Jadawalin Gwamnonin Da Suka Mulki Jihar Zuwa Yanzu
An taso daga Dungurun zuwa Kaduna a 16/11/1916.
WAIWAYE : Gwamnatin mulkin mallaka, ta taso zuwa Kaduna a ranar 16 ga watan nuwamba na shekarar 1916 , ma'aikatar Fidaburdi a ranar 26 ga watan Nuwamba suka taso. Amma ma'aikatar Safiyo da Baitulmali da sakatariya sai a karshen shekara suka iso. Wadanda suka taso daga basani su ne ma'aikatar laeiya da ta 'yan sanda.
A cikin karamin lokaci, watau wajen misalin shekaru hudu (1912-1916) an shiga manya manyan gine gine a kaduna. An yi wadannan gine ginen cikin rahusa, saboda arhar aikin lebura da Turawan suka samu. An kashe fam 116,150.00 wajen gina garin kaduna kafin a tare baki daya.
Turawan Mulkin Mallaka karkashin jagorancin Gwamna Luggar sun kafa Garin Kaduna dan ta kasance hedkwatan Nijeriya, sun gina garin bisa tsari.
Garin kaduna ya samu ci gaba da dama ta fuska daban daban tayanda a nan ne akwai cibiyoyi daban daban na ma'aikatu da dama, A nan ne akwai Hedkwatan Musulunci wato Jama'atu nasrul islam, Barikin Sojoji na NDA, Barikin sojojin Sama da na kasa da na ruwa, filin tashi da saukan jiragen sama, gidan gwamnati, Hedkwatocin ma'aikatu kamar na ilmi, lafiya, kudi da dai sauran su. Haka ma ta fannin makaranta, akwai manya manyan makarantu da dama, hakama asibitoci. Sai dai muce sam barka domin Kaduna ta amsa sunan ta Hedkwatan Nijeriya kamar yadda turawan mulkin Mallaka suka so hakan.
Tin daga Gwamna Lugga wanda shi ne gwamnan kaduna na farko, garin kaduna ta samu gwamnoni da dama, daga cikin su akwai:
JERIN SUNAYEN WASU DAGA CIKIN GWAMNONIN KADUNA
DA RADAN DA SUKA HAU DA SAUKAR SU.
1. Abba Kyari Daga 28 May 1967 zuwa Jul 1975
2. Usman Jibrin daga July 1975 zuwa 1977
3. Muktar Muhammed daga 1977 July 1978
4. Ibrahim Mahmud Alfa daga July 1978 zuwa October 1979
5. Abdulkadir Balarabe Musa daga October 1979 23 zuwa Jun 1981
6. Abba Musa Rimi daga 6 July 1981zuwa October 1983
7. Lawal Kaita daga October 1983 zuwa Decem 1983
8. Usman Mu'azu daga January 1984 zuwa. August 1985
9. Dangiwa Umar daga August 1985 zuwa June 1988
10. Abdullahi Sarki Mukhtar daga July 1988 zuwa August 1990
11. Abubakar Tanko Ayuba daga August 1990 2 zuwa Janu 1992
12. Mohammed Dabo Lere daga 2 January 1992 zuwa Novem 1993
13. Lawal Jafaru Isa daga 9 December 1993 22 zuwa Aug 1996
14. Hammed Ali daga 22 August 1996 zuwa August 1998
15. Umar Farouk Ahmed daga August 1998 zuwa 29 May 1999
16. Ahmed Makarfi daga 29 May 1999 zuwa 29 May 2007
17. Mohammed Namadi Sambo daga 29 May 2007 zuwa 19 May 2010
18. Patrick Ibrahim Yakowa daga 20 May 2010 zuwa 15 Decem 2012
19. Mukhtar Ramalan Yero daga 15 December 2012 zuwa 29 May 2015
20. Nasiru Ahmed El- Rufai daga 29 May 2015
No comments:
Post a Comment