Shugabanci na nufin rikon ragamar al’umma da ba su umarni da yi musu jagoranci bisa tafarkin da suka amince da shi, da tsara musu dokoki da sasanta tsakaninsu, da makamantan wadannan.
Shugabanci ta bangaren al’adun Hausawa kuwa, ya faro ne daga tsarin zaman iyali inda Maigida yake kamar Sarki a gidansa, a kullum shi ne babba, daga nan sai matarsa da sauran yaran gida. Yayin da aka samu gidaje biyu ko fiye da haka akan zabi wani dattijo a matsayin shugaba, ko kuma wani jarumi wanda ya nuna ya fi kowa sadaukantaka da jaruntaka da dauriya.
Wasu dalilai kamar halin kunci a cikin gida ko bukata irin ta tsaro ko rashin zaman lafiya, kan sa Maigida ya fitar da wasu daga cikin ‘ya‘yansa zuwa wani guri na daban, kamar gona ko garke.
Ta haka ne iyali kan yadu su yawaita su hada wani kauye.
Saboda haka ne sai a kara zabar wani shugaban da zai shugabanci wannan kauye. Wannan shi ya haifar da mukamin MAI UNGUWA kuma shi zai dinga tsara musu dokoki.
Kauye yakan bunkasa ya zama gari sosai, a sakamakon haka sai a kara zabar wani mutum a matsayin Maigari wato (Fagaci) don kula da wannan gari.
Da aka samu ci gaba kuma, garuruwa suka kara yawaita sai aka samar da mukamin Hakimi, ana ba wa Hakimi garuruwan Maigari akalla biyar don ya kula da su.
Da tafiya tai tafiya, sai aka samar da mukamin Sarki inda ake hada wa Sarki masarautar Hakimi akalla biyar ko fiye domin ya shugabance su ya kuma shimfida musu dokoki domin zaman lafiya.
A takaice dai ajin shugabannin da ke tsara dokoki a tsakanin talakawansu sun hada da Maiunguwa, da Fagaci, da Hakimi, da Sarki, don haka a tsarin zaman Hausawa komai dukiyar mutum in ba ya cikin wannan jeri to talaka ne.
No comments:
Post a Comment