Thursday, 27 October 2016

TARIHIN AL UMMAR HAUSAWA TA BANGARAN SHUGABANCI

Shugabanci na nufin rikon ragamar al’umma da ba su umarni da yi musu jagoranci bisa tafarkin da suka amince da shi, da tsara musu dokoki da sasanta tsakaninsu, da makamantan wadannan.

Shugabanci ta bangaren al’adun Hausawa kuwa, ya faro ne daga tsarin zaman iyali inda Maigida yake kamar Sarki a gidansa, a kullum shi ne babba, daga nan sai matarsa da sauran yaran gida. Yayin da aka samu gidaje biyu ko fiye da haka akan zabi wani dattijo a matsayin shugaba, ko kuma wani jarumi wanda ya nuna ya fi kowa sadaukantaka da jaruntaka da dauriya.

Wasu dalilai kamar halin kunci a cikin gida ko bukata irin ta tsaro ko rashin zaman lafiya, kan sa Maigida ya fitar da wasu daga cikin ‘ya‘yansa zuwa wani guri na daban, kamar gona ko garke.
Ta haka ne iyali kan yadu su yawaita su hada wani kauye.

Saboda haka ne sai a kara zabar wani shugaban da zai shugabanci wannan kauye. Wannan shi ya haifar da mukamin MAI UNGUWA kuma shi zai dinga tsara musu dokoki.

Kauye yakan bunkasa ya zama gari sosai, a sakamakon haka sai a kara zabar wani mutum a matsayin Maigari wato (Fagaci) don kula da wannan gari.

Da aka samu ci gaba kuma, garuruwa suka kara yawaita sai aka samar da mukamin Hakimi, ana ba wa Hakimi garuruwan Maigari akalla biyar don ya kula da su.

Da tafiya tai tafiya, sai aka samar da mukamin Sarki inda ake hada wa Sarki masarautar Hakimi akalla biyar ko fiye domin ya shugabance su ya kuma shimfida musu dokoki domin zaman lafiya.

A takaice dai ajin shugabannin da ke tsara dokoki a tsakanin talakawansu sun hada da Maiunguwa, da Fagaci, da Hakimi, da Sarki, don haka a tsarin zaman Hausawa komai dukiyar mutum in ba ya cikin wannan jeri to talaka ne.

Wednesday, 26 October 2016

TARIHIN KASAR MARADI (JAMHORIYAR NIGER)

Jihar Maradi itace cibiyar kasuwanci akasar niger, wacce Allah ya Albarkaceta, da masana, malamai, masu kudi, da ma’aikata, sannan kuma tana daya daga cikin manyan garuruwa daga cikin garuruwan kasar hausa, saboda tana daya daga cikin garuwuwa na kudancin Niger karkashin manyan garuruwan kasar hausa, kuma ta kasance karkashin mulkin Katsina shiyasa ma ake mata lakabi da Katsinan Maradi domin kuwa katsinan ta mulketa tun lokacin yake yaken kasar hausa, kuma hasalima yanzu idan za a kira sarautar maradi sai ance Sarkin Katsinan Maradi kaga kenan zamu iya cewa Maradawa Katsinawane tun asali.

Maradi tayi yake yake sosai a kasar hausa inda taci nasarar wasu garuruwa, wasu kuma suka bata kashi, amma dai tarihi ya nuna Bamarade jarumine, kuma bashi tsoro, wannan shisa ta bunkasa a kasar hausa har lukacin zuwan turawan mulkin mallaka nan kasar hausa inda suka sha
gwagwarmaya da turawa a wancan lokacin, a zamanin Sarki Katsinan Maradi Daci, tsakanin shekara ta 1892 zuwa 1894.
Bayan jihadin Sheik Usman Dan fodio mujaddadi, inda ya yaki Sarakunan Kasar hausa ya kuma jaddada addinin Musulunci a wannan nahiyar, ya kuma canza sarakuna da dama musammam wadanda
suka bujirewa ka'idodinsa Maradin ta shiga cikin jerin kasashen wannan abu ya ritsa dasu, ta kuma ta sami sarakuna har guda 23 bayan kafuwar masarautar Maradi. Wanda suka hada da:-

SARAKUNAN DA SUKAYI MULKI A KASAR MARADI

1. Sarkin katsinan Maradi Dan kasawa 1817-1830 Shekara 13
2. Sarkin katsinan Maradi Rauda 1830-1836 Shekara 6

3. Sarkin katsinan Maradi Dan Mari 1836-1843 Shekara 7

4. Sarkin katsinan Maradi Binoni 1843-1848 Shekara 5

5. Sarkin katsinan Maradi Dan Mehedi 1848-1851 Shekara 3

6. Sarkin katsinan Maradi Dan Baura 1851-1852 Shekara 1

7. Sarkin katsinan Maradi Dan Baskore 1852-1875 Shekara 22

8. Sarkin katsinan Maradi Barmo 1875-1879 Shekara 5

9. Sarkin katsinan Maradi Maza waje 1879-1882 Shekara 3

10. Sarkin katsinan Maradi Malam 1882-1883 Shekara 1

11. Sarkin katsinan Maradi Salau 1883-1887 Shekara 5

12. Sarkin katsinan Maradi Gulbi dan kaka 1887-1889 Shekara 3

13. Sarkin katsinan Maradi Dandadi 1889-1890 Shekara 1

14. Sarkin katsinan Maradi Mijin yawa 1890-1892 Shekara 2

15. Sarkin katsinan Maradi Naibo 1892-1894 Shekara 2

16. Sarkin katsinan Maradi Daci 1894-1897 Shekara 3

17. Sarkin katsinan Maradi Kure

18. Sarkin katsinan Maradi Mahamman Burja 1820

19. Sarkin katsinan Maradi Ali dan Kimale 1920

20. Sarkin katsinan Maradi Dan Kulodo 1920-1944 Shekara 24

21. Sarkin katsinan Maradi Dan Baskore 1944-1947 Shekara 3

22. Sarkin katsinan Maradi Elh Sani kure Buzu 1947-2004 Shekara 57

23. Sarkin katsinan Maradi Elh Ali Zaki 07/02/2005

HISTORY OF SALLAR GANI IN HADEJIA

Sallar Gani is an old tradition in Hadejia,
Jigawa state. It is celebrated annually
particularly during the Month of Rabiúl Auwal,
in the Islamic calendar when Muslims are
celebrating Maulud, the birth day of the Holy
Prophet Muhammad (SAW).

According to the former Galadiman Jauje of
Hadejia, Alhaji Baba Daudu, the tradition was
introduced by the Emir of Hadejia, late
Abdulkadir, 80 years ago. Galadiman Jauje
added that the late Emir introduced the
Hawan Gani and Hawan Bariki during his
reign, where festivities including a special
durbar are being carried out. Daily Trust
observed that Gani is a 3-day festivity in
Hadejia town.

On the first day, the Emir and his entourage
will leave the palace on horses in the evening
hours and go round the town. The entourage
will lead the Emir round the town through
Unguwar-Bayi to Magama-Hudu then to
Ramin-Hudi to Charbin-Barau, pass through
Majema to Bakin-Kasuwa then to Makwalla to
Kofar-Jerma and to the Hadejia Jumaat
Mosque, where the Emir makes a stop-over
and receive greetings from the horse riders.
This special greeting is traditionally called Jafi.
After greeting the Emir, the entourage will
forge ahead to the palace, while the Emir will
remain there until all horse riders have
passed. At the palace the district heads and
their associates will line up at the front of the
Emir’s palace and wait for the Emir. When the
riders have settled at the palace, the Emir will
be informed, and he will then move to his
palace to deliver his annual Gani message to
the Governor and other top Government
officials, who have been seated there waiting
for his arrival.

The entourage was arranged in such a way that the princes, district and ward heads, as well as other horse riders will be at the front followed by
the Emir, and finally the Wamban Hadejia and
District head of Balangu. This is why the
District head of Balangu is called Kurar-Baya,
which literally means the Emir’s rear body
guard.

On the second day, the Emir and his
entourage will ride their horses and head to
Bariki, popularly known as Nassarawa, where
in those days the Emir will intimate the
colonial masters about the problems and
yearnings of the people, for the latter to
address them.

However, now that, the country has secured
its independence, the Emir passes the
message to Government officials, including
the representative of the state Governor, the
Local Government Chairman and other
Government officials.

After delivering his annual speech at Bariki,
the Emir and his entourage will then return to
the palace. The Emir will enter his home, while
other horse riders will leave for their
respective homes. Thus marks the end of the
second day’s activities.
For the third and the final day, the Emir and
his entourage will leave the palace to Babban-
Daki (residence of the Emir’s mother) for the
annual greeting. This greeting is the last
segment of the Gani festival in Hadejia Local
Government.

By virtue of the activities taking place in
Hadejia town during Gani, one would believe
that to an average Hadejia indigene, the
tradition is a replica of Eid-fitr or Eid-el-Kabir
festivals. The Emir and the entire districts
heads, as well as other traditional title holders
are the participants of the special durbar.
The durbar is usually conducted in the
evening hours, where the Emir and other
traditional leaders ride their horses. The
horses are usually decorated in different ways
just to please visitors and other lookers,
during the festival.
Traditional drummers could also be seen
performing during Gani festival. While some of
these local drummers were performing
independently, others are sponsored by either
district heads or ward heads to be in their
entourage.

Because of the importance accorded to the
Gani festival by people of Hadejia, individuals
particularly children could be seen wearing
new clothes during the fiesta. Some
households also share delicious dishes with
relatives, friends, well-wishers and
neighbours, on the day of Gani festival.
Shedding light on the Gani festivity in Hadejia,
the former Galadiman Jauje of Hadejia, Alhaji
Baba Daudu said he was born in the year
when the then Emir of Hadejia, late
Abdulkadir, introduced the Hawan Gani and
Hawan Bariki.

Baba Daudu say that he has been
attending the annual Gani fiesta since the
reign of the Emir of Hadejia, late Usman. He
added that, “I have attended Gano under the
reigns of four Emirs which include late Emir
Usman, late Emir Haruna, and late Emir Maje
and now under the Emir Adamu.”

Daudu recalled that “the festivity is advancing
now. Things are changing concerning the
conduct of the annual festival. In the olden
days, the activities were not as much as they
are presently. The number of horse riders are
many now, unlike in the past where only few
horses were participating.”

Delivering his annual message to Governor
Sule Lamido, the Emir of Hadejia, Alhaji Adamu
Abubakar Maje said Gani festival is an annual
tradition which has been conducted by the
Hadejia emirate for years.
The Emir then appealed to the state
Government to provide enough drinking
water to the people of Hadejia, saying “my
people face serious difficulties before they
could get drinking water, whenever there is
power outage in the town.” Taskar Suleiman.Ginsau

“The existing generator brought to the town
by the Government is not enough. I am calling
on the authorities to look into the plight of
the Hadejia people, and provide them with a
bigger generator so that the water scheme
supplying water to them could be more
functional,” he said.
He also urged the state Government to
rehabilitate the road that links Unguwar-Bayi
to Bariki, saying “the road has a great
importance not only for horse riders during
the Gani festivity, but to other road users. The
road has remained dilapidated for some years
now.” taskar Suleiman.Ginsau

Maje commended the state Government for
facilitating the release of N10m by the Federal
Government for the completion of the Hadejia
Jama’are-River Basin Development Authority
(H-JRBA) Irrigation scheme, saying the scheme
will provide enough job opportunities to the
teaming unemployed youth in the state.

Tuesday, 18 October 2016

TARIHIN NAGERIYA A SHEKARUN BAYA!

Wani bangaren tarihi kasar da a yau tafi kowace yawan mutane a nahiyar Afirka wato Najeriya, ya nuna cewa mutanan farko da aka fara sa mu a kasar su ne kabilar Nok a wuraren Jos na Jahar Plato dake Arewa maso gabashin kasar. Shekaru 2,000 da suka wuce kabilar Nok sun yi suna wajen amfani da karafa domin kera wasu manyan kayayyakin kawa.

Garuruwan Benue da Calabar su ne asalin kabilar Bantu da sukai hijira suka bazu zuwa Afirka ta tsakiya da kasashen kudancin nahiyar shekaru aru aru da suka wuce.

A Arewacin Najeriya, Kano da Katsina sun kafu shekaru 1000 bayan fakuwar Annabi Isa (AS). Koda yake Daular Kanem Borno dake kusa da kogin Chadi ce ta mamaye Arewacin Najeriya har na tsawon shekaru dari shida 600, amma suma wadannan garuruwan sun kasance cibiyoyin kasuwanci a yankin tsakanin kabilar Bareberi na Arewacin Afirka da kuma garuruwan dake karkashin daular Kanem
Borno.

DAULAR USMANIYYA

A farkon karni na 19, Shehu Usman Dan Fodio ya ci yawancin garuruwan Arewacin Najeriya da yaki, inda suka koma karkashin daular Musulunci dake da shalkwatarta a Sokoto.

Masarautun Ife da Oyo na kabilar Yarabawa a kudu maso Yammacin Najeriya sun yi suna a shekarun 1400 wato karni na 15. Bisa ga tarihin Yarabawa, Ile Ife ita ce tushen bil adama a ra'ayinsu.
A yankin Ile- Ife ne ake sassake sassaken terra cotta wanda yai suna a kusan manyan kasashen duniya.

Shekaru da dama da suka wuce akwai lokacin da masarautar Oyo a yammacin Najeriya ta fadada har zuwa cikin kasar Togo, wanda yanuna asalin dadaddiyar mu'amala da dankwan zumunci tsakanin kasashen biyu.

Ana iya cewa masarautar Benin a kudu maso Yammacin Najeriya ita ce wadda tafi kowace girma da karfi a kasar. Tun daga karni na 15 zuwa na 19 ne masarautar Benin ta yi zamani, kuma girmanta ya kai har cikin Eko, garin da zuwan Turawan Portugal suka sauya
wa suna zuwa Legas. Ife da Benin sun yi suna ta wajen amfani da hauren giwa, katako da karafa wajen kera abubawan da suke sayarwa.

DAULAR NRI

Ta bangaren kudu maso gabashin Najeriya kuma daular Nri ta samu kafuwa tun daga kusan karni na goma har zuwa shekarar 1911, abinda yasa ta kasance daular da tafi kowace dadewa a Najeriya, kuma tana karkashin masarautar Sarki ko Eze Nri ne. Anyi ittifakin cewa garin Nri shi ne tushen al'adar kabilar Ibo.

Garuruwan Nri da Aguleri inda tarihi ya nuna nan ne asalin kabilar Ibo na cikin haular Umeuri wadanda tsatstsan sarki Eri ne.

Bayan kabilar Ibo, akwai wasu karin kabilu a yankin kudu maso Gabashin Najeriya, wadanda suka hada da Ibibiyo da sauransu.

A nan yankin ne aka samu wasu daga cikin
manyan sassake-sassake kamar Igbo-Ukwu da ke da dadadden tarihi a Afirka ta Yamma.

Gabanin shigowar Turawan mulkin mallakar Najeriya, 'yan kasar na zaman lafiya da juna tare da yin harkar kasuwanci batare da kokawar neman samun arzikin kasa ko mulki ba a dukkan sassan kasar.

Kowane bangare na amfani da tsarin mulkinsa na asali domin tafiyar da harkokin shugabantar jama'arsu. Wannan ya kawo ci gaban yankunan Najeriya.

Daga:-

Suleiman Ginsau

Thursday, 13 October 2016

WAKAR TARIHIN YAKIN HADEJIA DAGA MARIGAYI ALH. IBRAHIM KATALA!

Acikin shekara ta 1906 ne, Turawan mulkin
mallaka na kasar Ingila, tare da sojojinsu dauke da muggan, makamai suka yiwa birnin Hadejia tsinke. Inda hakan tayi sanadiyyar gwabza wani mummunan yaki/fada tsakanin Turawan mulkin mallaka da kuma Jaruman kasar Hadejia masu gwagwarmayar kwatar yancin kai. Hakan yayi sanadiyyar mutuwar KYAFTIN H.C.E PHILLIPS (MAI TUMBI), inda aka kissima cewa, dubban mutane ne suka rasa rayukansu a sanadiyar hakan. Babban abin lura shine, dukkan wadannan dubban bayin Allah da suka rasa rayukansu, sun rasa ne a rana guda, cikinsu kuwa harda Sarkin na Hadeja a wannan zamani, Wato Sarkin Hadejia Muhammadu. Taskar Suleiman Ginsau

Wannan waka ta tattare dukkan abinda ya faru a ranar, ta kuma yi cikkakken bayani gameda yadda Shahidan Hadeja suka jajircewa abinda suka kira, bautar dasu acikin kasarsu. Koba komai, wannan ya nuna yadda yan Afrika suka dauki yancinsu da muhimmanci.
Da fatan Allah ya jikansu, nakecewa ga abinda ya samu:-

WAKAR TARIHIN YAKIN HADEJIA DAGA MARIGAYI ALH. IBRAHIM KATALA!

1, Allahu sarki shi kadai yake wahidun sammai da kassai jalla bashi da kishiya.

2, Shi ba fari shi ba baki ba ubangiji ba ja ba ba alkashi bashi ga rawaya.

3, Ba sake sake ba ba kamar yarani ba shudi da kore jalla bashi da mai kama.

4, Zatinsa baya tattara bai rarraba da kawai da motsi bayayi ko sau daya.

5, Sarkinda ba na biyunsa ba na uku nasa ka dadan basira zanyi waken shahidu.

6, Ranar talata munga tashin duniya Rannan Muhammadu yai shahada zahira.

7, Shi yai jawabi ya fada shi bai gudu kuma bashi mai kamu a darul duniya.

8, Raggo ake kora a bishi a cim masa amma sadauki bai gudu sai faduwa.

9, Sarki Muhammadu yai jawabi ya cika shi bashi mai kamu a jashi ya tunkiya.

10, Dan melle sarkin yaki shima ya fada in dai da rai sarkinmu baya kamuwa.

11, Ma'ajin Hadejia saleh shima ya fada mun dau shahada zahira bahakikiya.

12, Manya da yara duk shirin yaki suke kowa yana wanka yana yin alwalah.

13, Kowa yana yin sallama a gida nasa sunsa gabansu a lahira ba dawaya.

14, Jama'ar Hadejiawa fa duk sun hallara kowa yana cewa fa mun zama shahidai.

15, Sarki Muhammadu mai shahadar zahiri ba badili ko dai cikin tawaga tasa.

16, Shi bai kamar tsoro ba baya razana kan ya ije ma babu sauran hanzari.

17, Ajali idan yayi babu kwana duniya kai dai zamo kullum shiri duka safiya.

18, Shi bai kamar tsoro a baya razana baya gudu dan Garba sarkin jarumai.

19, Mutuwa tafarki wanda kowa zayabi ai kulli nafsin dukka rai zai dandana.

20, Aka daura sirdi nai ya hau bisa ya tsaya yace mu dau himmar shahada zahira.

21, Sarki Muhammadu baya tsoro ko kadan Allah ma'aiki su take tsoro kadai.

22, Hauninsa linzamin mayani ya rike damansa tasbihi salatin annabi.

23, Dan mai karatu tudun kasa ba dawaya dan garba jikan sambo sarkin adalai.

24, Duk mai shahada auwalinsa madacima suka barace da fari ya mutu shahidi.

25, Farkon hawa yaki galadima sai haru ranar talata sun ka sauka a barzahu.

26, Alkali sarkin yaki kaura amada sarkin arewa da sunkaje can sun tsaya.

27, Suka jeru sunka tsaya a nan kofar gabas kafin suje har mai ruwa ya taddasu.

28, Kasan igwa dokinmu shi bai santa ba duka dokuna na faduwa ba lissafa.

29, Igwa tana tashi madafa na zuba yau sai ta Allah babu sauran shawara.

30, Jaruman Muhammadu basu tsoro ko kadan sun gwammace mutuwa da dai subi kafiri.

31, kuma sabo jikan tete harbi nai ake anan a kofar fada duk suka tuntsure.

32, Firyan Hadejia shi da bori na salihu kofar gabas suka fadi nan aka cim musu.

33, Dodo na zela da shi da gwanki barin nufe sun karbi hartashi a kwaryar kai nasu.

34, Ai babu mai mutuwa gaban ajali nasa kan surfa gero kan daka wasu sun fice.

35, iko idan Allahu yayi nufi nasa ai ba tsimi balle dabara ko daya.

36, Tamkar kamar inuwarka baka guje mata in kai gudun ta bika harma ka tsaya.

37, Hartashi na yawo kamar burduduwa tamkar zubar wake a can a masussuka.

38, Ya ratsa soraye ya ratsa katanguna tamkar kabewa ko kamar tumfafiya.

39, Yasha zarar soro ya keta katanguna da kago da zaure sun zube ba tambata.

40, Tsarnu da kurna har kasa durumi dada ya kar dabinai cediya da itatuwa.

41, Rannan Hadejia munga tashin hankali Allah da manzo su kadai ne magani.

42, Abdulwahabu baka tana hannu nasa artashi ya samar ya tsinke tsirkiya. 

Allah yaji kansu ya musu gafara, Allah ya yafemusu duk kan kura-kuransu baki daya. Amin...
MAWALLAFIN WAKAR:- MARIGAYI ALHAJI IBRAHIM KATALA. Allah yaji kansa da Rahma. Amin Idan tamu tazo Allah yasa mucika da Imani...

Wednesday, 12 October 2016

TAKARDAR NADIN SARKIN HADEJIA HARUNA, DAN SARKI MUHAMMADU, DAN BUHARI 1906-1909. WANDA TURAWA SUKA NADASHI. BAYAN KAMMALA YAKIN HADEJIA DA TURAWA.

                                                            24-10-1907

C. Temple, ESQ, Razdant Sokoto Province
Sokoto.

Kamar yadda na rubuto maka a TELEGIRAM dina mai Lamba 2035 da kuma amsar da kabani wacce ke dauke da zancen Takardar Nadin Sarkin Hadejia, ina mai rubuta maka fassarar wannan Takarda izuwa Harshen Turanci.

Sabon Sarkin shine da aka Nada shine Haruna dan Sarki Muhammadu dan Sarki Buhari. Shi Sarki Muhammadu shine wanda yaki yarda damu, kuma ya yaki Sojojin Sarkin Ingila.

Shine kuma wanda aka kashe lokacin ana yakin. Ya yinda za'a mikawa wannan sabon Sarki Takardar Nadin sa CAPT. HCB PHILISPS yayi masa bayanin dokokinmu dalla-dalla wanda ke kunshe a cikin ta a baiyane da manya-manya Hakiman sa da Bayinsa da Barorinsa da sauran ja'ar gari.
                                               Acting Secretary.
The Scretary
Zungeru 24th Oct. 1907.

Friday, 7 October 2016

NAZARI AKAN TARIHI DA RAYUWAR GALADIMAN HADEJIA ALH. USMAN ABDUL'AZIZ.

(TARE DA SULEIMAN GINSAU)

"SALSALAR HAIHUWA DA KARATUN  GALADIMA"

Kamar yadda yake a bayyane an haifi Mai Girma Galadiman Hadejia Alh. Usman Abdul'aziz a garin Hadejia da ke Jihar Jigawa a ranar 23 ga watan Oktoba a shekara ta 1959, wanda yayi dai-dai da 20 ga watan Rabi'ul Sani na shakarar ta 1379.
Idan muka dubi rayuwar Galadima a bangaran karatunsa ya halarci Makarantar Hudu Islamiyya dake garin Hadejia a shekarar 1963, ya halarci Makarantar Firamare ta Hadejia Central a shekarar 1965-1971, inda daga nan kuma ya wuce zuwa  Kwalejin Geamnati dake Kano wadda a yanzu ta koma Rumfa Kwalej a shekarun 1972-1976,  a matakin sakandare daga nan kuma ya wuce Makarantar koyan sana'a dake Kaduna (Kaduna Polytechnic)  anan ne ya yi karatunsa na Karamar Diploma ckin shekarun 1976-1979. Yayi Babbar Diploma akan kasuwanci a (Kaduna Polytechnic) cikin shekarun 1979-1981. Yaci gaba da karatunsa a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi a Shekarun 1997-1998 ya sami shaidar Babbar Diploma ta gaba da Digiri a kan kasuwanci, daga nan ya wuce kasar waje domin karo Ilmi inda ya shiga Jami'ar St. Clements da ke kasar Australia a shekarun 1998-1999 a inda ya samu shaidar Digiri na biyu a bangaran Kasuwanci, daga nan ya sake komawa Jami'ar Tafawa Balewa dake Baushi domin cigaba da karatunsa a inda ya sake samun shaidar wani Digirinsa na biyu a kan kasuwanci na komai da ruwanka wato ( General) a shekara ta 2000-2001. Mai Girma Galadima Usman Abdul'aziz ya yiwa kasa hidima a Jihar Binuwai daga shekara ta 1981zuwa1982

"RAYUWARSA TA AIKI"

Bangaran Rayuwarsa ta aiki kuwa abin abin sha'awa da ban mamaki Mai Girma Galadiman Hadejia Alh. Usman Abdu'aziz ya fara aiki ne a ma'aikatar Ciniki da masana'antu ta tsohuwar Jihar Kano a shekara ta 1982, a matsayin jami'i mai kula da bangaren ciniki.

"AIKIN GALADIMA A KAMFANIN TOTAL"

Daga nan ya kama aiki da Kamfanin Mai na Total a matsayin wakili mai kula da harkokin kasuwanci a watan Augusta na shekarar 1983, bayan samun horo da yayi a Hedikwatar Kamfanin da ke birnin Lagos,  daga nan an yi masa canjin aiki zuwa Jihar Kano a matsayin jami'i mai kula da harkokin kasuwanci.
Bayan dawowarsa Kano ansake yi masa canjin aiki zuwa Jihar Barno a shekarata 1988 a matsayin wakilin harkokin kasuwanci mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas na Kamfanin Mai na Total. Kasancewarsa a wannan shiyya ya bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban wannan Kamfani, hakan ne ya sanya aka sake yi masa canjin aiki zuwa sabon ofishin da aka bude na Kamfanin a Jos, hedkwatar Jihar Filato a matsayin Manaja mai kula sha'anin kasuwanci, zamansa a Jos ya gudanar da ayyukan da suka kai Kamfanin ga samun nasara, a inda aka daga darajarsa a wannan shiyya, hakan ta sa aka kara ciyad dashi gaba aka bashi Manajan kula da kasuwanci a shiyyar Arewa maso Gabas, a shekara ta 1996. A lokacin da yake gudanar da ayyukansa a wannan shiyya a Jos bayan ci gaban da na bayyana mai dorewa ya samar ta fuskar habaka kasuwancin Kamfanin. Lallai Galadima ya tabbatar wa  Duniya cewa shi tsayayye ne wanda yasan harkokin kasuwanci bisa gaskiya da rikon amana.
Har ila yau kwarewarsa ce ta sa aka sake karama masa mukami zuwa Manajan yanki wanda ya kunshi Jahohi kamar su:-
1. Bauchi
2. Gombe
3. Barno
4. Yobe
5. Adamawa
6. Taraba
7. Filato
8. Nasarawa
9. Binuwai
10. Kogi
shedikwatar tana nan a matsayinta a Jos
A shekara ta 2001 lokacin da Kamfanin Mai na Total da na ELF suka hade an sami canje-canje inda aka kirkiro sabon Ofis mai kula da Arewa mai nisa dake da shedikwata a Kano, tare da nada Galadima a matsayin Manajan shiyya mai kula da Jihohin da suka yi iyaka da kasashen Republic of Benin, Niger, Chad da Cameroon kamar haka:-
1. Kebbi
2. Sakkwato
3. Zamfara
4. Katsina
5. Kano
6. Jigawa
7. Yobe
8. Barno
9. Adamawa
A shekarar 2006 an kuma yi masa canjin aiki zuwa birnin Benin a matsayin Manaja mai kula da shiyyar yamma ta tsskiya. Kamfanin Total ya kirkiro Ofishin kasuwancin Najeriya a Abuja wanda aka bawa Galadima Manajan wannan Ofis mai kula da shi a shekara ta 2008.

"AIKIN GALADIMA A KAMFANIN MAI  NA NNPC"

Dangane da irin gagarumar gudun mawa da jajircewar sane tasa, daga bisani aka yi masa canjin aiki zuwa Kamfanin NNPC a shekara ta 2012 lokacin da Kamfanin na NNPC ya nemi Kamfanin Total da ya basu shi don ya taimaka wajen canja akalar tafiyadda kamfanin NNPC Retail yadda zai yi daidai da sauran manyan kamfanonin mai na kasuwanci irin su TOTAL.
A yayin zamansa a Kamfanin NNPC na kasa ya samar da ci gaba ta fuskar samar da kudaden shiga masu tarin yawa, ya samu nasarar bude kananan gidajen Mai shiryawa tare tabbatar da tsaftace kasafin kudaden Kamfanin, Galadima ya samar da ci gaban Kamfanin NNPC Retail tare da inganta harkokin kasuwanci a matsayin Janar Manaja mai kula da saye da kasuwanci a karkashin NNPC Retail Ltd, a Abuja cikin watan Maris na 2012.
Haka kuma Kamfanin NNPC ya sake ba shi mukami Janar Manaja mai kula da tsare-tsare da dabarun aiki cikin watan Maris na 2013 a dai karkashin NNPC Retail Ltd.

"A JIYE AIKIN GALADIMA"

Alhamdulillah mai Girma Galadima ya yi aikinsa cikin koshin lafiya tare rikon amana da gaskiya wanda hakan ya bashi damar ajiye aikinsa cikin walwala da jindadin, Galadima ya ajiye aiki don kashin kansa a shekara ta 2014, inda ya kafa Kamfaninsa mai suna ENCEE BUSINESS SERVICES, wanda yake gudanar da shawarwari da horo kan yadda za'a bunkasa harkokin kasuwanci Mai da Iskar Gas...
Galadima yana da matan Aure guda biyu da 'ya'ya Goma...

Wanda yayi nazari
SULEIMAN GINSAU

Association Of Nigerian Authors (ANA)

Wednesday, 5 October 2016

KASAR HADEJIA DA KABILUN CIKINTA

KASAR HADEJIA DA KABILUN CIKINTA

Kasar Hadejia tana da kabilu da dama wadanda kuma suke a barbaje a ko ina cikin kasar sannan suna da yarensu daban-daban irinsu:-
1. HAUSAWA
2. ABORAWA (FULANI)
3. MANGAWA
4. GIZMAWA
5. BADAWA
6. KOYAMAWA
7. TIJJANAWA

1. HAUSAWA:- Kabilar Hausawa sune kabila mafiya yawa a kasar Hadejia Domin su babu wanda zaice ga lokacinda suka shigo Kasar Hadejia. kuma tafi karfi a kasar sakamakon dadewar Garuruwansu. kamar Garun Gabas (Biram), Auyo, da Matsa, ko zuwan Bayajidda Garun Gabas yazo ne ya samu Mutanen Garin suna yin Hausanci. "Duk da wasu masana tarihi suna ganin cewa Tarihin Bayajidda ba gaskiya ba ne kawai tatsuniya ne"

2. ABORAWA (Fulani):- Kabilar fulani sun shigo kasar Hadejia tun a Farkon karni na goma sha biyar (15) kuma sun shigo ne daga yankin Machina wasu kuma daga Katsina, kuma sun Taho ne daga Gabar Kogin SENEGAMBIA wato SENEGAL. sun fara zama ne a Rinde wasu kuma sun Zauna a Jarmari wasu a Marke wasu a Adiyani da Margadu. Kuma ayarinsu ya kasu kashi  biyu Inda wasu suka wuce kasar Kano Karkashin Jagorancin Lamido Usman Kalinwama. A Karni na goma sha Tara (19) Wasu fulanin sun sake shigo Kasar Hadejia daga yankin Machina Karkashin Jagorancin Ardo Abdure Dan Jamdoyi. Kuma ance Kafin suzo Hadejia saida suka zauna a Kankiya ta Jihar Katsina. kuma wadannan fulani suke Sarautar Hadejia har zuwa Yau.

3. MANGAWA:- Kabilar Mangawa ko Barebari wadanda mafi yawancinsu suna zaune a Gabas da Hadejia da kuma Arewacin kasar Sun zo ne A karni na goma sha bakwai (17) sun taho ne daga yankin Borno kuma mafiya yawansu sun zo kasar Hadejia ne Tonon Azurfa da Tagullah. Inda kuma daga baya wasu sun shigo kasar Hadejia a lokacin da RaBe yaci Kukawa da Yaki sai suka kaura suka dawo kasar Hadejia, Kamar Birniwa, Baramusa, Kacallari, Dilmari, Musari, Kirikasamma, Kukadabo, da Sauransu.

4. GIZMAWA:- Gizmawa suma kamar Mangawa sun shigo ne a Karni na goma sha bakwai (17) kuma suma suna zauna ne a yankin Guri, Marma, Lafiya da sauransu kuma suma yarensu kusan kamar barbarci ne sai dai wasu kalmomin da yake canzawa.

5. BADAWA:- Kabilar Badawa basu da yawa a kasar Hadejia, kuma suna zaune ne a Garuruwan Iyakar Hadejia da Bedde, Kamar Gayin, Adiyani, Margadu, da Kadira. wasu sun zauna anan ne tun kafin yakin Gogaram. wasu kuma sunce dama anan suke tuntuni. ganin cewa suna iyaka ne da Kasar Bedde.

6. KOYAMAWA:- Kabilar koyamawa suma basu da yawa kuma dangin Barebari ne, sai dai zanensu ya bambanta. kuma yarensu ma ba iri daya bane. Kuma suna cewa sun taho ne daga Gabas da Sudan. sannan suna zaune ne a Kasar Kafin Hausa, Bulangu, Yayari, koyamari da sauran garuruwan kasar Kafin hausa.

7. TIJJANAI:- Kabilar Tijjanai fulani ne dake zaune a Yelleman kuma Malamai ne masu bin Darikar Tijjaniyya. shi yasa ake ce musu Tijjanai. Sun shigo kasar Hadejia a shekarar 1903 daga Malo a yankin Tukolar Senegal. sun taho ne bayan Turawan Faransa sun yiwa Yankinsu Mulkin Mallaka. sun taho karkashin jagorancin Shugabansu Muhammadu El-Bashir, kuma sun fara zama ne a Lokoja. Magajinsa kuma Ahmadu Madaniyyo sai ya sake tasowa daga Lokoja yazo Kasar Hadejia aka basu Guri suka zauna. wato Yelleman Tijjanai. Alhamdu lillahi.

Ismaila A Sabo

Monday, 3 October 2016

TSARIN ZAMAN JAMA'A DA TATTALIN ARZIKI A KASAR HADEJIYA KAFIN ZUWAN TURAWAN MULKIN MALLAKA.

TSARIN ZAMAN JAMA'A DA TATTALIN ARZIKI A KASAR HADEJIYA KAFIN ZUWAN TURAWAN MULKIN MALLAKA.

Hadejiya tana da kabilu daban-daban, amma duk da haka, masarautar a cure take a waje daya. Addinin Musulunci shi ne ya dada hada su da kuma harshen Hausa wanda suke magana da shi a matsayin harshen kasa. Babu ta baba cewa Addinin Musulunci shi ne Addinin da mafi yawan jama'a suke bi a wannan masarautar ta Hadejiya. Ka'idoji da dokoki da hukunce-hukunce Musulunci su ne suke tafiyar da rayuwa da ayyukan mutanen wannan kasa. Addinin Musulunci ya hada kan jama'a kuma ya samar da hanya madaidaiciya ta zaman al-umma. Ta haka ne Musulmi masu rinjaye da wadanda ba Musulmi ba marasa rinjaye mazauna kasar Hadejiya kafin mulkin mallaka suna ganin sarkin Hadejiya nada mutukar kima kuma shugaba ne babba duk da yake suna da hakimai da dagatai masu jagorancinsu. Mutanen Hadejiya sukan hadu a kowace shekara su gudanar da bukukuwan Sallah karama da Sallah babba a Hadejiya. Ta haka al'ummar Hadejiya take cudanya da juna cikin walwala, farin cikin, nishadi, jindadi da annashuwa da sakin fuska. Kuma bisa dukkan alamu, kabilun da suke zauna a Hadejiya sun shiga juna, za a taras bisa asali, Bahaushe, Bababbare ne, ko Bamange, ko babade, ko kuma bafulatani. Haka dai kabilun Hadejiya suka sarki juna.
Jama'ar da ba Musulmi ba suna karkashin kariya ta wannan masarauta, amma su kuma suna bayar da jizya. Al'adun Hausawa/Fulani Hadejiya suna da babban tasiri na mutanen Gabas wato al'adun Barebari. Akwai misali da yawa da za a iya bayarwa a kan haka, kauki misalin sunayen wasu mukaman sarautu kamar Zangoma da Bulama da Kacallah da Maina (dan Sarki) duka daga wajen Barebari a ka samo su. Hatta ma bikin Sallar maulidi ana gudanar da shi ne dai-dai yadda Barebari suke yi. Ashe ke nan al'adun Barebari sun yi tasiri. (Sulaiman Ginsau )
Kari a kan wadanan kyawawan huldodi na mutanen Hadejiya a tsakanin junansu, tsarin da masarautar ta bi wajen tafiyar da al'amuranta na mulki ya dada kara wannan dankon zuminci. Tun daga farkon kafuwar daular, Sarkin Hadejiya Malam Sambo ya dora kowace kabila daga cikin kabilun kasar a kan wani mukami na sarauta. Wannan tsari da aka ci gaba da aiwatar da shi, ya sanya jama'ar kasar sun zauna a dunkule tamkar tsintsiya domin kowace kabila ta san tana da wakilci a majalissar wannan masarauta.
Ta fuskar tattalin arzikin kasa kuwa, Hadejiya tana da yalwataccen arziki tare da sana'o'i da masana'antu iri-iri, duk da yake harkokin noma sunfi daukar kaso mai yawa. Magidanci shi ne tushen arziki a tsarin zaman jama'a tare da iyalansa a matysayin masu taimakawa. Talakawa sun tsayu sosai wajen yin noma na lokacin damina da noman fadamu a lokacin rani, sannan kuma kamun kifi da kiwo sun zama ruwan dare a tsakanin mazauna kasar Hadejiya. Amfanin gonar da aka fi nomawa sun hada da:-
1. Gero
2. Dawa
3. Shinkafa
4. Wake
5. Masara
6. Gyada
7. Auduga
8. Alkama
9. Ridi da Kankana
10. Rake da sauran kayan lambu kamarsu Timatir da Tatttasai da Taruhu da Rake da sauran kayan lanbu ana noma su ne ta hanyar noman fadama a lokacin rani. Kasar Hadejiya, kamar sauran kasashen wannan nahiya, tana da kyakkyawar kasar noma Gero da Kiwon Dabbobi. Har wa yau kuma wannan yanayin wuri ne mai albarka ya ba da damar aiwatar da wasu sana'o'I kamar su Rini da Saka da Kira da Ginin Tukwane da Jima da Dukanci da Gini da sauransu. (Sulaiman Ginsau)
A bangaren saka kuwa kauyen Bangelu wanda yake tsakanin Auyo da Hadejiya ya shahara sosai wajen saka da dinka Rigar Bullamai tare da sauran Rigunan Saki Fari masu inganci. Haka kuma kauyen Hadejia ya yayi suna a sana'ar Rini. Mutanen Hadejiya da suke zaune a daura da kogin Hadejiya sunyi fice a sana'ar Su ta kamun kifi. Haka kuma dajin Hadejiya cike yake da kudan zuma inda ake samun zuma mai tarin yawa. Diban zuma ya zama wata sana'a mai riba ga jama'ar kasar Hadejiya musamman yadda take tallafawa wajen warware matsalolin rayuwar yau da kullum.
Bugu da kari mutanen Hadejiya kamar sauran wurare, sukan sayar da amfanin gona wanda ya yi rara, ta haka suka shiga hada-hadar kasuwancin amfanin gona daga cikin hanyoyin da suka kara habaka Tattalin Arzikin Kasar Hadejiya kafin zuwan turawan mulkin mallaka. Ta wannan hanya masarautar Hadejiya ta zama wata cibiya kuma muhimmiyar mahada ta cinikin kayan amfanin yau da kullum a gabacin kasar Hausa a karni na sha tara (K19). Masarautar ta yi fice wajen fitar da kayayyakin abinci kamar Alkama da Kifi zuwa Kano da wasu wurare, ita kuma sai ta sayo Goro da makamancin abubuwan da masarautar take da bukata. Kamar yadda aka fada a baya, mutanen Hadejiya na kasuwancin Rigunan Saki ko Rigunan Fari da Zuma da Kiraga wato (Fatu) da Shanu, su kuma su sayo Gishiri da Dawakai da Kanwa. Ana kuma jin cewa Hadejiya ta zama wata hanya ta fatauci na fataken da suke ratso Sahara zuwa Kano ta yamma da kuma Barebari da Larabawan Fezzan da Azbinawa da Buzaye daga gabas da kuma yamma. Wadannan fataken sukan hadu a kasuwar Hadejiya su gudanar da harkokin cinikayyarsu na kayayyaki kamar Rigunan kano da kanwa da Shanu da Bayi da kayan Yaji (Sulaiman Ginsau).
A wannan lokacin da ake Magana, a Hadejiya akwai manyan kasuwanni guda biyu (2) daya kasuwar an yi ta a wajen ganuwa, an kakkafa rumfunan da kuma masaukai na baki wadanda aka yi don samar da wuraran zama da jin dadin fatake da sauran yan kasuwa. A cikin ganuwa ta birnin Hadejiya akwai wata kasuwa wadda take kula da bukatun mazauna birnin Hadejiya da makwabtanta. Wannan ya nuna cewa bayan kasancewar Hadejiya cibiyar mulkin da ayyukan jin dadi jama'a, haka kuma tana matsayin ingantacciyar cibiya ta kasuwanci. Wannan kasuwa tana karkashin kulawar Zangoma wato Sarkin kasuwa. Zangoma shi ne yake karbar dukkan haraji na wannan kasuwa tare da masu taimka masa.
A dunkule, wannan yayi bayanin Hadejiya a matsayin masarauta ta mulkin jihadi da kuma fito da tsarin zaman jama'arta da tattalin arzikinta kafin mulkin mallaka na turawan ingilashi a kan daular Usmaniyya ta Sakkwato. An kuma nuna cewa a fanning Siya sa, Hadejiya gari ne na 'yan Boko da 'yan siya sa masu yawan gaske kuma Hadejiya garine na kasuwanci wadda hakan ya sa mutane suna zuwa siyan kayayyaki daga gurare daban-daban, sannan masarautace mai karfi a tsakanin masarautun da suke gabacin kasar Hausa, musamman yadda take tsoma baki a harkokin cikin gida na makwabtan ta.
Haka kuma nayi wai-waye ta fuskar tsaro ya bayyana cewa Hadejiya kasace jaruma kuma karshen karni na sha tara (K19) sai ta zama kasa mai kyakkawar huldar dangantaka da zama na lumana da abokan taka da sauran masarautu. (Sulaiman Ginsau)