Monday, 11 June 2018

UNGUWAR BAYI A HADEJA

Wani Matambayi ya aiko min da tambayar yana son sanin, a ina Unguwar Bayi ta samo suna, da kuma su wanene mazauna unguwar.

Amsar wannan tambaya ita ce:

Ma’anar Bayi dai shine unguwar da take Ƙofar Baya. Anan ana nufin bayan Fadar Sarki. Ana sane da cewa ƙofofin fadar Mai Martaba Sarkin Hadeja guda biyu ne. Farko ita ce babbar ƙofar da ke gaban fadar a fuskar Yamma, ko kuma Ƙofar Fada a taƙaice. Ita wannan ƙofa, a shekarun baya kafin a rushe ta a gina ta zamani, ana kiranta Mai Tsatstsewa.

Ƙofa ta biyu ita ce wannan ƙofa ta baya, da ke fuskar Gabas, wadda aka fi sani da Kofar Ruhogo (babban rumbun aje kayan abincin Sarki).

A garuruwan Katsina da Zaria ma, haka waɗannan unguwanni suka samo suna. Saidai a Katsina ana kiran wannan unguwa ne da sunan Kofar Bai, a Zaria kuma ana kiranta da Ƙwar Bai. Karin harshe na Haɗejanci (Haɗeja dialect) yasa ake cewa Bayi anan Haɗeja. Kamar yadda wasu suke cewa Sarkin Bayi, a maimakon Sarkin Bai, duk asalin guda ne.

Abu na biyu kuma dangane da batun su wanene mazauna wannan unguwa ta Bayi? Amsar ita ce: akasarin mazauna wannan unguwa mahukuntan Gari da mashawartan Sarki ne, anan gidajen da yawa daga cikin ‘yan majalisa da hakimai suke.

Za’a iya fahimtar fa’idar hakan akan samarda wurin da zai bada damar tuntuɓa ta gaggawa tsakanin Sarki da manyan hakimansa ko ‘yan majalisa ko mashawartansa. 

Sannan kuma kasancewar gidanjen Hakimai a bayan gidan Sarki ya inganta tsaro ga Fadar domin gidajen hakiman kansu kewaye suke da na maƙarrabansu. Ta haka Fadar ta zama tana da kariya gaba da bayanta. Wannan tunani na magabata ta fuskar tsaro yayi matuƙar tasiri a wancan lokaci na yaƙe-yaƙe, kuma hakan ya bayyana ƙarara a shekarun nan da yanayin tsaro ya taɓarɓare a ƙasar nan.

Daga: Engr. Daudu Abdul'aziz

No comments:

Post a Comment