Thursday, 30 June 2016

MAKADAN FADA/SARAUTA

MAKA'DAN FADA/SARAUTA

Makad'an fada ko sarauta su ne wad'anda ke tsare kid'ansu ko wak'ok'insu ga wani basarake guda a matsayin ubangida. Sukan rayu ga yi wa shi wannan basarake wak'a ko dai wani amininsa, bisa izininshi. Taskar Suleiman Ginsa

Basaraken duk da ya rik'i wani makad'i a matsayin mawak'insa na fada, to fa shi ne ci da sha; sutura da muhalli; da duk wasu nauyaye-nauyayen wannan makad'i. Haka nan kuma mafi akasarin makad'an fada gadon kid'a suka yi a masarautar da suka taso, wato abin nufi sun gaji yi wa masarautar kid'a ne daga mahaifansu ko kakanninsu, har abin ya zo gare su. Misali Alhaji Musa 'Dankwairo ya gaji yi wa Sarkin 'Kayar Maradun kid'a ne daga babanshi.Taskar Suleiman Ginsau

A wasu lokutan kuma mawak'an na canjin ubangida ko basarake, ko dai don ya daina yi musu abubuwan da aka lisafta a baya; ko kuma saboda hango wani na sama da shi; ko kuma don wani dalili na k'ashin kai. Taskar Suleiman Ginsau

KAYAN KI'DIN MAKA'DAN FADA:

Kamar yadda kowane rukunin makad'a a Hausa ke da kayan kid'ansu na musamman, makad'an fada ma na da nasu; wad'anda suka fi yawan tu'ammuli da su. Daga ciki akwai:-
1. Tambari
2. Taushi
3. Jauje
4. Banga
5. Kotso
6. Algaita
7. Kakaki.

Bari mu d'auki wad'annan d'aya bayan d'aya mu yi tak'aitaccen bayani a kansu.

TAMBARI :-
Shi dai wannan wani abin kid'i ne mai girman gaske, ga amo mai kai wa nisan uwa duniya, (Watak'il hakan ta sa Hausawa ke kuranta shi da,''Tambari a ji ka sama'u''.) Ana yin sa da fatar ruk'ak'k'en taure ko kuma bajimin sa ko dai makamntanta.

Ana iya cewa a duk kayan kid'an makad'an fada, to tambari ne gaba da su, domin shi ba a kad'awa kowa sai basarake, shi ma sai 'Sarkin Yanka' da kad'an daga cikin amintattun hakiman masarauta.

TAUSHI :-
Wannan abin kid'a yana kama da akushi a siffa. Ana rufe samarshi da fata a rink'a duka yana fitar da sauti. Shi ma yana daga cikin kayan kid'an makad'an fada.

KOTSO :-
Fasalin kalangu gare shi, sai dai shi baki d'aya ne ake rufewa da fata, a rink'a buga shi da tafin hannu; ba tare da mabugi ba.

JAUJE :-
Yana kama da kalangu sosan gaske, domin kuwa ana rufe duk 6angarorinshi biyu da fata, a kuma buga shi da mabugi irin na kalangun.

BANGA :-
Kamar siffar gwangwani yake, a rufe da fata. Shi ma da hannu ake buga shi.

ALGAITA :-
Tana daga abin busawa da ke fitar da sauti mai ziza. Gajera ce; ba ta kai kakaki tsawo ba.

KAKAKI :-
Wani abin busawa ne mai k'ara da ziza sosai wanda ya lunka na algaita. Ana busa shi da baki, haka kuma yana da tsawo k'warai da gaske; wani ma ya fi mai busa shi tsayi.

SUTURAR MAKA'DAN FADA :
Duk inda makad'in fada yake za a iske shi yana shiga ta k'asaita da alfarma. Ba su yarda da saka sutura wacce ba ta isa ba, saboda kasancewarsu a gidan wadata da taskokin suturu. Sukan yi ado da manyan riguna da hulunan dara ko zanna ko k'ube, wasu lokutan ma har da rawani sukan nad'a.

JIGOGIN WAK'OK'IN MAKA'DAN FADA :

Masana sun fito da jigogi da dama na wa'ko'kin makad'an fada, amma manya daga ciki su ne:
1. Tarihi
2. Zuga
3. Yabo
4. Habaici
5. Zambo

A nan za mu d'auki wa'kar Alhaji Musa 'Dankwairo ta Sarkin Gombe, Shehu Na-abba don fito da wad'ancan jigogi daga cikinta.

TARIHI :
Makad'an Fada na da hikima ta sak'a tarihi a cikin mafi yawancin wa'ko'kinsu. Za a ji su suna ta rattabo wasu abubuwajen tarihi da suka shafi masarautar da suke yi wa wa'ka. A wannan wa'ka ga abin da 'Dankwairo ke cewa:
"...Yadda Buba Yero yai Sarki,
Kai ma ka zamà Sarkin Gombe,
Kai Allah yab bai wa k'asar nan.
Yadda Sarki Sule yai Sarki,
Kai ma ka zamà Sarkin Gombe,
Kai Allah yab bai wa kasar nan.
Yadda K'wairanga yai Sarki,
Kai ma ka zamà Sarki Gombe,
Kai Allah yab bai wa 'kasar nan.
Yadda Hassan yai Sarki Gombeee,
Kai ma ka zamà Sarki Gombe,
Kai Allah yab bai wa 'kasar nan..."
Har zuwa wurin da yake cewa,
"...Kamar Sarki Abubakar, shekara tai arba'in da takwas yana mulki 'kasar Gombe, fata mu kai ka nunkaaa,
Shehu don kai ad da halin Abubakar..."

Za mu ci gaba... a kashi na Biyu

Suleiman Ginsau ANA

Tuesday, 28 June 2016

HISTORY OF SHADAI WATER IN AUYO LGA (Hadejia Emirate)

Shadai Water.

Shadai is a pool in Auyo town (Hadejia Emirate) whose "miraculous" waters had the power of curing disabled and handicapped persons. People used to drink and bath with the water in order to get cured from their diseases and deformities. Although the story of Shadai is of recent vintage, its origin is traceable to the pre-jihadic era. According to one source, Auyo at the time of the Habe Chief of Auyo, Jibrin, had a considerable number of muslim scholars (Ulama) who established their base in the town. One day the Ulama decided to vacate the town as a result of a serious disagreement between them and Sarki Jibrin. They lacked all their belongings including their religious books, manuscripts and other items of value and sneaked out of the town at night. When the news of this development reached Sarki Jibrin, he immediately dispatched his bodyguards to pursue the fleeing Ulama and persuade them to return. However, in the event that they refused to return, the Chief further ordered that their books should be confiscated and brought to him. As it happened, the Ulama turned down Sarki Jibrin's request, whereupon all their valuable books were seized and brought to the Chief who had them placed in big pots and buried at the outskirts of Auyo town. Several years after that incident, water was suddenly seen gushing out from the spot where those books were buried. It was soon realized that the water was no ordinary water as it had medicinal powers. As news about this "miraculous" water spread, people from different parts of Nigeria and even abroad trooped to the scene. Soon the place became over- crowded, and a camp was established beside the pool to accommodate more visitors. The appearance and efficacy of Shadai waters was confirmed by the Colonial administration when the Divisional Officer (D.O) of Hadejia in his 1935 annual report, stated that: "people from many parts of Nigeria visited Shadai and most of them were cured people took bath and drank the water with prayers to meet their wishes. Blind men got their eyes opened, crazy people came to their senses, and women who had never given birth to children got children." The waters of shadai used to disappear and reappear in intervals of several years, with the latest reappearance said to be in 963. 

See Part 2

Tuesday, 21 June 2016

THE SHORT HISTORY OF HADEJIA PART 4

Aftermath of Gamon

Kaffur The victory at Kaffur
was both materially and psychologically
beneficial to the Hadejawa in general. To Buhari
in particular the triumph earned him a period of
non-interference from Sokoto. The Sultan simply
tried to forget the Hadejia problem and probably
prayed for the speedy death of Buhari. But Buhari
still had a decade of his life to live, and he spent
those years promoting the cause which had
always been the cornerstone of his foreign
policy: the expansion of the Hadejia frontier.
Marma was the first to suffer his wrath. Seizing
on a disagreement with the Emir of Marma,
Buhari besieged the capital, tunnelled under the
town wall, and at dawn carried out a punitive
attack on the inhabitants. Since then, Marma
and its subject towns have become parts of
Hadejia Emirate. Then in 1860 he turned his
attention once again on Miga, forcing the
evacuation of that district; but though it
remained deserted for three years, Miga was
never incorporated into Hadejia Emirate. Buhari
now switched his forces to Katagum – always a
problem Emirate for him. In order to capture
Katagum Buhari needed an advance
headquarters close to the city. And he decided
that the town of Tashena would serve this
purpose adequately. First though, he went to
Sarkin Tashena and asked for assistance in an
expedition he planned against Gorgaram, a
request which was willingly granted since the
Emir hated the guts of his rival at the Badde
capital. Taskar Suleiman Ginsau

“A prudent ruler cannot, and must not honour his
word when it places him at a disadvantage,”
wrote the-not-so-honourable Machiavelli. Buhari
couldn’t agree more. For once the Tashena
cavalry had joined his own, Buhari fell on the
town, killed its Emir and then made Tashena the
field headquarters from which for six months he
laid siege on Katagum city.

Perhaps it was poetic justice that he was unable
to overcome the town, and was forced to
withdraw due to overwhelming logistical
problems. But he did return, this time storming
through southern and central Katagum, where he
unsuccessfully attacked Azare, conquered Bidir
and Gambaki, and destroyed Jama’are town.
For all his conquests, Buhari’s dream of an
extensive Emirate remained largely that – a
dream. The truth was that he simply did not
possess the manpower to keep many of the
areas he conquered under any but temporary
occupation. Even in his lifetime Buhari had to
helplessly watch areas he conquered revert to
their former status. Taskar Suleiman Ginsau

The ambitious Buhari finally suffered “death for
his ambition”, to use a Shakespearian phrase.
And, like the Caesar to whom the quote referred,
he too was a victim of the treachery of his own
intimate circle. In fact, had Buhari possessed the
melodramatic bent of the fictitious Caesar, his
last words might have been “Et tu, Haruna?” For
although Haruna, another of Buhari’s brothers,
did not, in the manner of Brutus, actually slay his
more illustrious relative, there was not the
slightest doubt that he was guilty of planning it. Taskar Suleiman Ginsau

Buhari’s Death On his last campaign, which was
against the Badde capital of Gorgaram, Buhari
found himself alone, with only a few men, at the
head of one column. All his officials had hung
back as he made his advance, partners in an act
of premeditated desertion orchestrated by the
scheming Haruna. He was struck by an arrow,
and died later on the road back to Hadejia.

Late Muhammadu Buhari is remembered in
Hadejia as much for his military prowess as for
some of the civil contributions he made during
his 15-year chequered tenure. During his time
the number of administrative offices was
doubled. Numerous slave-quarters as well as
homes for leading figures were constructed. The
royal compound itself was greatly enlarged.

Indeed, all the Manyan Soraye of pre-colonial
Fada dated from Buhari’s time, as did the
modality of managing the Fada itself. And, as we
have seen, Buhari showed little class distinction
in his choice of officials.
The man might have been a rebel; but
Muhammadu Buhari was not a rebel without a
cause.

Sunday, 19 June 2016

SHEDAR KYAFTIN H.C.E PHILLIPS (MAI TUMBI) AKAN GANUWAR HADEJIYA.

SHEDAR KYAFTIN H.C.E PHILLIPS (MAI TUMBI) AKAN GANUWAR HADEJIYA.

HADEJIYA BABBAN GARI NE SOSAI KUMA TANA DA GAWURCACCIYAR GANUWA MANYA-MANYA MASU KYAU SOSAI A  ZAGAYE DA GARIN MAI TSAWO KIMANIN KAFA TALATIN GABA DA BAYANTA, TA KO INA A ZAGAYE DA ITA, AKWAI KOFOFI GUDA BIYAR KADAI, ITA KANTA GANUWAR KAURINTA YA KAI KAFA TALATIN DAGA KASA. KYAMARIN KOFOFIN MASU KARFI NE SOSAI YADDA HARSASHIN BINDIGA BAZAI IYA FASASHI BA CIKIN SAUKI, YAWAN JAMA'AR DA KE CIKIN GARIN SUN KAI KIMANIN DUBU TAKWAS ZUWA DUBU GOMA. FADIN GANUWAR GARIN YAKAI KIMANIN MAYIL HUDU DA RABI.

Wannan ita ce Shaidar da (H.C.E PHILLIPS) ya yi wa ganuwar Hadejiya, Nasamu wannan Shaidar ne a cikin wata wasiqa da (KYAFTIN H.C.E PHILLIPS) ya rubuta zuwa ga (LARYMORE) a watan 17
Disamba, 1903.

SOURCE: LITTAFIN RUWAN ATAFI

Saturday, 18 June 2016

THE SHORT HISTORY OF HADEJIA PART 3

The reason for this behaviour was, according to
oral tradition, that Buhari was averse to the idea
of fighting his junior brother for the throne. It
could well be that he felt his brother was no
more than a pitiable pawn of the Sokoto power
brokers. When in the aftermath of the battle of
Takoko Ahmadu was pursued and executed by
Sarkin Arewa Tatagana, Buhari was disconsolate:
“why”, he lamented, “did you have to kill my
poor brother.”
The battle of Takoko was itself forced on Buhari.
A year after he was driven out of Hadejia, the
Sultan sent Dangaladiman Sokoto to the capital.
His mission was to continue where his brother,
the Waziri, has left off. At Hadejia the
Dangaladima and Ahmadu were joined by
contingents from Kano, Katagum, Misau and
Jama’are. A joint attack was then launched on
Buhari at his camp, leaving him no alternative
but to fight back. Indeed, Buhari used the
opportunity to drive the Caliphate allies beyond
Hadejia city, and re-enter the palace. In a rather
hollow gesture, the Sultan now appointed Tukur,
another junior brother of Buhari’s, as his own
“Emir” of Hadejia. Tukur died in 1904, having
lived quietly for the rest of his life in Kano and
Katagum emirates.
Gamon Kaffur Barely a year after Buhari re-
entered Hadejia, Sultan Aliyu organised perhaps
the most menacing expedition against him. This
time virtually all the major Sokoto emirates were
involved. Apart from Sokoto itself, there included
Zamfara, Zaria, Kano, Katagum, Bauchi, as well
as Gombe, Misau and Jama’are.
According to some estimates horses alone
numbered at least 20,000. The Kanawa
contingents were led by Galadiman Kano
Abdullahi. Overall command fell to the Sultan’s
strongman, the formidable Wazirin Sokoto,
though his was more or less a supervisory role
only. Sarkin Miga Umaru was supposed to show
the way because he was the one most familiar
with the approaches to Hadejia. For all the
difference that made, the expedition could as
well have been guided by a blind man………
To be fair, Sarkin Miga cannot be blamed if the
expedition chose to move in a formation that
had always been vulnerable to an ambush.
Because once the allied units converged on
southern Hadejia, they had formed in solid
phalanxes, moving forward in a slow, confident
procession towards the capital. Somebody
should have told them that that was the sort of
thing you don’t do, especially in an area with
which you are not thoroughly familiar. Certain
units of Federal troops were fond of this type of
advance during the Nigerian civil war, and were
made to pay dearly by relatively ill-equipped
Biafrans.
The allied expedition confident – indeed over-
confident – in its numbers was oblivious to any
imminent danger. They had anticipated that they
will not meet any real opposition till they reached
the Hadejia walls, and once there had no doubts
whatsoever that they could squash any
opposition Buhari could muster. How wrong they
were…………
Because, as it turned out, Buhari did not stay to
be surrounded in his capital, but intercepted the
expedition forces at Kaffur village, six miles from
Hadejia. The eventual victory of Buhari at this
decisive battle owes, more than any other thing
else, to the fact that he was the one who picked
the field of battle. And his choice of the Kaffur
terrain amply demonstrated his military genius.
Movie buffs are familiar with scenes in old
westerns, where a number of Indians have
suddenly appeared on a ridge dominating a plain
over which certain cowboys have pitched their
tents. To the helpless cowboys the Indians
always seemed to materialize from nowhere, and
their numbers likewise invariably appear more
than is actually the case.
At Kaffur Buhari had, very much like an Indian
War Chief, quietly slipped his men into position
along a high ridge overlooking a broad plain
containing the expedition forces. He then had his
maroka drum out his well-known arrival tune to
the “unorganised mass of soldiery” – according
to Victor Law – resting below. What ensued was
pandemonium. Barden Rinde Muhammadu vividly
described the resulting melee:
“On hearing the drum beat, Galadiman Kano’s
army began to flee. Instead of bridling their
horses’ fronts they bridled their tails. All was
confusion as they attempted to save their lives.
No one stood his ground.”
In the subsequent rout that followed the general
confusion, a number of prominent casualties
were recorded. A son of Sarkin Zaria and three of
Sarkin Kano were killed, as were seventeen sons
of various Kano sarakuna. The Sultan himself
lost a grandson. As for the Waziri, we was
reportedly seen riding at full rein and would later
surface at Shira town, some seventy miles from
Kaffur.

Thursday, 16 June 2016

The Short History Of Hadejia Part 2

The Reign of Muhammadu Buhari Sambo

In the year 1848, Sultan Aliyu of Sokoto
sanctioned the selection and installation of
Muhammadu Buhari as the 4th Emir of Hadejia.
This approval by the Sultan though important
was not in fact essential: Buhari would have
installed himself even had the Sultan vetoed the
idea. As it were, Buhari was turbaned at Hadejia
by the Sultan’s envoy and second-in-command,
the Waziri of Sokoto. And thus began the reign of
the most controversial figure the Emirate, if not
the Caliphate, had ever produced.
Buhari was and still remains a different thing to
different people. He is one of those figures about
whom it is impossible to be neutral: one either
detests them, or adores them. To his detractors,
Buhari was ruthless, a rebel and an infidel to
boot; while to his supporters he was a great
administrator, a superb general and a
progressive leader who numbered among his
closest advisers persons of servile origin.
Succession Whatever else may be said about the
man, it has to be admitted that on the issue of
succession, Buhari had a valid claim to the
throne. Just what was the reason which made
Sambo attempt to by-pass Buhari and oft for the
junior brother, Ahmadu, as the Emir designate
will never be known. But going by past
precedents, the attempted change in the normal
though unwritten rule of succession was quite
unfair to the elder son.
When Sambo, Buhari’s father, came to the throne
in 1808, he appointed his eldest son, Garko, as
chiroman Hadejia and thus by tradition heir
apparent. In 1845 Sambo, already a
septuagenarian, abdicated his throne and
appointed Garko Emir. He then offered the post
of Chiroma to his second son, Abdulkadir. A few
years later Garko died. So it was a
straightforward issue, and in keeping with
traditional rules, for Sambo, still very much alive,
to crown Abdulkadir Emir, and to appoint his
third son, Buhari, as Chiroma and thus the Emir-
in-waiting.
As it happened the waiting was to be very brief
indeed, for Abdulkadir too died only after a few
months. Fate itself seemed to be making
Buhari’s ascension to the Hadejia throne quite
smooth and easy. But Sambo decided to go
against fate, and now the troubles began.
Quite inexplicably, and against all established
rules of succession, Sambo decided that
Ahmadu, Buhari’s junior brother, was to be the
new Emir. To this effect he sent a message from
his Camp David-styled retreat, at Mairakumi,
summoning Ahmadu to come and receive some
charms, which will ensure that he prevailed as
Emir over his rival, Buhari.
Unfortunately for the designs of the aged king-
maker, one of the Jakadiyas privy to the
summons was sympathetic to the cause of
Buhari and took no time in passing on the vital
intelligence to the necessary quarters. Always a
man of action, Buhari took the initiative.
Buhari now latched on to the privileged
information to hatch his own counter deceptive
plan. In the ensuing saga which unfolded, and in
subsequent years, he would show not the
slightest hesitation in employing deceit whenever
necessary, to achieve his goals. “The fact is,”
wrote Nicolo Machiavelli, “a man who wants to
act virtuously in every way comes to grief among
so many who are not virtuous.” Like a true
Machiavellian Prince, Buhari was on occasions
definitely not virtuous.
So when he learnt of Sambo’s plan the crown
Prince arrived just ahead of the hour set for
Ahmadu’s visit. Since Sambo was by then
virtually blind, all Buhari had to do was to add to
his other accomplishments the art, or rather act,
of voice mimicry. And this he did so successfully
as to convince Sambo that it was Ahmadu
speaking. Thus Buhari was able to secure the
important formula, which supposedly confirmed
him as the Emir of Hadejia.
Buhari’s Rule Having established his rule, Buhari
set about expanding his realm. It is true that his
approach to this was less than tactful, but then
expansionism was not a business for the
diplomatically inclined.
His first targets were the towns in the Hadejia-
Machina frontier which, with the aid of Sarkin
Misau, he subdued. Then he turned southwards
and invaded the wealthy region of Miga with the
armed support of Shehu Umar of Bornu. Miga,
incidentally, was the town where Buhari as a
child learnt the recital of the holy Qu’ran………….
At Miga a counter-expeditionary force said to
have included some 10,000 horses, was
marshalled against Buhari, but were all put to
flight by him. This emboldened him to carry out
his attacks deeper and deeper into the east Kano
Emirate until at one point, according to the
German traveller Heinrich Barth, he marched as
far as the Kano town walls.
Much closer home, Buhari stationed two of his
ranking officers, the Mabudi and Jarma of
Hadejia, at Kafin Hausa and Dakayyawa,
respectively. Their orders were to carry out
regular offensive raids along the Miga-Jahun
countryside. Such constant harassment of course
had the effect of seriously curtailing both farming
and grazing in the affected areas: it is a very
rare farmer indeed (or animal) that will stay put
while some characters are constantly throwing
nasty missiles all around. As a result, famine
ensued in the Miga-Jahun complex.
This resulting famine might not be altogether
fortuitous. It may well be that Buhari had
calculated that he could achieve his goal of
bringing Kano Emirate to the negotiating table
through a deliberate policy of starving her
subjects – the sort of policy which the late
Awolowo advocated against the Biafrans over a
century later. If that was indeed his plan, Buhari
succeeded admirably. For barely five years of
intimidation later, in about 1857, Buhari and
Sarkin Kano Abdullahi reached an agreement that
ceded to Hadejia a number of towns on their
common boundary.
Now Buhari began to incur the displeasure of
Sultan Aliyu Babba. To be sure, there had never
been any love lost between the duo: after all, the
Sultan would rather have had any of the other
two rivals of Buhari, namely Ahmadu and Nalara,
as the Emir of Hadejia. In fact, it was the
execution of Sarkin Auyo Nalara by Buhari on
charges of disloyalty to the crown, which finally
persuaded the Sultan to take a decisive step to
punish the erring Emir. In view of the eventual
dismal failure of the intended penalty, he should
not have bothered.
To be fair to the Sultan, before resorting to the
use of force he did try to peacefully mediate
between Buhari and Nalara, even to the extent of
summoning both to his presence at Sokoto. The
rivalry was inevitably because of Nalara’s
increasingly assertive claim to the crown. His
claim was by virtue of the fact that he was the
first son of Yusufu, the junior brother of Sambo.
But as any impartial observer will adjudicate,
Buhari had a far stronger claim. So the Sultan
made what he thought was a permanent
conciliation between the rivals, and was
infuriated to learn later that it was nothing of the
sort. But by then, of course, it was rather too
late……………
The man to whom fell the unenviable task of
bringing the supposedly recalcitrant Emir to
order was the very man who, ironically, had been
the major supporter of Buhari’s succession
within the Sultan’s inner circles – the Waziri of
Sokoto. However, the Waziri of Sokoto was not
the type of man to be worried by ironical twists.
Once he had his orders from “the commander of
the faithful” the Waziri would just as easily slay
a man as turban him. Just what exactly were the
precise orders the Waziri received as regards
Buhari is still a matter of speculation. But he
went about carrying them out with the
seriousness of a loyal and devoted general.
Waziri Abdulkadir first landed in kano and picked
up a force of Kanawa military. Under ordinary
circumstances a Sultan’s delegation would go
straight from Kano to Hadejia. But this was an
extraordinary mission, and so the Waziri headed
for Katagum instead. It was to this alleged
neutral ground that the Waziri now, rather
disingenuously, invited Buhari to join him for
“consultations”.
Any reader of present day thrillers can easily see
the net of intrigue about to be woven here. But
possibly because Buhari did not read thrillers, or
more likely because he felt confident enough to
handle any eventualities that might arise, he
accepted the invitation. As an insurance he
arrived outside the gates of Katagum with a
large column, which included all his central
government officials and many loyal sarakuna.
From there he sent word to Waziri within, that he
was ready to negotiate.
But the Waziri insisted on meeting inside
Katagum, claiming that he had a message from
the Sultan. Buhari reluctantly agreed, and got
ready to enter through one of the city gates. Had
he succeeded in doing so, he probably would not
have emerged alive. As it happened, a timely
intervention by one of Buhari’s praise-singers,
Dan Fatima, probably saved his life. “Garba, in
ka shiga,” he exhorted, “ka gaida min Nalara da
Sarkin Dutse Bello.” This rather poignant warning
was enough to make Buhari turn back and, with
his army, head back for his capital.
At this point a section of Katagumawa came into
the act in a somewhat chaotic manner. Infuriated
by the fact that Buhari had refused to “confer”
with the Waziri, the mob followed Buhari as he
moved down the road, shouting “coward”,
“pagan” and other insulting names at him, and
even killing a few of the rearguard. Acts of
hooliganism, it would seem, are not the
monopoly of British soccer fans alone.
Buhari may have departed, but he left behind a
seething Waziri who was yet to accomplish his
mission. Almost immediately he rallied a mixed
army of Kano and Katagum troops and advanced
on Hadejia, forcing Buhari and his nearest
followers to flee northwards to Machina.
Subsequently, the Waziri installed Ahmadu as the
new Emir of Hadejia. Now mission completed, the
Waziri returned to Kano.
Even at this point Buhari did not despair of
peace with the Sultan, for he still sent peace
offers to the Waziri in Kano. However, all his
overtures were summarily rejected. Alhaji Sa’id, a
well-known chronicler and a contemporary of
Buhari, ventured that the Waziri was bribed by
Kano sarakuna to fight Buhari rather than accept
his peace overtures.
Meanwhile Buhari had moved out of Machina
towards Hadejia, with a much larger following.
He encamped near the capital and showed a
curious reluctance to enter it. He would, at will,
attack all surrounding areas but leave Hadejia
town itself alone.

Wednesday, 15 June 2016

LITTAFIN RUWAN ATAFI

     LITTAFIN RUWAN ATAFI
                 NA
      SULEIMAN GINSAU

Littafin Ruwan Atafi littafine da yake dauke da tarihin Ruwn Atafi, da takaitaccen tarihin masarautar Hadejia, yadda aka kafa masarautar Hadejia da tarihin zaman takewar jama'a da tattalin arziki a kasar Hadejia kafin zuwan Turawan mulkin mallaka na kasar Ingila. Sannan wannan littafi yayi duba izuwa tsarin tsaro a kasar Hadejia kafin Mulkin Mallaka, sannan littafin Ruwan Atafi yayi wai waye dangane da irin gudun mawar da wannan ruwa mai albarka ya bayar musammam ga al'ummar kasar Hadejia baki daya, wajen yake-yaken da Hadeji a yake-yaken kasar Hausa a wannan lokacin duk gabas da sakkwato babu wata kasa ai karfi da nuna jarunta da yawan mayaka sadauki kamar kasar Hadejia, kasar Hadejia tayi suna ainun a fagen nuna jarunta. A irin wannan jaruntarne Kasar Hadejia tayi fito-na-fito da Sojojin Mulkin Mallaka na Kasar Ingila a 1906. A wannan fafatawar Mutana Kasar Hadejia suka fatattaki Turawan wanda Sarkin Hadejia Muhammadu Mai Shahada ya kashe Captin Philips wato shugaban sojojin Turawan wanda mutanan Hadejia suke yi masa lakabi da (Maitumbi). Kuma haryanzu kabarinsa yana cikin garin Hadejia. Ana jingina duk wannan jarunta da karfi ga mutanan Hadejia sabi da tasirin Ruwan Atafi. Mutanan Hadejia a lokacin yake-yake sai sukayi wani Rami sannan sukacewa mayakans cewa kowa yaje gida ya dauko Lakanin ko Dafa'i ko Maganin da yake dashi domin suna zubawa a cikin wannan Rami da suka tonahi, sannan sai su bebo ruwa suzuba acikin wannan Rami idan maganin ya tsomu koya juku sai subarshi sai yayi kwana Uku idan zasu fita yaki sai su taro a bakin wannan rami sai a debo wannan ruwa ana basu suna sha suna wanke fuskokinsu da hannayensu, bayan sun gama sai a basu umarni da cewa ATAFI ATAFI ATAFI ma'anar atafi shine sutafi subar wajen daga nan kuma sai filin yaki.

Mu hadu a kashi na 2

Tuesday, 14 June 2016

THE SHORT HISTORY OF HADEJIA PART 1

HADEJIA

Hadejia' (also Hadeja , previously Biram ) is a
Hausa town in eastern Jigawa State , northern
Nigeria . Hadejia is currently the largest and most
important commercial town in Jigawa State. The
City itself has a population of over 450,000
people strangely divided with the influence of the
then Kano State into at least 3-4 Local
government areas. Majorly taken by Hadejia
(southern part of the town, including the old
city), then by Malam Madori (the northern part
including the Shagari Quarters, the GRA, Gandun
Sarki and Gandun bundugoma) and by Guri LGA
(the eastern part, including the Rice mill factory
area). This significantly lowers the actual
population of the area considered as Hadejia
LGA.
History: Prior to the jihadist conquest at the
beginning of the 19th century, the territory now
known as Hadejia emirate consisted of several
separate and distinct Kingdoms whose rulers
received titles from and owed allegiance to the
Habe Galadima of Borno. The former Habe
Kingdoms included Auyo,Garin Gabas
(Biram),Hadejia,Kazura,Gaturwa,Marma,Dawa
and Fagi. The process of the evolution of these
Kingdoms of seems to be obscure except
perhaps for the Kingdoms of Hadejia,Auyo and
Garin Gabas. At the time of the foundation of
Hadejia, a number of small settlements were said
to have existed in the territory that came to be
known as Hadejia emirate. For example,on the
North-eastern side of Hadejia town, there was
Madagwaigwai, whose present site is near
Rubban Dakata a village about 10kilometres east
of Hadejia Kiri kasamma road. While on the
eastern side of the town was Maskangayu
(kulunfardu), a village said to have been
established by Damagarawa immigrants whose
ancestors now live in Hadejia (ILALLAH). The old
site of Kulunfardu was located near Tandanu, just
by the valley of River Hadejia, about 15kilometres
from TURABU. There was a tradition in Turabu
which said that, at the side of kulunfardu, there
was a large Tamarind (Tsamiyar linzamai)
whose branches were said to have bent due to
the weight of the Luggage of soldiers of Mai Ali
of Borno when they camped there on their way to
attack Kano during the reign of Sarkin Kano
Muhammadu Kambari Dan shariff(1731-1734)
By the western side of Hade's camp was
KADIME (still located to the site) which was
about 9kilometre from Hadejia. By the Northern
side of Hadejia was Majeri a few kilometre from
Mallam madori, and by the southern side were
Auyakayi(Tunawa), Unik(Arki), Majawa and
Auyo. These settlement were clearly established
in the surrounding areas much earlier than
Hadejia town.

NOMA DA KIWO SUNFI FETIR INGANTA TATTALIN ARZI.

Tattalin arzikin kasa shi ne irin ma’adanai da ke jibge a karkashin kasa ko samanta da sarrafa wadannan ma’adanai don gina kasa da ’yan kasa.
Allah Ya albarkaci Najeriya da kusan dukkan ma’adanai da kasashe ke iya gadara da su, kama daga Man-Fetur da Iskar Gas, Kalanzir, karfe da tama da karfen kuza da dai sauransu. Amma
wadannan duk ba su ne muhimman sinadaran tattalin arziki da ya kamata kasa ta yi gadara da su ba. Abubuwan da suka kamanci a yi gadara da su su ne, noma da kiwo.
Idan muka yi duba ga kasashen duniya mafi karfin tattalin arziki, za mu ga cewar idan ba dukkansu ba, mafi yawan su, ba su damu da duk wadannan ma’adanai da suke da su ba, wasunsu ma ba su da su balle su yi amfani da su. kasashe irin su
Amurka da Brazil da Sin (China), Indiya, Indonusiya da Jamus, sun dogara ne kacokan kan arzikin noma, yayin da suka yi fice wajen sayer da shinkafa, alkama da masara ga kasashen duniya irin su Najeriya.
kasashen kungiyar OPEC masu fitar da man-fetur mafi yawa a duniya, wadanda suka hada da Aljeriya da Angola da Ekodo da Iran (Farisa) da Kuwaiti da Libya da Najeriya da Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa da benezuela, kusan dukkanin wadannan kasashen ba su iya noma abin da za su ci sai sun sayo abinci irin su shinkafa da alkama daga kasashen waje, kamar su Amurka da Brazil.
A shekarar nan da muke ciki (2014), Gwamnatin Najeriya ta yi shelar karuwar karfin tattalin arzikinta, (wato Gross Domestic Product) wanda ya
kai Dala biliyan 502 (Kimanin triliyon N80.5) a karshen shekarar 2013. Haka zalika, a shekarar 2012 ne ma’aikatar kididdiga ta (National Bureau of Statistic) ta ce sama da kashi 70% na mutanen Najeriya su na rayuwa ne a cikin matsanancin talauci duk da cewar Najeriyar itace ta 8 acikin jerin kasashen OPEC masu fitar da Man-fetur mafi
yawa a duniya.
Kamar yadda kididdiga ta nuna a shekarun baya da suka wuce, noma da kiwo su ke da sama da kashi 70% na tattalin arzikin Najeriya (daga Dalar gyada da kwakwar manja da auduga, Shanu da sauran su), amman a yau Man-fetur ne ya mamaye tattalin arzikin da kusan Kashi 95.3% (Shekara, 2010).
Wannan ta sa shigowa da abinci Najeriya irin su Shinkafa, Siga, Nama, Kifi da Madara ke ta karuwa da kashi 36.7% tin daga shekarar 2011 zuwa yau (Jaridar banguard ta ranar 6/2/2013).
An kiyasta cewar, Man-fetur din da ke jibge a Najeriya bai wuce ganga biliyan 37,200 ba, kuma zai iya karewa zuwa wadansu shekaru masu zuwa (Inji dandalin Wikipedia). Idan muka dauki misali tsakanin Man-gyada da Man-fetur, za mu ga cewar gidan kowanne talaka ana amfani da man-gyada, amma ba kowane gida ne ake amfani da man-fetur ba. Kuma lita daya ta man-fetur din ba ya wuce N97 zuwa N120 amma lita daya ta man-gyada takan kai har N250, kuma har ila yau man-gyada baya fuskantar barazanar karewa kamar na man-
fetur.
Arewacin Najeriya ce ke da filin noma da kiwo, a cikin duk tafiyar mil 100 da mutum zai yi a Arewa, mil 60-70 filin noma da kiwo ne babu gari. Har ila yau, Arewan ce ke da tafkuna irin su tafkin Chadi da Chalawa, Tiga da Rima da koguna da suka ratsa daukacin yankin wanda ke dauke da filayen noma da kiwo. Jihohi irin su Kano da Kaduna da Borno da Benue da Adamawa da Filato da Taraba kawai, za su iya noma shinkafa da doya da alkamar da mutanen Najeriya za su ci a shekara idan aka kula da bada taki da iri mai kyau akan lokaci. Haka zalika in muka koma kiwo, babu wata
Jihar Arewacin Najeriya da babu wuraren kiwo (wato Lawani). Samar da Nama da Fata da Kashi da gashi da da duk wani abin da ake bukata daga Saniya, Akuya/Tunkiya, Rakumi, Kaji/Zabi ko Kifi sai a yankin Arewacin Najeriya.
Amman abin mamakin shi ne, wadansu abokan zaman mu a Najeriya (daga yankin kudanci) na kiran mu da cima-zaune, ma’ana mu ‘yan arewa bama tallafa wa Tarayyar Najeriya da komai na kudin shiga kamar yadda Neja/Dalta ke yi, wannan
kuwa ya farune don shugabannin mu na arewa sun gagara kyautata ayyukan noma da kiwo a yankin namu, sun bar al’amurran kudin shigar su daga albarkatun man-fetur kawai. Don haka nema wasu daga cikin su ke kiran a raba Najeriya don su a ganin su, yunwa ma za ta kashe mu idan aka rabu,
domin ba mu da man-fetur a yankin mu. Amman sun manta da cewar, duk wani tumatiri da albasa da tattasai da attaruhu da naman saniya da akuya da tunkiya, daga wurin mu ake kai musu.
Duk da cewar man-fetur yakawo ci gaba, amman kusan za a ce namai tonon rijiya ne. Kafin samun man-fetur a Najeriya, babu cinhanci da rashawa, babu nuna bangaranci, kabilanci ko kungiyoyi masu
fada da Gwamnati akan man-fetur, amman yanzu duk wadannan sun zama ruwan dare. A wancan lokacin, abinci bai gagari talaka ba, domin zai iya noma abin da zai ci a gonarsa, amman yau kowa ya koma sa rai a ayyukan gwamnati ko kamfanoni,
anyi watsi da noma balle kiwo dalilin ko-in-ku Siyasa, bangaranci da kabilanci, da wariyar addini sun taimaka wajen yin ko-in-kula da bangaren noma da kiwo musamman daga gwamnatin tarayya, irin hakan ta faru a kasafin kudin 2014 na
gwamanatin tarayya yayin da za ta kashewa tsagyerun Neja/Dalta biliyan N35 amman kuma, aka warewa bunkasa tattalin arzikin Arewa maso Gabas biliyan N2 kacal, yankin da ya kunshi jama’a sama da miliyan 19 (kidaya, 2006).
Abinda nake so jama’a su fahimta anan shi ne, Noma da Kiyo su ne tattalin arzikin da kowace kasa take la’akari da su. Domin dukkanin kasar da ba za ta iya ciyar da kanta ba, tofa ba ta kai a kirata kasa mai cin gashin kanta ba.
Kiraye-kirayena ga dukkanin matakai na
gwamnatocin kasannan su ne, inganta harkokin noma da kiwo za su kara kudaden shiga kuma su samarwa talakawa ayyukan yi. Samar da ingantaccen iri da taki akan lokaci, koyar da kiwon kaji, kifi, shanu, awaki da tumaki wa talakawa zaiyi matukar rage radadin talauci, samar da basuka wa al’umma don harkokin noma da kiwo, samar da
isassun masana akan harkokin noma don ilimantar da al’umma akan noma da kiyo, samar da kamfanonin sarrafa kayan gona irin su kamfanin tumatir, da dai sauran hanyoyin da suka dace don inganta wannan sashin, zai kara arziki ga kasa, ya rage talauci da kimanin kashi 70%, ya kuma kawo zaman lafiya da cigaban kasa kamar yadda akace ‘
NOMA TUSHEN ARZUKI.
Fatana dai shi ne mu sani cewar, koda
zamantakewar mu ta kare da masu man-fetur, to mune muke da dawwamammen tattalin arzikin da za mu rike kanmu da shi, wato ‘Noma na duke tsohon ciniki.......’, kuma dole su yi kasuwanci da mu wajen sayen dabbobin mu da kayan masarufin
mu tun da ba a shan man-fetur.
Allah ya taimaki kasar mu Najeriya, amin.

Suleiman Ginsau
Association Of Nigerian Authors ANA