Friday, 28 February 2020

Sama da Shekaru 50, Marigayi Sa'adu Zungur Yayi Wannan Wa'azin a Sigar Waka

~ Matukar a arewa da karuwai,
~ yan daudu dasu da magajiya.
~ Da samari masu ruwan kudi,
~ Ga mashaya can a gidan giya.
~ Matukar yayan mu suna bara,
~ Titi da Loko-lokon Nijeriya.
~ Hanyar birni da na kauyuka,
~ Allah baku mu samu abin miya.
~ Sun yafu da fatar bunsuru,
~ Babu mai tanyonsu da dukiya.
~ Babu shakka yan kudu zasu hau,
~ Dokin mulkin Nijeriya.
~ In ko yan kudu sunka hau,
~ Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
~ A Arewa zumunta ta mutu,
~ Sai karya sai sharholiya.
~ Camfe-camfe da tsibbace
tsibbacen,
~ Malaman karya yan damfara.
~ Sai karya sai kwambon tsiya,
~ Sai hula mai annakiya.
~ Ga gorin asali da na dukiya,
~ Sai kace dan annabi fariya.
~ Jahilci ya ci lakar mu duk,
~ Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
~ Ya daure kafarmu da tsarkiya.
~ Bakunan mu ya sa takunkumi,
~ Ba zalaka sai sharholiya.
~ Wagga al’umma mai zata yo,
~ A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
~ Zaya sha kunya nan duniya “.
~ “Mu dai hakkin mu gaya muku,
~ Ko ku karba ko kuyi dariya.
~ Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
~ Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.
~ Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.
~ Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
~ Marigayi Sa’adu Zungur a cikin
~ waken sa mai suna “Arewa
~ Jamhuriya ko Mulukiya”

Allah Yajikan Malam Saadu Zungur 

No comments:

Post a Comment