Thursday, 8 March 2018

SARKIN JAUJE TUKUR WADDA YAYI SHAHADA A YAƘIN HADEJIA DA TURAWA YANA YIWA SARKIN HADEJIA MUHAMMADU WAƘA YANA CEWA...

1. Muhammadu ne Toron Giwa, Na Sambo ka wuce raini Sarki.

2. Na Amadu Angon Kura, Kana Ɗaka ke Gayya na Garba da fitarka a watse ɗai ɗai, Na Abdu Hurdi ɗagogon Bannu, Jitau na Jarma abin ƙauna.

3. Bisa ga lumana Sarki, an ƙira ka Katagum ka je, haka ka je Sharfar ka zo, In ko babu lumana Hurdi, ƙofa tasa ma bai je ba bare su Bariki can mai nisa.

4. Ka lura Muhammadu na Garba, Ga Sarkin  Malle sai yawo take, Ga Sarkin Bidda da ma Sarkin Sudan, na Kwantagora ka duba, duka sun gudu don tsoro.

5. Uban Kabo Mamman ɗa, da gudun sa a goranta masa, kuma ko kowa a kama shi, Na Sambo gara kisa take, ƙi gudu gara shahada ta fi.

6. Da wulakanci ɗibgau, Shahada ta fi Muhamman, Da ka bisu a Tozarta ka, jama'ar ka su ɗai-ɗaice, na Amadu gara a gwabza ya fi.

7. Da dai na baya su goranta mana, Ace mun kasa har kai, ko ka gudu don tsoron wani, Ai gara mu ƙare duk, Da mu bar baya da Gorin banza.

8. Sa gudu baya wargi, Haka baya son mai wargi, kai ne Buhari tuna sosai, Da ka bi su a kama ka, Muhammadu gara ka kwana Kushewa.

9.

10.

Ismaila A Sabo

No comments:

Post a Comment