DAGA IBRAHIM ADO-KURAWA
A CIKIN 'yan kwanakin nan an samu sabuwar sha'awa kan Jihadin da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya jagoranta, da nufin a haifar da gaba tsakanin Hausawa da Fulani saboda shi Bafillace ne. Wannan wani shiri ne na siyasa da ake kitsawa domin wasu 'yan siyasa na so su samu madafa a arewacin Nijeriya.
To amma wannan ba wani sabon abu ba ne, domin hatta Turawa 'yan mulkin mallaka da 'yan mishan da su ka zo daga Birtaniya sun yi wannan ƙoƙarin a farkon ƙarni na ashirin miladiyya. Turawan sun ɗauka cewa Hausawa za su mara wa shirin su na mulkin mallaka baya saboda wai sarakunan Fulani na musguna masu. Wannan wata hikima ce da Rabaran Walter Miller ya kitsa masu, kamar dai yadda E.A. Ayandele ya ruwaito a maƙalar sa mai taken, "The Missionary Factor in Northern Nigeria, 1870-1918" wadda aka buga a cikin mujallar 'Journal of the Historical Society of Nigeria' III:3, a cikin 1966.
A cikin 'yan shekarun nan, an samu ƙaruwar farfagandar ƙin jinin Fulani, musamman tun daga farkon shekarun 1990, lokacin da Cif Bola Ige ya yi wasu rubuce-rubucen ƙiyayya a cikin jaridar 'Nigerian Tribune', wanda wannan abu duk shirin siyasa ne.
Wani abu da ke haifar da wannan yekuwar ƙiyayyar shi ne ƙaruwar hare-haren ta'addanci da wasu ɓatagarin Fulani makiyaya su ke aikatawa.
A safiyar yau (14 ga Disamba, 2021), na ci karo da wani rubutu na Zaharaddeen Ibrahim Kallah mai taken "Tsakanin Jihadin Fulani a Ƙasar Hausa, Mulkin Mallaka Da Rashin Tsaro a Yau", wanda mujallar Fim ta wallafa kuma ta yaɗa ta hanyar intanet. A cikin rubutun, an ruwaito inda babban yaya na da na ke girmamawa, wato Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya ce Jihadin da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya jagoranta shi ne mulkin mallaka na farko da aka yi a ƙasar Hausa, sannan na biyun shi ne mulkin mallaka da Turawan Birtaniya su ka yi a ƙarni na ashirin.
Wannan magana irin ta ce 'yan mulkin mallakar Birtaniya su ka riƙa yaɗawa a lokacin da su ka mamaye ƙasar nan. Sun yi iƙirarin cewa ba su da bambanci da Fulanin da su ka jagoranci Jihadi a ƙarni na 19.
To amma dukkan masanan tarihi da ake girmamawa sun yi watsi da wannan iƙirarin domin bai da makama a tarihi, sai dai kawai a siyasar Turawa ta tsarin mulkin mallaka. Babu wata makama ta ilimi da za a riƙe a kan haka, to amma dai tunda wani mutum mai ilimi ne ya yi zancen, na ga ya zama wajibi in yi masa wannan taƙaitaccen martanin.
Nazarce-nazarce da dama da manyan masanan tarihi irin su Abdullahi Smith, Jacob Ade-Ajayi, Murray Last, Bala Usman da Ahmad Kani su ka yi sun yi fatali da tunanin da masanan tarihi masu nuna wariyar launin fata su ka yaɗa, wato irin su M.G. Smith da jami'in mulkin mallaka ɗin nan mai suna H.A.S. Johnston, cewa wai Jihadin da aka yi Fulani ne kaɗai su ka aiwatar da shi. Saboda haka, babu buƙatar in maimaita dukkan maganganun. To amma zan kafa hujjar cewa ba a yi Jihadi da niyyar a yi mulkin mallaka don a ɗebi dukiya ba kamar yadda Turawan Birtaniya su ka yi a ƙarni na 20, an yi shi ne domin a farfaɗo da addinin Musulunci sannan a haɗe kan al'umma a ƙarƙashin inuwar adalci guda ɗaya.
Farfesa Ade-Ajayi ya yi rubutu kan yadda aka haɗe al'ummar. A cewar wannan sanannen masanin tarihin, Jihadin da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya jagoranta shi ne “jigo mafi muhimmanci a tarihin mu” tun daga ƙarni na 19 saboda ya fara ɗauko "hanyar da za a bi a hankali a hankali don a haɗe kan al'umma". Ya ƙara da cewa Jihadin “shi ne abu na farko da ya faru a zahiri mai muhimnancin da ya shafi dukkan ƙasa a tarihin mu. Da wuya a samu wani sashe na ƙasar nan wanda ya tsira daga tasirin sa. Tasirin sa babba ne matuƙa”. Dalilin haka shi ne ya shafi “al'ummomi daban-daban kamar su Yarabawa, Igala da Kanuri. Kuma ma abu mafi muhimmanci, ya fara ɗinke tarihe-tarihen Fulani, Hausawa, Nufawa, Jukunawa da sauran al'ummomi da dama a wurin da yanzu ake kira Arewacin Nijeriya” (duba littafin JFA Ajayi, wato 'Milestones of Nigerian History', 1980).
Jihadin ya kafa Daular Halifanci wadda ta ɗoru a kan manufofin adalci ga jama'a a bisa hukunce-hukuncen Islama, waɗanda Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya karantar da ɗaliban sa da jama'ar ƙasar Hausa baki ɗaya. 'Yan Jihadin sun samar da al'umma ta kowa da kowa ba tare da nuna wariya ba.
Gwamna Kayode Fayemi ya yi wata magana a kan ƙin raba kan jama'a tare da kawo shawarar haɗewar ƙasa, kuma daga nasihohin Shehu ya samu wannan tunanin. Ya rubuta cewa: "Shehu Ɗanfodiyo ya faɗa a cikin littafin sa na 'Bayan Wujub al-Hijra' cewa, 'Ɗaya daga cikin hanyoyi mafi sauri na wargaza ƙasa ita ce a nuna an fi son wata ƙabila a kan wata ko kuma a nuna wa wani gungun mutane so a kan wani'." Kayode Fayemi ya yi wannan tsokacin ne a shekarar 2020, cikin wani jawabi da ya gabatar a Gidan Arewa a Kaduna mai taken "Unfinished Greatness: Towards A More Perfect Union in Nigeria".
Irin wannan mulkin adalcin ne ya sanya Daular Usmaniyya ta zamo mafi girma da tsaruwa tare da albarka a dukkan yammacin nahiyar Afrika kafin zuwan Turawa (Dubi littafin P. Lubeck mai taken 'Islam and Urban Labour in Northern Nigeria', Cambridge, 1986, shafi na 12, da littafin J. Iliffe mai taken 'Africans: The History of A Continent', Cambridge, 1995, shafi na p. 171).
Matafiyin nan da ya zagaya duniya kafin zuwan Turawa, wato Clapperton, ya bada labarin yadda Daular Usmaniyya ta ke a lokacin da ya kawo ziyara a yankin a zamanin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. A labarin, ya bada tabbacin ana zaman lafiya da juna a ƙasar, inda ya ce: “Ana matuƙar aiki da dokokin Alƙur’ani a zamanin sa (shi Bello) ... ta yadda a duk ƙasar, in dai ba yaƙi ake cikin yi ba, ana bin dokoki sosai yadda ɓata baki ne a ce mace za ta iya tafiya da kayan zinari a bisa kan ta daga wani sashe na garuruwan Fulanin zuwa wani” (duba Clapperton, H., 'Journal of a Second Expedition into the Interior of Africa', London, 1829, p. 206).
Da Turawa su ka mamaye Afrika, sun yi wa kusan ko'ina mulkin mallaka. Daular Usmaniyya da sauran ƙasashen sarakai da al'ummomi waɗanda daga bisani su ka zama Nijeriya su na cikin yankin da Turawa su ka yi wa kan su kaso. Saboda haka ta yaya za a ce ƙasa ta na matsayin mai cin gashin kan ta, kuma jama'ar da ke cikin ta ne su ka kafa ta, sannan a ce mulkin mallaka ne? Wannan kawai wani tunani ne da tsarin ilimin da Turawa su ka jawo ya cusa a cikin zukatan 'yan boko saboda su na so su kawo hujjar danniyar da Turawan Birtaniya su ka yi.
Masu mulki a Daular Usmaniyya ba wasu baƙi ba ne su ka zo daga waje. Wasun su, kakannin kakannin su sun taso ne daga yankin Futa na ƙasashen Gini, Senegal da Mali sama da shekaru ɗari huɗu kafin Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, su ne su ka kafa Daular Usmaniyya.
Turawan da su ka ƙwace Afrika kuwa, su na da al'adun su daban. Baƙi ne a Afrika. Alaƙar da ke tsakanin Fulanin da su ka yi Jihadin da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya jagoranta da Hausawa ta fi bambancin da ke tsakanin su ƙarfi. Dukkan su dai Musulmi ne, su na sanya tufafi iri ɗaya, su ci abinci iri ɗaya, su yi auratayya da juna, sannan kuma Jihadin nan ya maida harshen Hausa gama-gari a dukkan yankunan daular. Idan ka ɗebe Fulani mazauna daji waɗanda ba su bin addini, Fulanin da ke zaune a garuruwa da birane sun zama Hausawa a wajen al'adun su saboda sun rungumi yawancin al'adun Hausawan. Shin wannan shi ne za a kira mulkin mallaka?
Farfesa Mahadi Adamu ya yi bincike tare da rubuta yadda wannan cuɗanyar da haɗewar ta kasance har ma ya ce dukkan Arewacin Nijeriya ta zama Bahaushiya (Mahadi Adamu cikin laccar 'Inaugural' da ya gabatar a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, cikin 2011, mai taken "The Major Landmarks in the History of Hausaland").
A yau a Nijeriya, har ma akwai masu faɗin Hausa-Fulani, to me ya sa? Dalilin haka shi ne saboda saboda zurfin cakuɗewar da mutanen su ka yi da kuma cewa ƙabilanci wani abu ne da ake ƙirƙira.
Saboda samun galabar siyasa, 'yan siyasa su kan ƙirƙiri sabon ƙabilanci. Kafin zuwan Turawa a
yankin da ya zama Nijeriya, yawancin lardunan mulki da garuruwan an gina su ne bisa faɗin ƙasa, ba bisa ƙabilun da ke cikin su ba. Amma a yadda Turawa su ka tsara gundumomin su ne aka samu tunanin ƙabilanci har ma daga baya ƙabilu su ke zancen wai akwai ƙasashen da su ka gina mulkin su bisa ƙabilanci kafin zuwan Turawa. Sai ya kasance abu mai wahala a bambance tsakanin yadda za a gane al'ummomin Arewacin Nijeriya, wanda hakan ya sa da yawa su ke kallon dukkan mutanen yankin a matsayin Hausawa.
Amma daga baya sai 'yan siyasa su ka lura da cewa lallai ne su gina siyasar bambancin ƙabila domin su samu madafa a Arewa ta hanyar dabarun raba kan jama'a. Saboda haka tilas ne a bambance Hausawa da Fulani don a zuzuta siyasar ɓangaranci a yankin.
Zancen cewa Fulani ne su ka fara yin mulkin mallaka ya ƙara rincaɓewa ne saboda bala'in nan na 'yan kidinafin da 'yan bindiga waɗanda yawancin su Fulani ne marasa addini kuma makiyaya. Saboda haka wannan ya yi daidai da farfagandar cewa waɗannan ɓatagarin Fulanin su na faɗa ne domin 'yan ƙabilar su su mamaye tare da ƙwace yankunan wasu, sannan ana amfani da ta'addancin da su ke yi a dazuzzukan Jihar Neja a matsayin misali. An san cewa Fulani makiyaya masu shiga harkar kashe-kashe da kidinafin manyan masu aikata laifi ne, to amma fa ba sun shiga wannan harkar ba ne domin ƙaruwar 'yan'uwan su Fulani. Saboda haka ɗaukar su a matsayin “Fulani”, wata farfagandar ƙiyayya ce kawai.
Batun kawo Jihadin Shehu a matsayin aikin mulkin mallaka wani sabon yunƙuri ne na ciyar da ajandar Turawan mulkin mallaka gaba don a haifar da rashin jituwa a tsakanin jama'a da kuma ajandar 'yan siyasar ƙabilanci masu son su wargaza Nijeriya.
Fulani makiyaya da ke aikata laifuffukan kidinafin da kashe-kashe mutane ne da gwamnatin Nijeriya ta haifar, kuma ba su da wata alaƙa da Daular Usmaniyya ko Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Saboda haka, danganta su da wani abu wai mulkin mallaka na farko wata farfagandar ƙiyayya ce.
Shekaru arba'in da su ka gabata, da wuya ka ji an yi fashi da makami a arewacin Nijeriya. Shekaru ashirin da su ka gabata, ba a cika yin kidinafin a wannan sashe na Nijeriya ba. Me ya jawo abin har ya ƙazance a yanzu? Daga ina waɗannan laifuffukan su ka samo asali? Shin ana danganta sauran ayyukan laifi da ake aikatawa a Nijeriya da wasu ƙabilu su kaɗai? Me ya sa aka fara farfagandar ƙin jinin dukkan Fulani tare da ƙoƙarin raba Fulani da Hausawa a yanzu?
Idan mun samu amsoshin waɗannan tambayoyin, sannan ne za mu iya warware ɓoyayyiyar manufar siyasa da ke lulluɓe a cikin wannan al'amari.
* Malam Ibrahim Ado-Kurawa, wanda masanin tarihi ne kuma Editan 'Nigeria Year Book and Who is Who', mazaunin Kano ne.