HAIHUWA DA NASABA:-
Sabon Turakin Hadejia Mal. Dauda Yusuf da wasu ke kiransa Malam Nakakai, jikan Turakin Hadejia Abubakar ne, Dan Alh. Yusuf Na Ginsau ne, Alh. Yusuf Na Ginsau Dan Turakin Hadejia Abubakar ne, an haife shi a Unguwar Makwallar Ashshe da ke garin Hadejia ranar 15-01-1955.
KARATUN ALLO:-
Yayi karatun Allo a makarantar Malam Garba na Galadima da Malam Abba Mai Kwa a Unguwar Fagge Kano.
KARATUN BOKO:-
Ya fara karatun Firamare a Fagge ya karasa a Kofar Arewa Firamare Hadejia a 1963-1969. Mal. Dauda Yusuf bai tsaya anan ba a shekarar 1970-1974 ya halarci Babbar Sakanderan Fantai da ke Hadejia (GSS Fantai), daga nan ya zarce Makarantar sanin koyarwa ta shekara daya a Kano wato (Pivotal Teachers College Kano a 1976).
AIKIN SA NA KOYARWA:-
Mal. Ya fara aikin koyarwa a Firamaren Arbus daga nan sai Dubatu Firamare, irin gudunmawa da cigaban da ya samar a da jajircewa da ya yi a wannan Firamaren sai aka bashi Mukamin Shugaban Makaranta wato (Head Master).
KARIN KARATUNSA:-
Sa bi da hazaka irin ta sa a shekarar 1980 ya koma Babbar Kwalejin Malanta ta Zaria a karkashen Jami'ar Ahmadu Bello University (ABU Zaria). Domin karin Kartu inda ya kammala karatunsa yayi wa kasarsa shidima wato (NYSC) a Jihar Anambra a 1980-1981. Ya koma Jami'ar Ahmadu Bello domin samun Digiri a bangaran Kayarwa a karo na biyu.
AIKINSA NA KOYARWA A KARO NA II
Mal. Dauda Yusuf yayi aikin koyarwa da Makaratun da dama, ya koyar a Makarantar horon Malamai ta Malam-Madori (Teachers College). Mal. Dauda Yusuf yayi aikin a Makarantun gaba da Firamare daban-daban a tsohuwar Jihar Kano.
MUKAMAN DA YA RIKE:-
A Jihar Jigawa kuma ya rike mukamai na mataimakin Shugan Makaranta (Vice Principal) a Makarantar Sakandiren Fantai Hadejia (GSS Fantai) a 1990-1993 sannan ya rike matsayin Shugaban Makaranta wato (Principal) a wadannan Makarantu:-
1. Sakandiren Aminu Yusuf Hadejia (A.Y.I.S.S) a 1993-1994
2. Babbar Sakandiren Maza ta Malam-Madori (GSS MMR) a 1994-1997
3. Babbar Sakandiren Mata ta Birniwa (GGASS Birniwa) 1997-1999
Yayi aiki bisa gaskiya da rikon Amana ya kawo ciga marar adadi a guraren da yayi aiki wanda hakan tasa basu taba mantawa dashi.
Irin wannan kokarin nasa ne yasa Ma'aikatar Ilimi a Jihar Jigawa ta bashi Mukamin Shugaban Ilimi na yankin Kirika-Samma wato (Zonal Head).
Daga baya ta maida shi Magatakarda Ilimi na Farko wato Education Secretary) a shiyyoyi kamar haka:-
1. Jahun a 2008-2011
2. Kirika-Samma 2011-2014
KAMMALA AIKINSA NA GWAMNATI:-
Alhamdulillah Mal. Dauda Yusuf ya kammala aikinsa a watam Satumba 2014 ya ajiye aikin a bisa dalilin shekaru na haihuwa. A yayin aikin sa yayi aiki bisa gaskiya, rikon amana, hakuri, da juriya yayi zaman lafiya da al'umma inda Jama'a suka nuna masa kauna.
TURAKIN HADEJIA
Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh. (Dr) Adamu Abubakar Maje ya tabbatar masa da Sarautar Turakin Hadejia Dan Majalissa ranar Juma'a 17-07-2020
Turakin Hadejia Mal. Dauda Yusuf yana da Matar Aure Daya da 'Ya'ya Bakwa Maza Biyu Mata Biyar da Jikokai Biyar. Allah ya tayashi riko Amin.
Daga: Suleiman Ginsau, GMNIM
No comments:
Post a Comment