Tawayen da Hadejia tayiwa turawan Mulkin Mallaka za a iya kallansa ta fuska biyu (2), fuska ta farko (1) ya zama wata hadaddaiyar dabi'a domin dukkan masarauatun da suke karkashin daular masu jihadi ta sakkwato sun nuna rashin amincewarsu da Turawa wadanda suke bakin haure ne masu mulkin kafirci.
- Fuska ta (2) ta shafi masarautar Hadejia ce kawai tun lokacin da Turawa suka shiga Hadejia, Hadejia taki yadda bangonta ya tsage balantana kadangare na gida ko bako ya samu wajen shiga, Hadejia itace masarauta daya jal wadda a wannan lokacin Turawa basu cita da yaki ba (Hiskett, da kuma Larymore, 1975:142). Tazarar da aka samu daga cinye wasu masarautu zuwa lokacin da Turawa suka tursasa wa Hadejia zama karkashin mulkin mallaka, a zashiri ya ba mutanan Hadejia damar su fashimci yadda mulkin Turawan Ingila yake gudana ba kamar yadda dan kallo zai gani daga bayan fage ba.
Yadda mutanan Hadejia suke ganin yanayin harajin Turawa da sassauya mulkin sarauta da manufofinsu ba abin ajidadi ko a yaba bane. Hakika masarautar Hadejia tana da wasu dalilai wadanda suka sa jama'arta suka rinka hamaiya da mulkin Turawa, masaruata Hadejia ta gaskata cewa, Musulnci yana nufin mika wuya zuwa ga dokokin Allah, mahaliccin kowa da komai. Hakika kuma a sane Hadejia take cewa Musulunci bisa zahirin gaskiya yayi kira a bayya ne, dalla-dalla cewa dole ne Musulmi ya tashi tsaye ya kare kansa kuma kada ya yarda da dokokin da bana shari'a ba gwargwadon iyawa da karfinsa. Ashe ke nan ba ta yadda za ayi mutanan Hadejia su saki tsarin Musulunci don su rumgumi tasarin kafirci, sai bisa tilas idan anfi karfinsu, ko da an rinjayesu din ne ai karfin mulki da sarrafa shi za a kwace, amma ba imanin mutum ko Addininsa na Musulunci ba.
Domin haka mutanan Hadejia suka sami kansu cikin wani hali mai wuya, musamman ganin cewa ba ta iyuwa garesu su amince da mulkin kafirai. Zabinsu game da wannan al'amari bashi da yawa kamar yadda dai ta faru a wasu masarautun, ko dai su kaurace wa mulkin Turawa ko kuma su tsaya tsayin daka su kare kansau ko za ta kaisu gayin yaki da su, ko dai kuma suyi kaura, su sake wurin zama.
Sai dai abin tambaya dangane da zabi na biyu ina zasu tafi ne idan suka yi kaura? Ai duka sauran masarutu na daular Musulunci na fama da wannan bala'in na Turawa. Sannan kuma ta yaya Sarki zai kare martabarsa a idon jama'a idan yayi hijira, tun da jama'a na kallan duk Sarkin da ya yi kaura matsoraci ne kuma rago ne wanda ya kauce wa gaskiya. Saboda haka zabin da ya rage shi ne bijirewa umarnin Turawa.
Domin kara wa wannan zabi karfi shi Sarkin Hadejia Muhammadu kammalallen mutum ne, bawan Allah cikakken mabiyin darikar Tijjaniyya, kuma babban jarumi mai fada da mulkin kafirci (Wakili H. 2005). Hakika za a iya cewa darikar Tijjaniyya tana da wasu Malamanta a masarautar Hadejia wanda suke rura wutar a ki Turawa da mulkinsu. Daga cikin misalan wadannan Malamai mabiya darikar Tijjaniyya akwai Malam Ahmadu Madaniyyo wanda ya taso daga Burmi bayan Turawa sun cinye garin da yaki a 1903. Shi wannan Malami tare da almajiransa sun zauna a Dakaiyawa, gari wanda yake kilomita ashirin da huda (24KM) daga Hadejia. Babu shakka, Sarki da malamai da sauran mabiya darikar Tijjaniyya suna mutukar kin Turawa da mulkinsu na kafirci.
Kari akan abubuwan sai maganar "Mahdi" ta kunno kai ta haka wasu suke da ra'ayin cewa tawayen Hadejawa yana da alaka da zuwan Mahdi, harka ta Mahadiyya a matsayin wata hanya ta gwagwarmaya ta kara wa wannan rikici na Hadejia kaimi tare da rurutashi.
Sauraron zuwan Mahdi ya yi babban tasiri a wannan masarautu kamar yadda ya yi tasirin a sauran masarautu makamanciyarta da kuma tun a farkon yake-yaken jihadi da aka yi a karni na goma sha tara (K19). Haka ma ya faru a farkon karni na ashirin (K20) da Turawa suka zo da zimmar kwace mulki a yawancin sassa na daular Sakkwato an dauka cewa zuwansu wata alamace ta bayyanar Mahdi.
A ra'yin Mahadiyya da koyarwarta babu yarda ko amincewa da mulkin mallaka ko wata danniya ta nuna fin karfi (Sa'id, 1972:1) sai dai wasu na ganin rawar da Mahdiyya taka a rikicin Hadejia takaitacciya ce domin ba a gudanar da shi bisa wannan akida ba.
Amma duk da haka za a iya nuna cewa maganar zuwan Mahdi da yawaita magana dangane da kusantowar karshen duniya sun taimaka wajen iza watar fadece-fadace da barkewar wannan yaki.
Babu shakka a lokacin da Turawan mulkin mallaka suka fara yi wa mutanan Hadejia barazana sai suka amince cewa daukar makami su yake su shi ne mafita kuma yin haka jihadi ne na kare Addini ko da kuwa za a mutu. Mutuwa a irin wannan yaki na Musulunci "SHAHADA" ce, shahada kuwa wata kololuwar daraja ce da Musulmi zai iya samu.
An tabbata cewa yawancin jama'ar Hadejia da sukayi wannan yaki sunyi shi ne ba domin wata sha'awa ta su sami galaba a yakin ba, a'a sai domin su yi shahada. Domin haka ne ma mutane suke kiran wannan yaki da Yakin SHAHADAR HADEJIA, shi kansa Sarkin Hadejia wanda ya jagoranci yakin kuma aka kasheshi ana yi masa lakabi da SARKI MUHAMMADU MAI SHAHADA haka duka sauran mutanen da aka kashe ana jin sunyi shahada ne bisa jimlarsu.
Ra'ayi na shahada a Musulunci ta hanyar yaki da kafirci ya kara wa mutanan Hadejia kwarin guiwa su tunkari Turawan mulkin mallaka gaba da gaba ko da kuwa za su rasa rayuwarsu domin su yi shahada abar kuduri. Babu shakka akidar shahada mai nauyi ce matuka a wajen wasu Musulmi.
Haka kuma wani babba dalili mai kwari da ya iza wutar wannan yaki yana da mutukar dangantaka da yanayin zaman jama'a da hanyar gudanar da mulkinsu.
Tawayen Hadejia ba a kamar wasu masarautu ba, ya hada rukunonin jama'a da yawa, da za a iya rabawa zuwa manyan gidaje biyu (2) wato gidan masu sarauta da gidajen talakawa. Wadannan gidaje biyu, bayan suna kan manufa daya, Misali kare hanyar tafiyar da rayuwarsu, haka kuma suna da kananan mabambantan manufofi da suka dace da yanayin kawane gida.
Babban miasali, an ce a lokacin da Turawa suka tunkari Hadejia, ra'ayoyin sun bambanta a tsakanin masu sarauta a Hadejia wato a iya yaki da Turawa ko a sallama musu. Rukunin da yake yayata a yi yaki da Turawan ya hada da:-
1. Sarkin Arewan Hadejia Tatagana
2. Madakin Hadejia Ahmadu
3. Mabudin Hadejia Zakari
4. Jarman Hadejia Warkaci
Wadannan dukkansu suna rike da manyan sarautu na bayi ma'ana bayi ne.
Sai kuma rukunin da yake kaurace wa a yi yaki da Turawan rukunin ya kunshi:-
1. Galadiman Hadejia Usman
2. Ciroman Hadejia
Da mabiyansu wadanda suke rike da manyan sarautu daga bangaran 'ya'ya. Wannan kungiya ta karshe tana ganin ba za a sami wata nasara ta yin yaki da Turawa ba domin sun mallaki manyan makamin yaki wadda Hadejia ba ta irinsu. Kuma sun fashimci cewa idan kida ya canza dole rawa ta canza, ta haka suke ganin ya fi dacewa Hadeja ta mika wuya a maimakon a yi tawaye da zai kai ga zubar da jini da rayukan mutane.
Sai dai su manyan bayin Sariki masu sarauta kuma masu fada aji tun daga zamanin Sarkin Hadejia Buhari (1849-1863), sun kekasa kasa suna ingiza cewa sai a yi fada da Turawa. Kamar yadda aka fada a baya, wadannan manyan bayi sun yi amfani da karfinsu domin su dakushe kowana shiri da za a yi da Turawan Ingila a Katagum da Sarkin Hadejia Muhammadu. Kusan ana ganin su ne suka hana Sarki ya mika wuya. Dubi yadda a ko da yaushe Shamakin yake makale wa Sarki a duk lokacin da Turawan suka kirashi domin ganawa, ko da kuma Turawan suna son gana da Sarkin ne shi kadai.
Ta haka ne Turawan ba su cim ma burinsu na Hadejia ta yi saranda da kanta ba. Sarkin yaki wanda wanda ake ce ya rantse da Alqur'ani mai tsarki zai ci gaba da zama da Sarki a ko ina shi ma ya bayyana a zahiri mutum ne wanda ba ya sha'awar a yi wani sulhu da kafirai wayo Turawa.
Babu shakka zuwa wannan lokaci Turawa sun fahimci matsayi mai tsauri da manyan bayi da mabiyansu suke nuna musu a rubuce-rubucen Turawan mulkin mallaka sun bayyana yadda manyan bayi suke murkushe kokarin da suke yi na Hadejia ta miki kanta da kanta. Misali a wata takardar Telegiram da Rasdan na Kano Dr. Cargill ya aika wa babban Kwamishinan Ingila a Zungeru ya fadi cewa "Tattaunawa ra'ayi na mutanan Hadejia na wasu tsurarin mutane ne daga cikin manyan bayi" Dubi yadda shamaki ya karbawa Turawa mulki gayyatar da suka masa domin tattaunawa (amma sai kash shamakin bai nuna kulawa ta sosai a kan wannan gayyata ba).
Kamar dai yadda aka bayyana a baya. Ga alama wannan shi ne yunkurin na karshe da Turawan suka yi na neman sulhu da shamaki domin su rarraba kawunan mutanan da suke adawa da su. Idan kuwa haka al'amarin yake to lallai Turawa sun fadi warwas domin shi shamakin yana kallon wannan kira kamar goran yaki ne Turawa suka ba mutanan Hadejia.
Muhimmiyar tambaya da ta kamara a yi dangane da dagewar wannan rukuni na manyan bayi a kan kin mulkin mallaka na Turawa ita ce me ya kawo haka? Amsar wannan tambaya mai sauki ce domin a lokacin da Turawa suke karbar mulki wadannan mutane su ne na farkon da za su rasa matsayinsu da mukaminsu. Kuma sannan sun jima suna rike da wadannan mukamai, kuma suna ta gwagwarmayar su kawo wani sabon tsari a masarautar Hadejia inda za a danka wa 'ya'ya da dangin Sarki kawai mukaman sarauta su kuwa su koma a matsayin na bauta.
Idan kuma aka dada zurfafawa za a hango wani dalili da zuri'ar bayi suke sa kafa su shure ra'ayin a amince da Turawa. Su dai manyan bayi masu sarauta suna a matsayin wakilan jinsunansu ne a tsari irin na masarautar Hadejia mai kabilu iri-iri. Misali Sarkin Arewa yakan fito ne daga zuriyar mangawa, wato wasu masu sarauta sukan fito ne daga bangaran da ba ns Fulani ko Hausawa ko Kanuri ba. To manyan bayi masu sarauta suna gudun kada Turawa su zo su yamutse wannan tsari har ta kai a yi wa wasu juyin waina. Bisa dukkan alamu, kamar yadda aka sha nanatawa wannan ya kawo shamaki ya dinga bin sarki a duk inda ya sa kafa yana kaffa-kaffa da shi don kada ya yarda da Turawan Mulki.
Budu da kari a lokacin da aka yi taro na karshe a ranar Litinin 24-04-1906 inda aka yanke hukunci a yaki Turawa mulikin mallaka, wasu mutane.
Daga cikin masu ingizawa a yi yaki da Turawa sun yi yekuwa cewa 'kowa ya je gida ya shirya inyaso gobe duk mukwana lahira' ta haka manyan bayi masu sarauta suka ruruta ayi yaki da Turawa, sannan wani abin la'akari a nan shi ne dukkansu suna da hanyoyin da zasu shawo kan jama'a mai tarin yawa a kowana lokaci suke bukata domin suna da dukiya mai tarin yawa da bayi da iko.
No comments:
Post a Comment