An haifi Maigirma Sardaunan Hadejia, Ambassador Haruna Ginsau, mni, a garin Hadejia a ranar Laraba, 30 ga watan Satunba, 1959. Mahaifin sa shine Marigayi Dan Amar Hadejia, Hakimin Kafin Hausa, Malam Usman Ginsau, dan Chiroman Hadejia Malam Aliyu, dan Sarkin Hadejia Malam Haruna Maikaramba, dan Sarkin Hadejia Malam Muhammadu Maishahada, dan Sarkin Hadejia Malam Haru Babba, dan Sarkin Hadejia Sambo, dan Ardo Abdure.
Mahaifiyar sa Hajiya Barira, 'ya ce ga Wamban Hadejia Malam Sulaiman, dan Shamaki Muhammadu.
Maigirma Sardauna ya yi karatun allo kafin ya shiga, da kuma yayin da yake karatun Firamare. Ya kammala karatunsa na Firamare a makarantar Garko dake garin Hadejia a December, 1972. Daga nan kuma ya samu shiga Makarantar Gwamnatin Tarayya da ke garin Jos in da ya kammala karatunsa na sakandare a 1977. Daga nan kuma sai ya samu shiga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya inda ya samu digiri na farko a fannin Kimiyyar Siyasa a shekarar 1981.
Maigirma Sardauna ya yi aikin bautar kasa a garin Azare, jihar Bauchi, inda ya koyar a Comprehensive Day Secondary School, Azare. Bayan wannan ne kuma ya samu nasarar samun aiki a Ma'aikatar Harkokin Waje ta Najeriya a ranar 10 ga watan Oktoba a shekarar 1982. Ya yi aiki a sassa daban-daban a hedikwatar Ma'aikatar Harkokin waje (MFA) da kuma Ofisoshin Jakadancin Najeriya a kasashen waje wadda suka hada da Senegal, Britaniya, Andalus (Spain), Sudan da Jaza'ir (Algeria). Ya rike matsayin Mukaddashin Jakadan Najeriya a Spain da Fadar Paparoma, da kuma Sudan. Haka kuma ya rike mukamin Wakili na dindindin a Hukumar Yawon Shakatawa ta Majalisar Dinkin Duniya mai shalkwata a birnin Madrid.
A watan Yuli 2012 kuma Shugaba Goodluck Ebele Jonathan, GCFR ya nada shi a matsayin Jakada na Musamman kuma Mai Cikakken iko na Tarayyar Najeriya a kasar Algeria da yankin Saharawi Arab Democratic Republic (a lokaci guda), kuma ya kammala wannan aiki a watan Fabrairu, 2016.
Maigirma Sardauna ya kuma yi ayyuka a wajen Ma'aikatar Harkokin Waje. Daga 1997 zuwa 1999, ya zama Mamba, Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa a matsayin Kwamishinan Kasa da raya Birane. Bayan kammala wannan aiki sai ya koma Ma'aikatar Harkokin Waje na dan takaitaccen lokaci, yayin da daga bisani aka nada shi Shugaban Protocol na Majalisar Wakilai ta tarayya daga Disamba, 1999 zuwa Yuni, 2000. Daga Yuni 2000 zuwa Mayu 2003 kuma ya yi aiki a matsayin Shugaban Ma’aikata, (Chief of Staff) a Ofishin Mai Girma Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, marigayi Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba. Ya kuma kasance memba, kwamitin fasaha na majalisar wakilai akan kasafin kudi da ofishin bincike.
Maigirma Sardauna ya halarci babban kwas na 32/2010 na Cibiyar Koyarda Tsare Tsare da Sanin Makamar Aiki (NIPSS), dake Kuru, Jos, daga February zuwa November, 2010, kuma an ba shi lambar girma ta zama memba na Cibiyar (mni).
Bayan ya yi ritaya daga aikin Gwamnatin tarayya a watan Oktoba 2017, ya dawo Hadejia da zama kuma tun lokacin zuwa yanzu yana jagorancin Kwamatin Zartarwa na Gidauniyar Cigaban Masarautar Hadejia an inda yake bada gudummawa ta fannoni dabam dabam don wanzuwar hadin kai, zama lafiya, cigaban Masarautar da al'umar ta.
Ya rike sarautar gargajiya ta BARADEN Hadejia daga Agustan 2004 zuwa Satunba na 2025. Maimartaba Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje, CON, shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, ya tabbatar wa Ambasada Haruna Ginsau, mni, sarautar Sardaunan Hadejia a ranar Asabat, 27 ga watan Satumba, 2025.
Maigirma Sardauna ya auri Hajiya Amina Hassan Hadejia a 1982 kuma Allah ya albarkace su da ‘ya’ya biyar (5). Mutum ne mai sha'awar hawan doki, kwallon kwando da ninkaya, sannan kuma ya tsunduma kansa cikin harkar noma. Ya ziyarci kasashe da dama a duniya.
No comments:
Post a Comment