Tsarin tsaro na masarautar Hadejiya, sarki wato AMIR shi ne shugaban mayaka, sai dai ya kan nada wasu sarakunan yaki wadan da suke shigewa gaba a madadinsa da suka hada da:-
1. Sarkin Yaki
2. Jarma
3. Madaki
4. Sarkin Arewa da sauran mayan mayaka ko sakarunan yaki. Rundunar sarki ta kan kunshi fadawa da masu sarauta da bayi da dogarai da sauran jama'ar gari. Masarautar Hadejiya tana da manyan rukunonin yaki guda biyu (2) wato mayaha doki da 'yan kasa wato (dakaru), Hakika, Hadejiya ta shara ainun ta fuskar yake-yake a na ganin ita ce masarauta mafi karfi a sashen gabas da Kano.
Hadejiya tayi wannan suna ne da jimawa, an san cewa ba kanwar lasa bace a fagen yake-yake. Shaharar ta kara fitowa sarari ne a lokacin Sarki Buhari har zuwa baiyanar Turawa a lokacin sarkin Muhammadu mai Shahada a 1885-1906.
Kamar yadda yake a tsarin masarutar masu jihadi, hakimi da manyan jakadu da dagatai suna tafiyar da hukunce-hukuncen shari'a a garuruwansu na mulki. A masarautar Hadejiya akwai wuraren hukunci wato Kotuna guda biyu 1. Kotun Sarki ita ce babbar kotu, kuma ita ce wadda ake daukaka kara zuwa gare ta, sannan akwai 2. Kotun Alkali duk wadannan kotuna suna babban birnin masarautar ne. Kotun Alkali ita ce take kula da shari'u na ma'amala da hudud, amma shari'u kan rikicin kasa ko rikicin iyakoki da haddi wanda ya shafi hukuncin kisa a kotun Sarki ake gudanar da su. Akwai babban gidan Yari a birnin Hadejiya wanda ake amfani da shi a masarautar baki daya.
Dogarai kuwa suna yin ayyuka irin na 'yan sanda suna zama masu kare Sarki da rakiyar masu sarauta idan tafiya ta kama su, har wa yau kuma suna zama jakadu wato masinjoji. Idan aka dubi dangantakar Hadejiya da sauran wurare, kamar huldar Hadejiya da sakkwato, za'aga dangantaka ce ta tsakanin bara da ubangidansa ta hanyar kai gaisuwa da halartar tarukan manyan sarakuna na shekara-shekara da aikawa da mayaka domin taimakawa jahadi.
(A irin wanna taimakon ne masarautar Hadejiya ta tura mayaka inda suka hadu da mayankan Katagun da Misau, sukaje suka yaki Yamusa na Dutse, mai goyon bayan Mahdi. Haka kuma mayakan Hadejiya da Katagum da Gombe da Bauchi da Jama'are da Misau suka yaki Jibril saboda shima yana goyon bayan Mahdi.) Suleiman Ginsau Ruwan Atafi
Ita kuma sakkwato ita ce take tabbatar da zaben sabon sarki a kowa ne lokaci da ake da bukatar yin haka, kuma ita ce mai yin sulhu ko shiga tsakani idan aka sami sabani tsakanin marautar a cikin gida ko a waje. A dunkule, a lokacin da masarautar Hadejiya take kula da al'amuranta na cikin gida, shi ne kuwa Amir al-muminin (Sarkin Musulmi) shi ne mai kulawa da tabbatar da an bi shari'a sau da kafa domin ita ce tushen daular Jahadi ta Sakkwato.
Masarautun da suke gabas Sakkwato Waziri ne idon Sarki Musulmi a harkokinsu, shi ne wakilinsa. Babu shakka dangantakar tsakanin Sakkwato da Hadejiya dangatakace mai danko sosai in ban da lokacin da Sarki Buhari ya yi tawaye.
(A salin tawayen Sarki Buhari rigima ce ta sarauta tsakaninsa da dan uwansa Ahmadu. Ana jin Ahmadu ne masu zaben sabon Sarki suka zaba, amma Buhari ya kwace wannan dama tare da taimakon manyan bayi. Da daular Sakkwato ta sa baki a matsayin Sarkin Musulmi, sai yaki ya barke inda Sarki Buhari ya sami galaba ainun akan rundunar daular Sakkwato wadda ta kunshi mayaka daga Sakkwato da Katagum da Bauchi da Kano da Misau. Amma duk Sarki Buhari yagama dasu, ana yiwa wannan yaki da lakabi da yakin GAMON GAFFUR. Wato a Kaffur aka yi yakin. Daga wannan lokacin ne Sarki Buhari ya bujirewa ikon Sakkwato kuma ya dinga kai wa makwabtanta hari). Suleiman Ginsau Ruwan Atafi
Kuma Da rundunarsa taci galaba a kan rundunar mayakan daular Jahadin Sakkwato, sai ya ture ikon daular na wani lokaci. Dangantakar lumana da kyakkyawar hulda da zaman lafiya su ne kashin bayan dangantakar Hadejiya da sauran masarautu gabanin mulkin mallaka. (Suleiman Ginsau, Ruwan Atafi. 2015)
No comments:
Post a Comment