Daga cikin masu ingizawa a yi yaki da Turawa sun yi yekuwa cewa 'kowa ya je gida ya shirya inyaso gobe duk mukwana lahira' ta haka manyan bayi masu sarauta suka ruruta ayi yaki da Turawa, sannan wani abin la'akari a nan shi ne dukkansu suna da hanyoyin da zasu shawo kan jama'a mai tarin yawa a kowana lokaci suke bukata domin suna da dukiya mai tarin yawa da bayi da iko.
Akwai wani dalili kuma da za a dangantashi da halayyar jama'ar wurin, kuma ana shi ne ya karfafa aka goyi bayan ayi yaki da Turawa Turawa. Shekaru da dama Hadejia ta sami shaidar cewa ita jarumar kasa ce (Barth, 1965:545). Masarautar ta kara samun wannan daraja a zamanin mulkin Sarkin Hadejia Buhari wanda saboda kokarin assasa ikonsa ya yaki wurare da yawa har sai da ya dangana da badalar Kano daga yamma (Barth, 1965:45).
Haka kuma a yayin da SarkinHadejia Buhari ya samu galaba akan rundunar daular Sakkwato a yakin Kafur, sai Hadejia ta zama dodo a tsakanin masarautun da suke a gabashin daular. Wasu kuma cewa suke Hadejia ta zama hatsabibiyar masarauta a gabas. (Ja'afaru marubucin tarihin Kano). Shi ma ya ayyana cewa Hadejia ta zama ciji abar tsorobtun a lokacin da ta gagari daular Sakkwato a Kafur, sai ta zama wadda ta gagari kundila.
(Low, 1972:141). Tun daga wannan lokaci aka fashimci Hadejia kasace ba mai tsoro ba kuma jaruma mai karfin gaske. A al'adance kuma ana cewa duk yaron da aka haifa a Hadejia sai an bashi "Ruwan Atafi" ya sha a lokacin da yake jariri domin yaran suna tashi da jarunta da rashin jin tsoro, (Suleiman Ginsau, Ruwan Atafi 2015). Duk wanda yasha wannan ruwa ba shi ba lalaci ba zai ji tsoro ba, zai zama jarumi kuma sadauki.
Saboda wannan yarda da mutanan Hadejia suke da ita a wannan dalili, ake ganin sun ba da kai borin yaki da nasara ya hau su. Suka hakikance cewa ba za ta yiwu su mika kansu ga Turawa ba tare da wata fafatawa ba, kuma suna a sane da hadarin fada wa abokan yakin da ya fi makamai masu inganci. Sun fita fagen daga ne da sanin cewa makaman abokan gaba sun fi nasu nesa ba kusa ba, amma sun yi haka domin su bar tarihi.
Manyan bayi masu sarauta da suke neman a gwabza da Turawa ana jin sun yi ta banza jita-jita kamar yadda abin yake a lokacin da ake hango wutar fara yakin. An shs tafi da tunanin jama'a acikin dabara ta nuna cewa talakawa na cikin halin kaka-naka-yi wadanda suke cikin masarautun da Turawa suka kwace mulkinsu. Haka kuma ake baza labarin cewa talakawan Katagum sun dawo Hadejia, wasu talakawan ma daga Kano sun gudo zuwa Hadejia. Haka dai abin ya ci gaba da wanzuwa sun gudo har sai da talakawan Hadejia suka kai ga kagara da su gwabza da Turawan mulkin mallaka na Ingila. Wani labari kuma da ake ta bazawa ya kara kumbura mutane inda ake cewa Turawan mulkin mallaka suna nan suna kokarin su kama Saeki su fitar da shi daaga sarauta.
Amma a kokarin mayakan Turawa na su kwantar da tarzoma sun yi kokarin nuna wannan labari ba gaskiya ba ne, sai dai talakawan Hadejja ba su saurare su ba domin ma sun kagu su fara yaki. Duk wani namiji mai lafiya, mai jin karfi ya jima da shiryawa. Mazaje sun baro kauyuka sai mata da yara sun zo birni suna dakon yaki da Turawa (Lugard,1911:378).
Da Turawan mulkin mallaka suka gaji da take taken mutanan Hadejia, sai suka tsayar da shawara su shiga Hadejia da yaki ta amfani da karfin soja da suke dashi a wannan lokaci domin sauran kasashen da suke sashen gabas da suke tunanin yin tawaye, kamar dai yadda suka ladabtar da mutanan Satiru (Lugard 1911:378).
Babban abinda ya gaggauta wannan tawaye kuma shi ne umarnin da Lugard ya bayar inda ake ce kowa ya kawowa Turawa makamin yakinsa, sannan kuma a mikawa Turawa shuwagabannin da suke iza wutar a yi yaki kuma a sharewa Turawan hanya mafi sauki da za su shiga cikin garin Hadejia. Wani sharadin na Turawan kuma yana neman a rushe ko a bude wani sashe na ganuwar Hadejia domin a sami hanyar shiga mayalwaciya (Lugard, 1911:378-379).
An sami wannan sako a fadar Sarki daga nan aka tattauna shi a majalissar Sarki amma nan take aka yi watsi da shi wato aka shure shi da kafa. An ce ma wani barde sai yi wuf ya mari masinjan Turawa wanda ya kawo wannan sako wato Ibrahim Tafinta, ya gaya masa ya shaida wa iyayen gidansa wato Turawa cewa su zo da kansu su kama shugabannin tawayen.
A hakikanin gaskiya Turawan mulkin mallaka sun shirya su yi fiye da abin da jarimi Ibrahim Tafinta da 'yan uwansa suke zato. Tuni a lokacin da suka bayyana wa'adinsu sun riga sun a'ajiye makansu a kusa da birni. An ga wadannan mayaka suna sintiri a sashen gabas wato inda suka gina matsugunninsu sojojinsu har zuwa yamma.
Ashe ke nan su ma Turawan Ingila sun riga sun shirya a lokacin da suke dakon su sami amsar mutanan Hadejia kuma sun sami amsar yadda suke zato za ta faru. Daga nan kuma suka ayyana yaki a kan Masarautar Hadejia.
Sai dai a lokacin da Capt. LEWIS ya shiga garin Hadejia sai yaga duk abinda yake faruwa sai ya rubutawa Kwamashina mai kulada lardin mulki na Hadejia wato Resdan wasika a 9th Mayu, 1905. Cewa ina mai ra'ayin 'yan kalilan Sojoji, domin sojojin da suke tare damu anan Hadejia, bazafa su iya tare wata kura da zata iya tasowa a gaba ba. Akwai bukata a aiko mana da Igwa a cikin gaggawa. Kuma ganin babu bukatar Sojoji a Katagum kwata-kwata wannan runduna babba ta Sojojin Kasa da take Katagum lallai a aikata Hadejia a cikin gaggawa (Suleiman Ginsau 2015).
Wadannan wasu dalilai ne da suka haddasa yakin Shahadar Hadejia.
YADDA YAKIN HADEJIA DA TURWAN MULKIN MALLAKA YA FARU...
No comments:
Post a Comment