1. An samu bulluwar wata cutar Dabobi a Kasar Hadejia a 1898 wadda tayi sanadiyar mutuwar dabobi da dama a wancen lokacin.
2. Anyi wata Yunwa a Kasar Hadejia a 1908 a lokacin Sarki Haru Mai Karamba, bayan kammala Yakin Turawan Mulkin Mallaka wadda tayi sanadiyyar mutuwar Jama'a da dama tare da Dabobin su. Mutanan Hadejia suna mata lakabi da (Yunwar Biri).
3. Anyi wata karamar Girgizar Kasa a Kasar Hadejia a 1909.
4. An samu bulluwar wata Cuta (Epidemic Disease) a Kasar Hadejia a 1909 wadda tayi sanadiyyar mutuwar Jama'ar gari da yawa, ta sanadiyar wannan cuta ne Allah ya yiwa Sarki Haru Mai Karamba rasuwa.
5. A zamanin Sarkin Hadejia Abudulkadir a 1914 Farkon Yakin Duniya a Farko anyi wata Babbar Yunwa a Kasar Hadejia wadda sanadiyar mutuwar Jama'a wasu kuma sukayi hijira zuwa wasu garuruwa.
6. An samu bulluwar wata Cuta (Community Disease) a 1917 a Kasar Hadejia wadda mutane suke mata lakabi da (MARISUWA) wannan Cuta ta kama Mutane da Dabobi.
7. Anyi wani Zazzabin Gari mai Zafin gaske a 1925 a Kasar Hadejia wanda yayi sanadiyar mutawar Jama'ar Gari da dama, ta sanadiyyar wannan Zazzabi ne Sarkin Hadejia Abdulkadir Allah ya masa rasuwa.
8. A Zamanin Sarkin Hadejia Usman a 1927 anyi wata Yunwa a Kasar Hadejia wadda mutane suke mata lakabi da (MAI BUHU).
Wanda ba'aga anan insha Allahu za'a gani a kashi na biyu
KASHI NA BIYU NA NAN TAFE