Thursday, 30 June 2016

MAKADAN FADA/SARAUTA

MAKA'DAN FADA/SARAUTA

Makad'an fada ko sarauta su ne wad'anda ke tsare kid'ansu ko wak'ok'insu ga wani basarake guda a matsayin ubangida. Sukan rayu ga yi wa shi wannan basarake wak'a ko dai wani amininsa, bisa izininshi. Taskar Suleiman Ginsa

Basaraken duk da ya rik'i wani makad'i a matsayin mawak'insa na fada, to fa shi ne ci da sha; sutura da muhalli; da duk wasu nauyaye-nauyayen wannan makad'i. Haka nan kuma mafi akasarin makad'an fada gadon kid'a suka yi a masarautar da suka taso, wato abin nufi sun gaji yi wa masarautar kid'a ne daga mahaifansu ko kakanninsu, har abin ya zo gare su. Misali Alhaji Musa 'Dankwairo ya gaji yi wa Sarkin 'Kayar Maradun kid'a ne daga babanshi.Taskar Suleiman Ginsau

A wasu lokutan kuma mawak'an na canjin ubangida ko basarake, ko dai don ya daina yi musu abubuwan da aka lisafta a baya; ko kuma saboda hango wani na sama da shi; ko kuma don wani dalili na k'ashin kai. Taskar Suleiman Ginsau

KAYAN KI'DIN MAKA'DAN FADA:

Kamar yadda kowane rukunin makad'a a Hausa ke da kayan kid'ansu na musamman, makad'an fada ma na da nasu; wad'anda suka fi yawan tu'ammuli da su. Daga ciki akwai:-
1. Tambari
2. Taushi
3. Jauje
4. Banga
5. Kotso
6. Algaita
7. Kakaki.

Bari mu d'auki wad'annan d'aya bayan d'aya mu yi tak'aitaccen bayani a kansu.

TAMBARI :-
Shi dai wannan wani abin kid'i ne mai girman gaske, ga amo mai kai wa nisan uwa duniya, (Watak'il hakan ta sa Hausawa ke kuranta shi da,''Tambari a ji ka sama'u''.) Ana yin sa da fatar ruk'ak'k'en taure ko kuma bajimin sa ko dai makamntanta.

Ana iya cewa a duk kayan kid'an makad'an fada, to tambari ne gaba da su, domin shi ba a kad'awa kowa sai basarake, shi ma sai 'Sarkin Yanka' da kad'an daga cikin amintattun hakiman masarauta.

TAUSHI :-
Wannan abin kid'a yana kama da akushi a siffa. Ana rufe samarshi da fata a rink'a duka yana fitar da sauti. Shi ma yana daga cikin kayan kid'an makad'an fada.

KOTSO :-
Fasalin kalangu gare shi, sai dai shi baki d'aya ne ake rufewa da fata, a rink'a buga shi da tafin hannu; ba tare da mabugi ba.

JAUJE :-
Yana kama da kalangu sosan gaske, domin kuwa ana rufe duk 6angarorinshi biyu da fata, a kuma buga shi da mabugi irin na kalangun.

BANGA :-
Kamar siffar gwangwani yake, a rufe da fata. Shi ma da hannu ake buga shi.

ALGAITA :-
Tana daga abin busawa da ke fitar da sauti mai ziza. Gajera ce; ba ta kai kakaki tsawo ba.

KAKAKI :-
Wani abin busawa ne mai k'ara da ziza sosai wanda ya lunka na algaita. Ana busa shi da baki, haka kuma yana da tsawo k'warai da gaske; wani ma ya fi mai busa shi tsayi.

SUTURAR MAKA'DAN FADA :
Duk inda makad'in fada yake za a iske shi yana shiga ta k'asaita da alfarma. Ba su yarda da saka sutura wacce ba ta isa ba, saboda kasancewarsu a gidan wadata da taskokin suturu. Sukan yi ado da manyan riguna da hulunan dara ko zanna ko k'ube, wasu lokutan ma har da rawani sukan nad'a.

JIGOGIN WAK'OK'IN MAKA'DAN FADA :

Masana sun fito da jigogi da dama na wa'ko'kin makad'an fada, amma manya daga ciki su ne:
1. Tarihi
2. Zuga
3. Yabo
4. Habaici
5. Zambo

A nan za mu d'auki wa'kar Alhaji Musa 'Dankwairo ta Sarkin Gombe, Shehu Na-abba don fito da wad'ancan jigogi daga cikinta.

TARIHI :
Makad'an Fada na da hikima ta sak'a tarihi a cikin mafi yawancin wa'ko'kinsu. Za a ji su suna ta rattabo wasu abubuwajen tarihi da suka shafi masarautar da suke yi wa wa'ka. A wannan wa'ka ga abin da 'Dankwairo ke cewa:
"...Yadda Buba Yero yai Sarki,
Kai ma ka zamà Sarkin Gombe,
Kai Allah yab bai wa k'asar nan.
Yadda Sarki Sule yai Sarki,
Kai ma ka zamà Sarkin Gombe,
Kai Allah yab bai wa kasar nan.
Yadda K'wairanga yai Sarki,
Kai ma ka zamà Sarki Gombe,
Kai Allah yab bai wa 'kasar nan.
Yadda Hassan yai Sarki Gombeee,
Kai ma ka zamà Sarki Gombe,
Kai Allah yab bai wa 'kasar nan..."
Har zuwa wurin da yake cewa,
"...Kamar Sarki Abubakar, shekara tai arba'in da takwas yana mulki 'kasar Gombe, fata mu kai ka nunkaaa,
Shehu don kai ad da halin Abubakar..."

Za mu ci gaba... a kashi na Biyu

Suleiman Ginsau ANA

No comments:

Post a Comment