Wani muhimmin al'amari a mulkin Turawa ya danganci tarawa da karban kudaden shiga da za'ayi amfani dasu wajen tafiyar da al'amuran mulki. Turawan mulki sun lura da cewa hanyoyin da masarautar Hadejiya take amfani dasu a da wajen tara kudaden shiga ba su gamsar da suba. Turawan mulki sun so mutane kalilan su kasance masu gudanar da wannan aikin, wadanda cikin sauki za'a rinka kulawa da su da kuma dora musu nauyin duk abinda ya fara na almubazzaranci da kudaden jama'a. Ta hakane kawai za'a iya kiyaye koda da oda na wannan aikin. Daga nan ne Turawa suka kawo wani tsari sabo na saukaka hanyoyin tara kudaden shiga. A wannan sabin tsarin, a wannan kamar yadda aka bayyana a baya kadan, an nemi hakimai su koma garuruwansu da zama su sa ido a kan harkikin gurarensu. Ta haka aka rushe matsayin Jakadu a kaikaice.
To a, wannan tsarin mai unguwa zai karbi harajin jama'arsa zai tattara wadannan kudade ya kai wa hakiminsa kai tsaye, daga nan shi kuma zai dauka ya kai wa Sarki.
Ikon tarawa da binciken kudaden shiga kuma na Resdan ne ko kuma wakilansa, amma duk da haka wannan ikon an bawa hakimai shi zuwa dan wani lokaci. An cigaba da karban ire-iren haraji a 1906 in banda wasu kadan kamar harajin sana'a.
Haka kuma an kirkiro wasu nau'o'in haraji, Misali a 1914 aka shigo da kudin su inda aka dirawa masunta su dinga biyan wasu 'yan kudi gwargwadon kimar kifin da suka kama ko kimanin kayan kamun kifin da suke amfani da su. Domin haka masunta masu amfani da koma za su biya kudi kasa dana masunta masu amfani da taru domin nasu yafi girma kuma yafi kami kifi da daya.
Haka kuma an shigo da harajin magidanta da kudin gona da ake karba gwargwadon fadi da tsayin gona . Daga nan kuma Turawan mulkin mallaka suka suke Zakka da Jizya wadanda ake karba a lokacin daular masu jihadi ta Sakkwato. Ta haka ne Turawan mulki suka gwama tsakanin kudaden shiga da ake karba kafin 1906 da wadanda suka shigo da su sababbi inda tsarin ya fara aiki a wajajen 1918.
Daga wannan lokaci ne aka fara buga haraji ga mutanan kasa inda aka aza wa mutum daya magidanci Sule Biyar, shi kuma matashi wanda ya kai farfi Sule Uku. Ga kuma Jangali inda aka sa wa kowace saniya daya Sule daya da 'yan kai.
Da farko harajin da aka tara ana rabshi kashi biyu, "kashi daya za a turawa Gwamnatin Ingila" sauran kashi daya za a barwa hukumar cikin gida domin biyan bukatunta na mulki. Daga baya kuma aka yankawa ma'aikatan N.A albashi a kowana karshen wata.
An fara sabon tsarin ajiye kudi a Baitul-Mali a Hadejia da Katagum a shekarar 1909. Turaki shi ne ya fara zama ma'ajin farko na Baitul-Malin Hadejia, "amma a shekarar 1911 an sami wani sabani ya faru tsakaninsa da Sarkin Hadejia Abdul'kadir da Turaki Munkaila akan yadda za a kashe kudaden da ake tarawa. To tun daga wannan lokaci Sarki ya ci gaba da kula da Baitul-Mali da kansa har zuwa lokacin da aka nada wani amintaccen Sarki sabon Ma'aji.
Har wa yau kuma a shekarar 1915 an sake samun wani saban tsari a Hadejia a wannan lokacin an kirkiro wani lardi daga masarautar Katagum da Gumel da kuma Hadejia wannan lardi an fara ajiye hedikwatarsa a Gumel, amma a shekarar 1916 sai aka mayar da ita izuwa Hadejia. Daga nan kuma aka sake daddatsa gundomumin Masarautar Hadejia zuwa guda tara a karkashin ikon Rasdan W.F Gower. Wadannan sababbin gundumomi sun hada da:-
1. Gundumar Birniwa Sarkin Arewa
2. Gundumar Guri Ciroma
3. Gundumar Garun Gabas Mabudi
4. Gundumar Kirikasamma Sarkin Damawaki
5. Gundumar Kaugama Madaki
6. Gundumar Auyo Sarkin Auyo
7. Gundumar Kafin Hausa Sarkin Bai
8. Gundumar Bulangu Wambai
9. Gundumar Dakido Tafida
Wadannan gundumomi tara 9 suna ci gaba da wanzuwa har zuwa shekarar ta 1926 a lokacin da aka sake zuwa da wani sabon tsari kuma inda lardin Katagum wanda ya hada masarautun Katagum da Jama'are da Misau aka mayar da shi a cikin lardin Bauchi. Shi kuma lardin Katsina ya koma cikin lardin Zariya, Hadejia da Gumel da Daura da Kazaure aka sake hada su a wani sabon lardin Arewa aka yi masa hedikwata a Hadejia.
Har ila yau kuma wadannan gundumomi tara 9 an sake rage yawansu aka mayar dasu bakwai 7 gasu kamar haka:-
1. Kafin Hausa
2. Malam Madoei
3. Bulangu
4. Guri
5. Auyo
6. Kirikasamma
7. Birniwa
Wannan shi ne tsarin na karshe wanda Turawan Mulkin Mallaka suka tashi suka bari a dai-dai a karshen 1959.
Abin tambaya a nan shi ne yaya jama'ar kasa suka karbi wadannan canje-canje?
Hakika jama'a basu yi na'an da wadannan tsare-tsare ba, a wani wurin ma suna nuna fushinsu. Wadannan tsare-tsare bisa yawanci sun kara wa talakawa ne nauyi ta hanyar dora musu harajin Kai da na sana'o'i, ga kuma ayyukan gayya da ake sa suyi a ko da yaushe ba tare da an biya su ba, haka kuma tsare-tsaren sun haifar da rashin cikakkiyar biyayya, Misali a gundumar Gizimawa da Badawa suna biyan harajinsu ta hanyar Sarkin Bade, amma a sabon tsarin Turawa sai a suka dora musu Ciroma. Wannan ya kawo rashin nutsuwa ga mutanen Bade domin wani bangare na Gizimawa ma sai da suka bijire wa biyan haraji. Daga nan Turawan Mulkin Mallaka suka kama shugabanin wada suka ki biya aka sa su a kuekuku, daga baya aka sasanta kowa ya biya nauyin da aka dora masa. Amma duk da haka wasu sun ki biya, a saka makon haka ne sukayi kaura zuwa Gumel. SULEIMAN GINSAU
MADOGARA
Heussler, R. (1968) The Biritish in Northern Nigeria. London: Oxford University Press.
Gower, W.F. (1921) Gazetteers of Kano Province. London: Frank Cass
Hiskett, M.A (1975) Two Verse Account of Hadejia History a cikin History of Hausa Islamic Verse.
Wakili H. (2005) Turawa a Kasat Hadejia. Benchmark Publishers Ltd.