LITTAFIN RUWAN ATAFI
NA
SULEIMAN GINSAU
Littafin Ruwan Atafi littafine da yake dauke da tarihin Ruwn Atafi, da takaitaccen tarihin masarautar Hadejia, yadda aka kafa masarautar Hadejia da tarihin zaman takewar jama'a da tattalin arziki a kasar Hadejia kafin zuwan Turawan mulkin mallaka na kasar Ingila. Sannan wannan littafi yayi duba izuwa tsarin tsaro a kasar Hadejia kafin Mulkin Mallaka, sannan littafin Ruwan Atafi yayi wai waye dangane da irin gudun mawar da wannan ruwa mai albarka ya bayar musammam ga al'ummar kasar Hadejia baki daya, wajen yake-yaken da Hadeji a yake-yaken kasar Hausa a wannan lokacin duk gabas da sakkwato babu wata kasa ai karfi da nuna jarunta da yawan mayaka sadauki kamar kasar Hadejia, kasar Hadejia tayi suna ainun a fagen nuna jarunta. A irin wannan jaruntarne Kasar Hadejia tayi fito-na-fito da Sojojin Mulkin Mallaka na Kasar Ingila a 1906. A wannan fafatawar Mutana Kasar Hadejia suka fatattaki Turawan wanda Sarkin Hadejia Muhammadu Mai Shahada ya kashe Captin Philips wato shugaban sojojin Turawan wanda mutanan Hadejia suke yi masa lakabi da (Maitumbi). Kuma haryanzu kabarinsa yana cikin garin Hadejia. Ana jingina duk wannan jarunta da karfi ga mutanan Hadejia sabi da tasirin Ruwan Atafi. Mutanan Hadejia a lokacin yake-yake sai sukayi wani Rami sannan sukacewa mayakans cewa kowa yaje gida ya dauko Lakanin ko Dafa'i ko Maganin da yake dashi domin suna zubawa a cikin wannan Rami da suka tonahi, sannan sai su bebo ruwa suzuba acikin wannan Rami idan maganin ya tsomu koya juku sai subarshi sai yayi kwana Uku idan zasu fita yaki sai su taro a bakin wannan rami sai a debo wannan ruwa ana basu suna sha suna wanke fuskokinsu da hannayensu, bayan sun gama sai a basu umarni da cewa ATAFI ATAFI ATAFI ma'anar atafi shine sutafi subar wajen daga nan kuma sai filin yaki.
Mu hadu a kashi na 2
No comments:
Post a Comment