a irin wannan rana in yi hoɓɓasa domin ganin na bijiro da wasu muhimman batutuwa waɗanda suka shafi BAHAUSHE

Ina son a wannan rubutun zan yi tsokaci a kan  wasu abubuwa domin tunawa da RANAR HAUSA TA DUNIYA kamar haka:-
1. HAUSA
2. WANE NE BAHUSHE
3. A INA ƘASAR HAUSA TAKE?
4. SHAHARAR HARSHEN HAUSA

1. HAUSA:- Mahadi A. (1978) cewa ya yi, 'Hausa na nufin sunan da ake kiran wata ƙabila ko ƙasarsu'. Misali wani ya ce, 'Za ni Hausa'. Wato, zai tafi ƙasar Hausa ke nan.
     Muhammad: 'Hausa suna ne da yake da ma'anar harshe da mutanen da suke magana da shi da kuma ƙasar da ake magana da shi'.
     Abdullahi S. (1978), Ya ce. 'Asalin Hausawa daga cikin harsunan CADI yake, waɗanda suka samu nasu tushen daga (Proto Language). wato, harshen Hausa ya fito ne daga iyalan harsunan Cadi, waɗanda suka haɗa da: Ngizim da Shirawa da Mobber da Auyokowa da Badde da Montol da Bambara da Yiwom da Riyom da sauransu.

A dunƙule ana iya cewa, 'Harshen Hausa, harshe ne da Hausawa suke yin magana da shi, da shi suke gudanar da dukkan abubuwan da suka shafi rayuwarsu, da harshensu suke rubutu da karatu da kasuwanci tare da sarrafa shi wurin zantukansu na azanci da suka shafi, waƙa da zambo da habaici da karin magana da zaurance da sauransu.
Dangane da asali kuwa, masana sun fi karkata kan cewa, harshen Hausa yana daga cikin harsunan iyalan Cadi

2. WANE NE BAHAUSHE: Mahadi A. (1978), 'Bahaushe shi ne, wanda aka haifa a ƙasar Hausa, kuma mahaifinsa Bahaushe ne, ko da kuwa baƙo ne, a kuma same shi, yana gudanar da al'adun Hausawa da ɗabi'unsu yana kuma magana da Hausa'.

Adamu cewa ya yi, 'Hausa harshe ne na Hausawa, su kuwa Hausawa wasu al'umma ne da suke zaune a ƙasar Hausa a cikin yankin Afirka ta Yamma. Kuma su Hausawa mutane ne baƙaƙe, wato baƙar fata ba farare ba, ko da yake akan samu ƴan jefi-jefi musamman idan aka samu auratayya da wata ƙabila'.

Duba da wannan, ashe, kai da ni da ke da ku da su duk Hausawa ne, matuƙar mun samu kammu a cikin matakan da aka ambata na zama Bahaushe a sama. Sai dai idan ya ka sance mahaifinka ko mahaifiyarka ba Hausawa ba ne ba, to fa ka saɓa lamba.

3. A INA ƘASAR HAUSA TAKE:- Za a iya lalubo ƙasar Hausa a cikin Afirka ta Yamma, wato farfajiyar nan da take tsakanin dazuzzukan da suke kurkusa da gaɓar tekun Atilantika daga Kudu cikin Nijeriya, zuwa hamadar sahara a Arewa cikin ƙasar Nijer. Wasu kuwa na ganin ƙasar Hausa tana nan, daga abin da ya kama tsakanin tafkin kogin Cadi daga Gabas, zuwa guiwar kogin Kwara a can Yamma, don haka, ne ma suke kiranta da (Sudan ta Yamma).

Idan aka duba tasiwirar Afirka, za a samu ƙasar Hausa a tsakanin layi na (15N) zuwa na (18N) na Arewa da Ikwaita (equator). Kuma ƙasar tana tsakanin layi na (18E) da na (12E) a Gabas da layin Girinwich (Greenwhich).

     A nasa ra'ayin Tahir Adamu (2003) ya ce, 'Ƙasar Hausa a yau, tana nan cikin Afirka ta Yamma a Arewacin Nijeriya, kuma a kwance ta taɓo har cikin ƙasar Nijer wajen su Maraɗi da wasu ƴan garuruwa, haka kuma, daga Gabas ta yi iyaka da ƙasar Borno, daga Yamma kuma, ta yi iyaka da wani yanki na ƙasar Dahomi (Dohomey) a gaɓar kogin Kwara, daga Kudu, ta yi iyaka da ƙabilun Gwari, da kuma ƙabilun Kudancin Zariya da na Kudancin Bauchi'.

Tirƙashi! To kun ji fa, inda ƙasar Hausa take da iyakokinta.

4. SHAHARAR HARSHEN HAUSA:-
    Harshen Hausa ya shahara ya tumbatsa ta yadda kafatanin harsunan Afirka idan ka cire harshen Laraɓci (Arabic) babu wani harshe da ya kai harshen Hausa tumbatsa har da kuwa harshen Ki Swahili ko Swahili, musamman ta fuskar yawan masu magana da harshen da yawan karantar da harshen da yawan amfani da harshen a kafafen yaɗa labarai.
Zan iya bugun gaba, ba tare da jin ɗar! Ko shamaki ba, in bayyanawa duniya cewa, kafatanin harsunan Afirka babu harshen da ya kai harshen Hausa tara Gwanaye (Professors), haka nan, babu harshen da ya samu gata irin yadda Hausa ta samu ta yadda jami'o'in duniya suke karantar da harshen Hausa musamman irin su:

Ahmadu Bello Univesirty da Bayero University da Udus da Umyuk da Kadsu da University of Sebba, Libya da Versity of Logon, Ghana da Versity of Poland da King Sa'ud University, Riyadh da SOAS University of London da Colombian University, New York da UCLA University of Los Angeles, U.S.A da University of Khartum, Sudan da dai sauransu... Haka nan, ya samu gata ta ɓangaren kafafen yaɗa labarai da suka ƙunshi gidajan rediyo da mujallu da gidajan talabijin na duniya kamar irin su: Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da Jaridar Aminiya da Jaridar Nijeriya Ta Arewa da Jaridar Ƴancin Ɗan Adam da Jaridar Himma da Haske da Bazazzaga da Suda da Gamzaki da sauransu. Ɓangaran gidajan rediyo kuwa akwai irin su: Rediyon R.F.I (France) da Rediyon Cairo da Rediyon Misira da Kamaru da S.A Makka da  na Ghana da na Moscow da Damagaram da Kolon (Jamus) da Beijing (China) da Rediyo D.W da na V.O.A America da na B.B.C Hausa da sauransu....

    A taƙaice, a wannan ɗan rubutun, mun bayyana asalin harshen Hausa da ma'anar Hausa har ma da bayani akan wane ne Bahaushe da kuma bagiren da ƙasar Hausa take tare da fito da ƙima da kuma shaharar da harshen Hausa ya yi.
    Hausa mai ban haushi na Kande mai kan bashi. Lallah Hausa ta ciri tuta, Hausa ta tumbatsa, sai dai kash! Har yau har gobe ina kuka, dangane da yadda samarimmu suka yi fatali da yawa daga cikin al'adummu musamman ta fuskar tufiafi da mu'amala.

Daga Ɗan Hausa

No comments:

Post a Comment