Wednesday, 26 October 2016

TARIHIN KASAR MARADI (JAMHORIYAR NIGER)

Jihar Maradi itace cibiyar kasuwanci akasar niger, wacce Allah ya Albarkaceta, da masana, malamai, masu kudi, da ma’aikata, sannan kuma tana daya daga cikin manyan garuruwa daga cikin garuruwan kasar hausa, saboda tana daya daga cikin garuwuwa na kudancin Niger karkashin manyan garuruwan kasar hausa, kuma ta kasance karkashin mulkin Katsina shiyasa ma ake mata lakabi da Katsinan Maradi domin kuwa katsinan ta mulketa tun lokacin yake yaken kasar hausa, kuma hasalima yanzu idan za a kira sarautar maradi sai ance Sarkin Katsinan Maradi kaga kenan zamu iya cewa Maradawa Katsinawane tun asali.

Maradi tayi yake yake sosai a kasar hausa inda taci nasarar wasu garuruwa, wasu kuma suka bata kashi, amma dai tarihi ya nuna Bamarade jarumine, kuma bashi tsoro, wannan shisa ta bunkasa a kasar hausa har lukacin zuwan turawan mulkin mallaka nan kasar hausa inda suka sha
gwagwarmaya da turawa a wancan lokacin, a zamanin Sarki Katsinan Maradi Daci, tsakanin shekara ta 1892 zuwa 1894.
Bayan jihadin Sheik Usman Dan fodio mujaddadi, inda ya yaki Sarakunan Kasar hausa ya kuma jaddada addinin Musulunci a wannan nahiyar, ya kuma canza sarakuna da dama musammam wadanda
suka bujirewa ka'idodinsa Maradin ta shiga cikin jerin kasashen wannan abu ya ritsa dasu, ta kuma ta sami sarakuna har guda 23 bayan kafuwar masarautar Maradi. Wanda suka hada da:-

SARAKUNAN DA SUKAYI MULKI A KASAR MARADI

1. Sarkin katsinan Maradi Dan kasawa 1817-1830 Shekara 13
2. Sarkin katsinan Maradi Rauda 1830-1836 Shekara 6

3. Sarkin katsinan Maradi Dan Mari 1836-1843 Shekara 7

4. Sarkin katsinan Maradi Binoni 1843-1848 Shekara 5

5. Sarkin katsinan Maradi Dan Mehedi 1848-1851 Shekara 3

6. Sarkin katsinan Maradi Dan Baura 1851-1852 Shekara 1

7. Sarkin katsinan Maradi Dan Baskore 1852-1875 Shekara 22

8. Sarkin katsinan Maradi Barmo 1875-1879 Shekara 5

9. Sarkin katsinan Maradi Maza waje 1879-1882 Shekara 3

10. Sarkin katsinan Maradi Malam 1882-1883 Shekara 1

11. Sarkin katsinan Maradi Salau 1883-1887 Shekara 5

12. Sarkin katsinan Maradi Gulbi dan kaka 1887-1889 Shekara 3

13. Sarkin katsinan Maradi Dandadi 1889-1890 Shekara 1

14. Sarkin katsinan Maradi Mijin yawa 1890-1892 Shekara 2

15. Sarkin katsinan Maradi Naibo 1892-1894 Shekara 2

16. Sarkin katsinan Maradi Daci 1894-1897 Shekara 3

17. Sarkin katsinan Maradi Kure

18. Sarkin katsinan Maradi Mahamman Burja 1820

19. Sarkin katsinan Maradi Ali dan Kimale 1920

20. Sarkin katsinan Maradi Dan Kulodo 1920-1944 Shekara 24

21. Sarkin katsinan Maradi Dan Baskore 1944-1947 Shekara 3

22. Sarkin katsinan Maradi Elh Sani kure Buzu 1947-2004 Shekara 57

23. Sarkin katsinan Maradi Elh Ali Zaki 07/02/2005

No comments:

Post a Comment