Tsakure
Wannan maqala an shirya ta ne da nufin dubawa da kawo gudummawar marubuta wurin havaka tattalin arziqin qasa a jihar Jigawa. A qasashen da suka ci gaba wannan batu ba sabon abu ba ne domin dama dai masu hikima kan ce “dillalin wada shi ya san kuxin jariri”. Babu wani ja in ja, idan muka ce harkar rubutu a sassan duniya ta fi ta man fetur da duk wani ma'adani na lu'ulu'u da zinare da azurfa da zabarjadi da kuma yaqutu muhimmanci. Domin kuwa, duk waxannan ma'adinai na qarewa amma fikirar xan'adam za ta ci gaba da wanzuwa ne a doran qasa matuqar mutum guda na numfashi. Sai dai, wannan aiki ya yi nutso ne tare da ninqaya cikin kogin nazari a jihar Jigawa domin ita ce farfajiyar binciken. A dalilin haka, an yi gabatarwa da bayanin kevavvun kalmomin nazari da hanyoyin gudanar da bincike da sakamakon bincike wanda ya qunshi gudummawar marubuta wurin havaka tattalin arziqi a wannan jiha mai albarka. Don haka, wannan tattaunawa da za a zayyana a yau dama ce kuma burgami na musayar ra’ayi a tsakanin mahalarta wannan taro, sannan ma’auni ne na tantance matsayin marubuta a tsakanin al’umma ta fuskar bunqasar tattalin arziqin wannan jiha ta Jigawa.
1.0 Gabatarwa
A wannan rana ta yau, na xauki gabatar da wannan maqala a matsayin wani al’amari mai matuqar muhimmanci a gare ni, kasancewar zan gabatar da rubutu na ne a kan marubuta da rubutunsu kuma a gaban marubutan. A xabi’a, na ta so ne da son karatu na kowane irin abu da kuma girmama baiwar marubuci. Dalili kuwa shi ne, su marubuta a cikin kowace al’umma, mutane ne da suka fi shahara da baiwa da fikira da tunani da kuma hangen nesa. Marubuta na da halittaccen tabarau na hango burace-burace da qudurce-qudurcen da ke birnin zuciyar al’umma da suke tafikar da tunaninsu. Cikin salale da dabaru da kuma hikimomi marubuta kan rattaba waxannan burace-buracen a kan holama su kuma qawace su da ruwan tawada ta hanyar amfani da alqalami wanda yake dacewa da dukkan zamanin da al'umma ta tsinci kanta a ciki.
Surar da ta fara sauka a al’qur’ani ta yi umarni ne da karatun duk wani abin karantawa muddin an haxa shi da sunan Allah, surar Iqra’a. Sannan a aya ta 13 cikin surar Hujurat an bayyana muhimmancin nazarin harshe, ciki har da rubutu. Haka kuma, Ubangijinmu Allah ya bayyana tasirin amfani da tunani wurin warware wa al’umma matsala, don haka, yake qarfafawa mutane gwiwarsu da su yi amfani da hankali da ilimin da ya ba su domin yin nazarin abubuwan da ya halitta a kewaye da su ta hanyar nazari da rubutu su kalli halittar Allah, su warware matsalolinsu na rayuwa. A cikin suratul Ali Imrana sura ta uku aya ta (190- 191) Allah yana cewa:
Lallai ne, a cikin halittar sammai da qasa da savawar dare da yini akwai ayoyi ga masu tunani (ma’abota hankali). Waxanda suke tunawa da Allah a tsaye da zaune da a kan sansaninsu, kuma suna tunani a kan halittar sammai da qasa. Ya ubangiji ba ka halicci wannana kan banza ba. Tsarkinka! Saboda haka, ka tsare mu daga azabar wuta”. (Gumi, 1985:158)
Qiyasin al’ummar Jigawa dai ya nuna kashi 98% musulmi ne kuma suna wakiltar musulunci ne da musulmi cikin rubutunsu da duk wata fasaha da al’amuran rayuwa. Don haka, waxannan hujjoji na baya qunshe suke da matsayin marubuta a mahangar addini da rayuwa. A yanzu zamu qusa cikin gangar jikin maqalar, mu fito da samuwar rubutu da gudummawar marubuta a harshen Hausa da kuma bayani kan jihar Jigawa musamman ta fuskar ilimi da kuma tattalin arziqi a jihar Jigawa.
2.0 Kebabbun Kalmomin Nazari
A wannan bagire ne aka duba bayanan masana kan abin da ya shafi samuwar rubutun Hausa da gudummawar marubutan Hausa a fagagen rayuwa da kuma bayani kan jihar Jigawa musamman kan al’amuran ilimi da tattalin arziqin qasa.
2.1 Samuwar Rubutu a Qasar Hausa
Kafin kawo tarihin rubutu da samuwarsa a qasar Hausa, yana da muhimmancin mu kawo bayanin Abdullahi (1977: 2-3) cikin Yahaya (1988), wanda ya nuna cewa, al’ummar Sumerawa mutanen qasar Mesophotamiada su ne suka fara qirqirar rubutu shekaru 5,000 da suka wuce ta sigar zanen surori ko alamomi da suka kai kimanin 600. Masu biyewa Sumerawa su ne al’ummar Sinawa waxanda suke rubutun surori a shekaru 3,500 kuma suna amfani da surori kimanin 5,000 domin isar da saqo. Mutanen Masar su ne maqwabtan qasar Mesophotamia su ma rubutunsu irin na Sumerawa ne a wancan lokacin suna amfani da surori 700 kafin su sauya zuwa na Larabci. Wani fannin rubutu shi ne naLarabci da ya shafe fiye da shekaru dubu biyu da suka wuce.
Fonisiyawa wato al’ummar da ke kusa da Siriya ne suka fara qago rubutun abacada shekaru 3,400 da suka suna amfani da baqaqe da wasula 22. Bayan shekara 1000, sai Romawa suka kwaikwaye suka rubuta harshensu na Latin ta yin amfani da baqaqen abacada guda 23 wanda ya zama tushen rubutun boko.
Idan mun gangaro ga samuwar rubutu a qasar Hausa. Hakan, ya doshi shekaru xari biyar zuwa shida tun daga lokacin da suke baddala haruffan Larabci zuwa Hausa wato Ajamin Hausa. Yahaya (1988). Bayan shekaru xari biyu zuwa uku aka sami rubutun boko na Hausa. Don haka, harshen Hausa ya rabauta da hanyoyin rubutu iri biyu da yake adana adabinsa da al’adunsa da kuma shi kansa harshen. Sai dai Abdullahi (2013), ya qalubalanci Hausawa da cewar ba su da rubutun kansu har zuwa yau, kuma ya kawo mafita cikin littafinsa na “Rubutun Tafi”.
2.2 Gudummawar Marubutan Hausa A Fannonin Rayuwa
Marubuta sun daxe suna luguden kalmomi da baje koli fasaharsu a fannoni da dama na rayuwa cikin hanyoyin adabi da waqa ko labari ko wasan kwaikwayo ko kuma fim. Rubutu mafi daxewa dai shi ne na waqa da aka fi amincewa da an fara tun a qarni na sha bakwai zuwa yau ta sigar ajami, ko da yake akwai waqoqin da suka shafi addini zalla a qarnukan (17 da 18 da kuma 19) da waqoqin haxakar addini da rayuwa da kuma waqoqin rayuwa zalla (20 da 21).
Cikin mashahurin littafin da har kwanan yau ba a samu kamarsa ba kan tarihin rubuce-rubucen Hausa, Yahaya (1988), ya bayyana samuwar rubutun boko na Hausa tun a qarni na sha shida. A qasar turai, wato Denmarka aka fara renon rubutun, kuma a can ne Turawan suka fara goyonsa. Sannan wasu daga cikinsu, sun biyo shi qasarsa ta haihuwa tare da shayar da shi mama. Da suka ga ya fara ta-ta-ta sai suka nemo magadansa suka haxa shi da su har ya fara tafiya dagwai-dagwai. Daga nan, aka sami marubuta qagaggun labarai ‘yan gida, a lokacin hukumar talifi (Zangon Imam: 1933), da na kamfanin gaskiya da lokacin NORLA, har zuwa Zangon NNPC zuwa na Adabin zamani da ya shiga qarni na ashirin da xaya. An kuma samu ci gaba wurin rubutun labari a mayar da shi fim musamman a wannan sabon qarni da muke ciki. Adamu, A. da Adamu, Y. M. da Jibril U.F (2004).
Shi kuwa fitaccen farfesa na harshen Ingilishi wato Kamal (2014:200) ya duba litttafan hikaya ne ta fuskoki biyu na Ingilishi masu da’awar aqidar boko zalla da kuma littafan hikaya masu da’awar musulunci. Hakan ya sa, rubuce-rubucen farfesan suke wakiltar musulunci da Hausawa. Haka, kuma rubuce-rubucen marigayi Gimba (2015) suma sun tabbatar da samun rubuce-rubuce na hikaya masu da’awar musulunci cikin harshen Ingilishi.
A vangare guda rubutun wasan kwakwayo ya fara ne daga zuwan rubutun boko kuma shi ne auta a cikinsu. Cikin bayanin Yahaya (1978:6-8) da Omotoso, da Skinner (1978) sun nuna yadda musulunci ya hana samuwar wasan kwaikwayo a cikin ajami. Sai dai Ahmed (1987:4) ya yi iqirarin cewa za a sami rubutaccen wasan kwaikwayo da aka yi da ajami kafin a fara yi da boko, tun da an same shi a tsakanin wasu al’ummatan da ke amfani da tsarin rubutun ajami. (Malumfashi 2014:265).
Domin bayyana matsayin marubuta a al’umma Adamu (2010), ya bayyana cewa babu al'ummar da za ta ci gaba matuqar babu marubuta a cikinta domin kuwa su ne ke tattara tarihin al'ummarsu su adana shi cikin rayayyen adabi. Farfesan na kimiyyar qasa ya duba marubuta ne ta fuska biyu wato waxanda ake haihuwarsu da baiwar da kuma waxanda suke koyo. Domin tafiya bisa wannan turba, Abba (2020) ya qara da cewa"ko xan baiwar rubutu ba ya gane hakan sai ya fara rubutun ne baiwar take bayyana”. Hakan tasa ya ke gani ya kamata marubuci ya zama tamkar quli-quli wanda ko'ina ka juya shi zaka same shi yadda kake so.
Domin qarin bayani kan na baya, Adamu (2010), ya sake fito da muhimmancin marubuta a cikin al'ummarsu inda yake nuna cewa marubuta sun bambanta da sauran mutane ba wai don sun fi su ba, sai don baiwar da Allah ya yi musu ta tunani wadda sauran mutane ba su da ita. Haka kuma, tunanin marubuta ya bambanta da na sauran al'umma domin sukan kalli rayuwa da al'amuran da kan je su komo da wata fahimta ta daban, wannan tunani shi ne yake sauyawa ya zama rubutu da za mu iya kallonsa a matsayin tafsiri na rayuwa.
Domin qarin bayani kan marubutan adabin zamani, Adamu (2010) ya yi wawaye kan annobar da ta samu marubuta musamman na qasar Hausa daga lokacin da kamfanin wallafa littafai na NNPC ya dakatar da buga littattafai, marubuta na wannan zamani suka shiga halin ni ‘ya su. A cikin wannan hali Farfesan ya ambaci wasu jigajigan marubuta Hausa da suka haxa da Talatu Wada Ahmed da Farfesa Yusuf Adamu da Ado Ahmad Gidan dabino da Sunusi Shehu Daneji da Xan 'azumi Baba Cexiyar 'Yangurasa da su Balaraba Ramat Yakubu da da Adamu Muhammad da Alkhamees D. Bature da Bala Anas Babinlata da sauransu da yawa suka jagoranci naqudar Adabin Hausa na zamani.
Shehin malamin ya rufe batun da cewa, haqiqa zan iya cewa gudummawarsu ta taka rawa wajen dawwamar da adabin Hausa na zamani har ya zama a raye zuwa yau. Haka kuma, tagomashin da waxancan marubuta adabin zamani suka bayar ya sa harshen Hausa ya zama cikin manyan harsunan da ake rubutu a cikinsa.
Adamu (2008), farfesan ilimi da sadarwa, shi ma ya jagoranci gyara wa marubuta sahu musamman na fasahar fim. Hakan, ya jawo sa-toka-sa-katsin da suka yi da wasu shahararrun ‘yan fim. A vangare guda kuma, ya jawo rashin mutuwar rubutu cikin gaggawa. Domin da kasuwar adabi na littattafai ta fara da kushewa, sai marubutan suka fara sauya sheqa suna rubutun fasaha. A yau muna da fina-finai masu dogon zango daga taskar marubuta irinsu “daxin kowa” da kuma “kwana casa’in” wanda gwamnatin wannan jiha ta bayar da gudummawa ta musamman kan xaukar shirin a cikin jiharta.
Shi kuwa rubutu a fanni guda, shi ne amfani da alamomi ko zayyana su ko qyasa su a kan takarda ko wani bagire don sadar da magana wadda xan’Adam ya fi faxarta da baki a ji da kunne (Yahaya, 1988:1). Haka kuma, rubutu hanya ce ta isar da saqo cikin sauqi fiye da hanyar magana ta baka wadda ke cike da sammatsi tsakanin mai magana da wanda yake sauraro da wahalar yin tafiyayya da gudun mantuwa. Ko ba komai mun san “kai riqo yake amma ajiya sai rubutu”. Tun da rubutu ne yake wakiltar mai shi, don haka, buqatar qwarewa da amfani da hikimomi da adon harshe ke qara masa armashi da kuma sauqaqa salon marubucin.
Masana sun bayyana rabe-raben marubuta ta fuskoki biyu—qagaggu da na haqiqa; wannan maqala ba ta bai wa wani vangaren rubutu fifiko ba domin kuwa, “da nonon da aka saya da wuri da kuma wanda aka saya da xari duk farinsu xaya”. Tabbas, marubutan Hausa karanku ya kai tsaiko domin kuna cikin mashahuran limaman gyara da daidaitawa al'umma sahu ta fuskar ilimi da zamantakewa da siyasar rayuwa da wayar da kan al'umma.
2.3 Jihar Jigawa
Kirarinta shi ne tarin Allah, musamman saboda jihar Jigawa ba a dunqule take wuri guda ba, haka kuma ana yi mata kirari da sabuwar duniya. Tana da masarutu guda biyar. A fahimtata warwatsuwar Jigawa ‘yar manuniya ce ta havaka da bunqasar sassanta cikin qanqanin lokaci. Babban birnin jihar shi ne, Dutse a masarautar Dutse. Sauran masarautun sun haxa da Gumel da Haxejiya da Kazaure da Ringim.Wannan jiha ce da ta ginu shekaru 29 da suka wuce daga tsohuwar jihar Kano. An qirqiri jihar ranar 27 ga watan Agusta a 1991.
A qidayar al’umma ta shekarar (1991) jihar na da al'umma kimanin 2, 829,929. A shekara ta (2006), qiyasin ya nuna 4, 3000,000 inda ake samun qaruwar al’umma da kashi 3.5% a duk shekara, kashi 48% matasa ne ‘yan shekaru goma sha biyar zuwa qasa. Jiha ce da ke da manyan harsunan guda biyu wato, Hausa da Fulatanci. Harshen da yake biye musu shi ne na Manganci musamman a sassan Birniwa da kiri-kasamma. A vangaren Guri kuma akwai harshen Badanci sannan da harshen Warji a yankin Birnin Kudu. Akwai kuma harsunan da ke magagin mutuwa irinsu Auyakanci da Duwanci a yankin Haxejiya da kwarkwanci a yankin Gwaram.
Ta fuskar ilimi jihar Jigawa na kan gaba da manyan farfesoshi da likitocin ilimi da manyan malamai a fannoni daban-daban da ba za su qidayu ba. Akwai jami’o’i biyu ta tarayya da ta jiha. Ga kuma kwalejin ilimi da fasaha da kimiyya da ayyukan gona da fasahar sadarwa da kuma vangaren lafiya da aikin ungozoma.
Bayan shekaru goma da qirqirar jihar, alqaluma sun nuna cewar jihar na da koma baya ta fuskar tattalin arziqi. Hakan ya zaburar da dattijan jihar wurin yin hovvasa don ganin an samar da hanyoyin havaka tattalin arziqin jihar. Hakan kuma, ya kawo bunqasar tattalin arziqin jihar ta fuskoki da dama.
A jihar Jigawa akwai qungiyoyin marubuta muhimmai guda biyu na ANA da JISWA da suke taka muhimmiyar rawa wurin samar da rubuce-rubuce da wallafe-wallafe da sauran al’amura na fasaha.
3.0 Hanyoyin Gudanar da Bincike da kuma Ra’in Nazari
Wannan maqala takenta da yanayinta da kuma yadda sakamakonta zai kasance ba ta buqatar bin tsohuwar mazahaba ta rubutu daga kwance (Arm Chair Approach) sai dai bin salon nazari ta hanyar tattaki (Empirical Approach). Hakan yasa aka duba Fasalin Jihar Jigawa aka kuma bai wa kowane vangare haqqi bisa masarautun jiha. Ra’in da wannan maqala ta duba shi ne modern technological production, “aikin fasahar sadarwa cikin wallafa” na Karl Max cikin Ado (2017).
3.1 Jama’ar Bincike da Samfurinsu
Jama’ar bincikenmu ta nuna cewa duk da rashin cikakkiyar hujja kan yawan marubuta a jihar Jigawa, sai dai qiyasi ya nuna sun kai kimanin 300-400 daga sassa daban-daban na jihar Lamixo (2020).
Samfurin Jama’ar Bincike:
An xauki marubuta ashirin da ke jihar jiagwa kuma an zave su ne daga vangaren masarautu biyar daga masarautun Dutse da Gumel da Hadejia da Kazaure da kuma Ringim.
Maza
Mata
Adadi
Dutse
2
1
2
Gumel
2
3
5
Hadejia
3
3
6
Kazaure
2
1
3
Ringim
2
2
4
4.0 Sakamakon Bincike
Wannan qarni na ashirin da xaya ya bambanta da sauran qarnukan da suka gabace shi, domin ya fifita sadarwa a kan kowane fanni na rayuwa. Shi kuwa rubutu na xaya daga cikin manyan hanyoyin sadarwa da ya haxa da fikara da kuma qirqira. Hakan yasa, rubutu da marubuta suka zama tushe na samun ci gaban kowace al’umma da ke duniya. Don haka, suka kuma zama manyan tubala na havakar tattalin arziqi.Kasancewar ana yi wa mutum kwatance ne daidai da karan hancinsa, wannan vangare ya fito da ganawar da ka yi da marubuta ashiri (20) ta hanyar tattaunawa ta baka da baka da kuma naxar maganganu da adana su cikin ma’adanin magana a wayar salula.
4.1 Gudummawar Marubutan jihar Jigawa ta fuskar havaka tattalin arziqin qasa
A madadin "gudu da waiwaye wanda ke kawo mugun zato", Usaini (2020) da Mujahid (2020), da Babandede (2020), da Umar (2020), da kuma Inuwa (2020), suka zavi yi wa tafiyarsu ado da waiwaye kan gudummawar marubuta da kuma karvuwar da suka yi shekaru talatin baya, musamman a arewacin Najeriya. A wancan lokacin, kusan kowace jiha akwai marubuta, sannan tsohuwar jihar Kano (da take haxe da Jigawa) ta zamanto cibiyar masana'antar. Kowane marubuci ko marubuciya idan sun rubuta littafin za su zo Kano ne a buga musu kuma su masu bugawar ne ke sayar musu da shi ta hanyar sararwa ko kuma zubawa a shagunansu domin sayarwa. Misali Mandawari Publishing Company da Kasuwar Bata da Al'amin Publishing Company da Gidan Dabino Publishing Company da sauransu. Matan aure masu qaramin qarfi sun xauki sana'ar da gaske kuma tana taimaka musu domin ta hanyar ta ne suke juya taro ya koma kwabo ta hanyar zuwa kasuwannin littattafai su kai tsofaffin na hannunsu a ba su sababbi su komo unguwanninsu suna ba da haya ana biyansu.
Bahaushe dai kan ce “kowa ya raina mai labari, in ka ga mai gudu shi ne”. A ganawar da na yi da Umar (2020), ya bayyana cewa gintsewar tunani ce babba idan aka yi zancen marubuta ba sa cikin masu taimakawa hanyar bunqasar tattalin arziqin jihar Jigawa. A ganinsa vangarori biyu ne suka fi rubutu wato ilimi da lafiya, su xin ma ba sa tava bunqasa sai da tagomashin marubuta. Haka kuma,Bahaushekan ce “Inda yaro ya tsinci wuri, nan ya fi saurin tunawa”, don haka, marubucin ya qara da cewa“a jihar jigawa hanyar rubuta waqa da buga ta da rera ta ya fi tasiri fiye da rubuta qagaggun labari da wasan kwaikwayo da ayyukan fasaha na musamman”.Muftahu (2020) shi ma ya goyi bayan wannan ra'ayi. Qarin haske kan gudummawar marubuta kan bunqasar tattalin arziqi a Jigawa aya samu goyon bayan Ubali (2020), da Ya'u (2020), da Lamixo (2020) da Gumuel (2020) da kuma Binin kudu (2020). Don haka, suka dubi havaka Tattalin arziqin a waxannan fuskokin:
Daidaikun al'umma
Hanyar rubutu tumbin giwa ce; inda ta al’umma ke amfana da ita da suka haxa da 'yan kasuwa iri-iri tun daga masu sana'ar takardu da na alqalami da almajiran da ke cikin kasuwa da ke dakon littattafai da yaran da ke gararamba a kan titi da 'yan tasha da jami'an tsaro da direbobi da masu Sitidiyo (mawaqa da marubuta da masu ‘yan amshi) da masu shago da yaran shago da ‘yan agaji da sauransu kowa yana cin albarkacin marubuta da rubutu.
Hukuma:
Hanyar cike foma-fomai da rasitai da harajin qungiyoyin da na hukuma
Masu sauraro:
Suna samun bunqasar tunani ta hanyar sauroron waqoqi masu amfani tare da karanta littattafai masu ilimantarwa.
Manazarta:
Malaman manyan makarantu da na jami'o'I, shehunnan malamai da likitocin ilimi da sauransu suna samun ci gaba ta hanyar nazari
'Yan Fassara:
Masu fassara fim daga wani harshe musamman zuwa Hausa su ma na samun tattalin arziqi. Rubuce-rubuce na taimakawa gaya domin samun kevavvun kalmomin nazari da qamusu-qamusu na marubuta, haka kuma sababbin kalmomi na shigowa daga bakin mafassaran. Ana yin fassara a rubuce ko a xora murya bayan an gama fassarar akwai kuma masu tace muryar da aka xora, dukkaninsu albarkacin rubutu ne da marubuta.
Bunqasar Arziqi ta Sistam:
Wannan hanya ce da ta zama kamar Ambaliyar ruwan arziqi ga wanda ya shige ta. Babu wulaqanci,babu karya tattalin arziqi, babu “wa-ka-ci- ka tashi” a ciki ko “kan tawaye”. Mutum yana iya yin tallar liittafinsa ko waqarsa ko wata fasaha yana kan gadonsa ta hanyar turawa 'yan kwamadi domin su tallata hajarka, a youtube, tare da bayar da link xin da za a shiga domin samun littafin ko waqar. Kafafe na sada zumunta su ma za su bunqasa wannan haja misali, “whats’up” da “face book” da sauransu. Duk lokacin da mutum ya shiga link xin akwai kaso da zai faxa asusun marubucin. Ana kuma iya buxe shafi ta rariyar liqau wadda yawan jama’ar da suke ziyartar shafin tamkar su ne jarin marubuci, yayin da suka kai wani qiyasi daga nan marubuci ya zama kadara. Fitattun shafukan utube sun haxa da “Tsakar gida da Hausa Top TV”.
Tallata gari da yanki:
Ta hanyar marubuta jama’a na sanin gari da yanki kuma na jawo jama’a su shigo su kafa dandali tare da baje kolin sana’arsu, inda kuma al’umma ta yawaita wasu abubuwan ci gaba.
Kai kukan al’umma ga hukuma
Jiha da al’ummar cikinta na samun ci gaba yayin da marubuta suka fito da matsalolinsu, kuma suka isar da su ga hukuma ta hanyar rubuce-rubuce. Musamman yadda ake amfani da sababbin fasahohin sadarwa irinsu, whatsup da face book da sauransu.
Makarantu/ cibiyoyin ilimi
Ana samun ci gaba daga fikirar marubuta a cibiyoyin ilimi da makarantu, ta wannan hanyar ana ziyartar su domin bunqasar tunani da nazari, kuma ta wannan hanya duniya kan san marubuci. A irin waxannan hanyoyi fitattun marubuta suka yi shura suka fito aka sansu a duniya.
Bayanin sakamakon bincikenmu ya nuna cewa, kashi 55% na marubutan da aka yi wa tambayoyi, (musamman waxanda suke cikin qungiyoyin marubuta) sun gamsu da cewa suna bayar da gagarumar gudummawa wajen havaka tattalin arziqin qasa,domin idan kura na da rabo ajikin takobi sai a sayar da shi a sayo akuya”. Amma kashi 45% cikin xari na marubutan na ganin rubutu a matsayin “wutsiyar tsaka mai gautsi” ", musamman idan muka duba matsalolin da suka yi kaka-gida a duniyar rubutu da marubutan wannan jiha ta Jigawa.
4.2 Matsalolin da Marubuta ke fuskanta a jihar Jigawa
Hausawa kan ce kuma “muguwar miya dai ba ta qarewa a tukunya”, hakan na nuni da tarin matsalolin da marubutan jihar Jigawa suka bayyana yayin nemo bayanai kan wannan batu.
1. Matsalar al’umma:
Rashin xaukar aikin fasaha da daraja daga al'ummar qasar Hausa
Nuna kyama da hantara da nisanta daga al’umma.
Rashin xabi’ar karatu.
2- Hukuma:
Matsalar tsaro
Kasuwar talifi/tallatawa guda xaya
Rashin tallafi
Rashin tausayi daga vangaren hukuma
Qarfafa gwiwa da sanya gasa
Satar fasaha
Rashin sanya littafan zamani a cikin manhaja
3- Matsalar Marubuta:
Rashin faxaxa ilimin rubutu
Rashin ilimi kan sabuwar fasahar sadarwa
Rashin amfani da qa’idojin rubutu
Rashin jituwa da musayar ayyuka
Rashin bincike yayin rubutu
Rashin kuxi
4.3 Hanyoyin Inganta harkokin Rubutu a jihar Jigawa
Ma’abota hikima dai na cewa “kuwwa da kuwwa ba ta korar buzu”, kuma “tsakuwa xaya ba ta dave”, hakan ta sa wannan maqala ta kawo shawarwari daga ɓangarori mabambanta da za a inganta harkar rubutu da kuma marubutan, ta waxannan fuskoki:
1- Marubuta:
Ilimin rubutu/qa’idojin rubutu/sabuwar fasahar sadarwa/musayar ayyuka/rashin kuxi
Qwarewa ta fuskar koyo
Qirqira
Kaifafa tunani
Haxin gwiwa
Sadarwa
Qwarewa ta fuskar ilimi
Nemo bayanai
Amfani da kafafen saadaewa
Sanin sabuwar fasahar sadarwa
Qwarewa ta zamantakewa
Sauqin hali
Jagoranci
Samar da wallafa
Iya mu’amala
2- Hukuma:
Yarda da cewa marubuta za su magance matsalolin tavarvarewar tattalin arziqi a tsakanin al’umma;
Jan marubuta a jika da nuna musu su ma mutane ne masu daraja;
Samar da dokar kare martaba da tsaro ga rayuwar marubuta;
Samar da kasuwar talifi/tallatawa a kowace masarauta da kuma babbar kasuwa a babban birnin jihar Jigawa, wato Dutse;
iii) Fitarwa harkar wallafa kasafi na kuxin jiha/qasa;
Adalcin hukuma kan kuxaxen haraji da foma-fomai da rasitai;
Qarfafa gwiwa da sanya gasa a tsakanin marubuta daban-daban da ke jihar da ma qasa baki xaya;
Amfani da fasahar sadarwa domin kamawa da daqile satar fasaha;
Samar da tsarin haxaka na malamai da manazarta da kafafen sadarwa da marubuta domin musayar ilimi;
Samar da tarurruka iri-iri masu alaka da wannan.
3- Al’umma:
Wayar da kan al’ummar da ke qasar Hausa a kan:
Daina nuna qyamata da hantara da nisantar marubuta ta hanyar kafafen sadarwa da malam addini da kuma Malaman zamani;
Samun karsashin xabi’ar karatu ga al’umma tun daga matakin ilimin firamare zuwa jami’a da sauya salon koyarwa da cusa karsashin karatu tsakanin yara qanana, musamman ta amfani da shirin Rana da DFID ya xauki nauyin tallafawa jihohin Arewa ciki har da jihar Jigawa.
Shigowar sarakuna da mawadata da mala cikin harkar marubuta
Samar da tsarin karatu a cikin gidajenmu
Kammalawa:
Ma'abota wannan taro,mu tuna da cewa "idan kaji mutum na tsoron dare ba a xaure shi ya kwance ba" kuma “In ka ji na qiya samun dama ne”, haka kuma “matsi shi ke sa kalangu zaqi.A yau duniya ta dunqule wuri guda ta zama xan qaramin qauye na hulxa da juna cikin sauqi musamman ta fuskar sadarwa ta rubutu. Don haka, ya zama wajibi marubutan su tafi da zamani da tsare-tsaren da ke cikinsa masu albarka. Kasancewar an yi wa wannan batu kallon garau tare da nazarin qwaqwaf da Kuma tarken tsatsaf kan gudummawar marubuta wurin havaka tattalin arziqin wannan jiha tamu mai albarka. Da sunan Allah nake qarqare wannan maqala a matsayin tukuici ga marubuta da mazarta da kuma xaliban harshen Hausa na jihar Jigawa da qasa baki xaya, domin kuwa “da babbar rowa gara qaramar kyauta”.
Manazarta
Adamu, A.U. (2008). “Hausa da Hausanci a qarni na 21: Qalubale da Madosa” Taskar Gidan Dabino Being a paper resented at a one day sensitization meeting of Hausa Motion Picture.
Adamu, A. da Adamu, da Y. M. da Jibril U.F (2004). Hausa Home Vedio Technology, Economy and Society. Kano: Gidan Dabino.
Adamu, Y. (2010). Marubuta a Al’umma. Maqalar da aka gabatar a taron Ranar Marubuta.
Ado, A. (2017) Ra'o'in Bincike kan al'adun Hausawa. Maxaba'a Kanku Classique. Katsina.
Gidan Dabino, A.A. (2004). “Matsalolin da Nasarorin masu shirya fina-finan Hausa Musamman na Kano”. In Hausa Home Vedio Technology, Economy and Society. Kano: Gidan Dabino.
Ahmed, U.B (1987). “Muhammad Agigs Trans-Saharan Saga: a critique of An Early Hausa Dramatic Litereture”.
Babandede, B. (2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. Rana:20/1/2020
Birnin kudu, A. (2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. Rana:18/1/2020
Gimba, A. (2015) Scared Apple
Gumel,A.A (2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. Rana: 15/1/2020
Gumi, A. (1985) Tarjamar Ma'anoni Alqur’ani mai girma mai girma zuwa harshen Hausa. Darul Arabiyya lilxiba'ati Wannissar Beruit Lebanon.
Inuwa, M. U. (2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. Rana:22/1/ 2020
Kamal, A. (2014) “The Islamic Novel and Structure’. In Festschrift in Tribute to Abdulqadir Xangambo
Lamixo, A.S. (2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. 13/1/ 2020
Muftahu, M.U. (2020), Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. Rana:25/1/2020
Malumfashi, I. (2014). “Rubutattun Waqoqin Hausa kafin jihadi”. In Festschrift in Tribute to Abdulqadir Xangambo
Mujahid, U.U. (2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa.Rana: 2/2/2020
Omotoso, K. (1976)
Skinner (1980) An anthrophology of Hausa Litereture
Umar, N. (2020), Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa.16/1/2020
Umar , H.(2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. Rana: 28/1/2020
Ubali, M. L. (2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. 27/1/2020
Usaini, A.S (2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. 23/1/2020
Yahaya, I . Y.(1988). Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce cikin Hausa
Ya'u, M. (2020) Tattaunawa kan Gudummawar marubuta wajen havaka tattalin arziqi a jihar Jigawa. 1/2/2020
No comments:
Post a Comment