Monday, 11 June 2018

UNGUWAR BAYI A HADEJA

Wani Matambayi ya aiko min da tambayar yana son sanin, a ina Unguwar Bayi ta samo suna, da kuma su wanene mazauna unguwar.

Amsar wannan tambaya ita ce:

Ma’anar Bayi dai shine unguwar da take Ƙofar Baya. Anan ana nufin bayan Fadar Sarki. Ana sane da cewa ƙofofin fadar Mai Martaba Sarkin Hadeja guda biyu ne. Farko ita ce babbar ƙofar da ke gaban fadar a fuskar Yamma, ko kuma Ƙofar Fada a taƙaice. Ita wannan ƙofa, a shekarun baya kafin a rushe ta a gina ta zamani, ana kiranta Mai Tsatstsewa.

Ƙofa ta biyu ita ce wannan ƙofa ta baya, da ke fuskar Gabas, wadda aka fi sani da Kofar Ruhogo (babban rumbun aje kayan abincin Sarki).

A garuruwan Katsina da Zaria ma, haka waɗannan unguwanni suka samo suna. Saidai a Katsina ana kiran wannan unguwa ne da sunan Kofar Bai, a Zaria kuma ana kiranta da Ƙwar Bai. Karin harshe na Haɗejanci (Haɗeja dialect) yasa ake cewa Bayi anan Haɗeja. Kamar yadda wasu suke cewa Sarkin Bayi, a maimakon Sarkin Bai, duk asalin guda ne.

Abu na biyu kuma dangane da batun su wanene mazauna wannan unguwa ta Bayi? Amsar ita ce: akasarin mazauna wannan unguwa mahukuntan Gari da mashawartan Sarki ne, anan gidajen da yawa daga cikin ‘yan majalisa da hakimai suke.

Za’a iya fahimtar fa’idar hakan akan samarda wurin da zai bada damar tuntuɓa ta gaggawa tsakanin Sarki da manyan hakimansa ko ‘yan majalisa ko mashawartansa. 

Sannan kuma kasancewar gidanjen Hakimai a bayan gidan Sarki ya inganta tsaro ga Fadar domin gidajen hakiman kansu kewaye suke da na maƙarrabansu. Ta haka Fadar ta zama tana da kariya gaba da bayanta. Wannan tunani na magabata ta fuskar tsaro yayi matuƙar tasiri a wancan lokaci na yaƙe-yaƙe, kuma hakan ya bayyana ƙarara a shekarun nan da yanayin tsaro ya taɓarɓare a ƙasar nan.

Daga: Engr. Daudu Abdul'aziz

Wednesday, 6 June 2018

CIROMAN HADEJIA SAMBO

An haifishi a Ranar .../.../1909

Matsayin da yafi zama daidai da na Chiroman Hadejia Sambo a wancan lokaci shine kamar matsayin Secretary na local Government a yanzu, domin shine wanda wuk’a da nama ke hannunsa wajen gudanar da aikin N.A. (in charge of N.A. administration).

Aikinsa na farko bayan ya kamala karatu a ‘Katsina Training College’ a shekarar 1930 shine ‘Temporary Teacher’ a Kano Middle School a wannan shekarar ta 1930.

Ya rike mukamin Headmaster a Hadejia Elementary School daga 1932 zuwa 1941.

An yi masa Sarautar Dan Iya daga 1941 zuwa 1950 sannan ya zama Chiroma daga 1950 zuwa 1958 lokacin da Allah ya karbi ransa. Abin lura anan shine Chiroman ba ritaya daga aiki yayi ba, illa dai ta Allah ce ta kasance (Allah ya jikansa da rahama).

‘Member’ ne na Hadejia N.A. Council, sai kuma Member na ‘Area and Provincial Development Commission’ sannan kuma N.A. Schools Manager

A matakin kasa kuma, ya zama dan Majalisar Jihar Arewa dake Kaduna, bugu da kari kuma yayi dan Majalisar Tarayya a Ikko, sannan kuma yana cikin ‘yan majalisa masu rike da kambu biyu, abin da ake kira a wancan lokacin da suna ‘Regional Joint Council’. Bayan wannan ya zama daya daga cikin mambobi na kwamatin da ake kira ‘Regional Committee of Selection’.

Ya halarci kwas na local government tare dasu Sardauna Ahmadu Bello a kasar ingila a 1947.