Saturday, 10 October 2020

HAUSA DA TURANCI

Yafiya = Forgiveness
Tausayi = Pity
Tausayawa =Sympathy
Tausasawa = Compassion
Sassauci =Leniency
Rangwame = Clemency
Rahama =Mercy
Kau da kai = Overlooking
Juyayi =Empathy
Jajantawa = Condolence
Haƙuri =Patience
Alhini = Mourning
Alfarma =Favor
Afuwa =Pardon
Acceptance = Karɓuwa
Zaman lafiya = Peace
Yarjejeniya = Treaty
Sasantawa = Conciliation
Manta baya = Magnanimity
Lumana = Peacefulness
Lafawa = Pacification
Kwanciyar hankali = Tranquility
Juriya = Forbearance
Ijma’i = Consensus
Haƙuri da juna = Tolerance
Fahimtar juna = Understanding
Alƙawari = Pact

Ta’addanci = Terrorism
Samame = Incursion
Rashin-tausayi = Brutality
Rashin imani = Ruthlessness
Mamaya = Invasion
Hari = Raid
Harbi = Firing
Gaba = Hostility
Fir’aunanci = Savagery
Fatattaka = Chase
Farmaki = Attack/Assault
Dirar-mikiya = Blitz
Bara = Charge
Azabtarwa = Cruelty

Artabu = Combat
Batakashi = Shoot-out
Ɓarin-wuta = Shelling
Faɗa = Fight
Fitina = Skirmish
Gumurzu = Dogfight
Jahadi = Crusade
Karon-batta = Clash
Rikici = Conflict
Taho-mu-gama = Ram
Tarzoma = Riot
Tashin-hankali = Violence
Tawaye = Rebellion
Yaƙi = War
Zubar da jini = Bloodshed

Gaba-da-gaba = Confrontation
Kai-hannu = Exchange blows
Kai-ruwa-rana = Tussle
Karo = Encounter
Kokuwa = Duel
Rigima = Dispute
Rikitarwa = Controversy
Ta-da-jijiyar-wuya = Altercation
Ta-da-ƙayar-baya – Intimidation
Taƙaddama =Contention
Tashin-tashina = Brawl
Tirjiya =Resistance

Cacar-baki = Shouting match/Exchange words
Gardama = Scuffle
Hatsaniya = Quarrel/Row
Hayaniya = Squabble
Kyara = Bullying
Musu = Argument
Sa-in-sa = Altercation
Tsangwama = Oppression
Rabuwar-kai = Fray
Ƙyamata = Resentment
Zaman-doya-da-manja = Rancor
Jayayya = Tug-of-war

Anger = Fushi
Animosity = Ƙullaliya
Antagonism = Rashin jituwa
Bitterness = Ɗacin-rai
Disagreement = Rashin daidaito
Discord =Saɓani
Distrust = Rashin yarda
Enmity = Ƙiyayya
Envy =Kishi
Grievance =Damuwa
Grudge = Riƙo
Hate = Tsana
Malice = Hassada
Misunderstanding =Rashin fahimta

Adulthood = Manyanta
Babyhood = Jarirantaka
Boyhood = Yarinta
Brotherhood = ‘Yan-uwantaka
Childhood = Yarinta
Eldership = Dattijantaka
Friendship = Abota/Ƙawance
Girlhood = Yarinta
Manhood =  Mazantaka
Oldage = Tsufa
Sisterhood = ‘Yan-uwantaka
Womanhood = Matanta
Youth = Ƙuruciya

Bakace = Sifting
Ɓarza = Crushing
Daddage = Mashing
Daka = Pounding
Dandaƙe = Crunching
Kwankwatse = Crushing
Marmasawa = Crumbling
Niƙa = Milling/Grinding
Shiƙa = Winnowing
Surfe = Chaffing
Sussuka = Threshing
Tankaɗe = Sieving
Tata = Filtering
Tsinta = Picking
Bakace = Sifting
Ɓarza = Crushing
Daddage = Mashing
Daka = Pounding
Dandaƙe = Crunching
Kwankwatse = Crushing
Marmasawa = Crumbling
Niƙa = Milling/Grinding
Shiƙa = Winnowing
Surfe = Chaffing
Sussuka = Threshing
Tankaɗe = Sieving
Tata = Filtering
Tsinta = Picking

Anatomy = Yanayin gaɓɓan jikin
Antibacterial = Yaƙar ƙwayar bacteria
Antibiotics = Maganin kashe ƙwayoyin cuta
Arthritis = Amosalin gaɓɓai
Gynecology = Ilimin mahaifa
Histocompatibility = Dacen-jin
Laxative =Kasayau
Mortality = Yiwuwar mutuwa
Physiology =Yanayin jiki
Tumor = Ƙari

Sputum = Kaki
Sneezing = Atishawa
Pain = Zogi/Raɗaɗi
Nasal swab = Kwarfatar hanci
Nasal Congestion = Cushewar hanci
Mucus = Majina/Gamsai
Infect = Harba
Flu = Mura
Fever = Masassara/Zazzaɓi
Cell = Tantanin halitta
Bronchitis = Mashaƙo
Addiction = (Zamewa) Jaraba
Acute = Mai muni

Available = Mai samuwa
Liable = Ɗaukar alhaki
Memorable = Abin tunawa
Noticeable = Mai ban-mamaki
Objectionable = Abin ƙi
Permissible = Halattacce
Pliable = Mai tanƙwasuwa
Portable = Mai ɗaukuwa
Possible = Mai yiwuwa
Reliable = Tsayayye
Visible = Mai ganuwa
Vulnerable = Mai rauni

#MAGNITUDE
Faɗi = Breadth/Width
Girma = Size
Gwargwado = Ratio
Iyaka = Limit
Ƙarƙari = Reach
Kauri = Thickness
Kima = Rate
Kini = Equal
Maƙura = Extreme
Mataki = Extent
Matsayi = Stage
Matuƙa = Maximum
Nauyi = Weight
Siranta = Thinness
Tamka = Parallel
Tsayi= Height
Zurfi = Depth 

Antivirus = Manhajar kare cutukan kwamfuta
Antivaxer = Mai adawa da rigakafi
Antiseptic = Kare ɗaukar cutuka
Antidote = Makari
Anticrime = Yaƙar manyan laifuka
Antichrist = Magabcin Kristi
Anti-venom = Kardafi
Anti-party = Zagon ƙasa ga jam’iyya
Anticorruption = Yaƙar almundahana

Consequently = Sakamakon haka
Daily = Duk rana
Explicitly = A sarari, Ƙuru-ƙuru
Formally = Bisa ƙa’ida, A hukumance
Fortunately = Abun birgewa
Happily = Abin farin ciki
Only = Kacal, Kaɗai, Kawai
Publicly = A bainar jama'a, A fili
Sufficiently = A wadace
Timely = A kan lokaci

Agara = Achilles tendon
Allon kafaɗa = Shoulder blade
Damtse = Upper arm
Dunduniya = Sole
Haƙarƙari = Rib
Hammata = Armpit
Ijiya = Eye
Karan hanci = Nose bridge
Kunci = Cheek
Kwankwaso = Pelvis
Kwiɓi = Body side
Ƙugu = Hip
Muƙamuƙi = Jaw
Sha-raɓa = Calf
Tsintsiyar-hannu = Arm

Centre for Disease Control =Hukumar Daƙile Cutuka
Coronavirus = Ƙwayar cutar numfashi
Cough =Tari
#COVID19 = Murar mashaƙo
Social distancing = Ƙauracewa juna
Face mask =Takunkumi
Gloves = Safar hannu
Quarantine = Keɓancewa
Self-isolation =Killace-kai
Sore throat = Maƙaƙin maƙoshi

1. Tsara=Peer/Array
2. Tsare=Guard/Prevent
3. Tsari=System/Refuge
4. Tsaro=Security
5. Tsaru=Planned
6. Tsere=Race/Flee
7. Tsira=Survive
8. Tsire=Kebab/Pike
9. Tsiri=Peak/Geyser
10.Tsiro=Shoot
11. Tsoro=Fear
12. Tsura=Pure/Unmixed
13. Tsure=Scared
14. Tsuro=Sprout
15. Tsuru=Timid

To this day = Har zuwa yau
Sooner or later = Ko ba-jima ko ba-daɗe
On your own = A kan kanki
On the other hand = A gefe guda
On the contrary = A akasin haka
In place of = A madadin
In a nutshell = A taƙaice
At the same time = A lokaci guda
At the heart of = Kan-gaba

#Hausa troponyms for STEALING and CON:

Almundahana = Pilfering
Bizi = Lifting
Damfara = Duping
Fashi = Robbery
Fashi da makami = Armed robbery
Ƙwace = Snatching
Sane = Pickpocketing
Sata = Stealing
Sibaranye = Filching
Taɓargaza = Squander
Wala-wala = Swindling
Wawura = Looting 

As long as = Muddin
As such = Don haka
Directly – Kai-tsaye
Hopefully = Ana fatan
In addition = Bugu da ƙari
In fact = A zahiri
Mainly = Galibi
Shortly = Jim kaɗan 
Strenuously = Yi tuƙuru
Suddenly = Kwatsam
Unfortunately = Abin takaici
Usually = Yawanci
Voluntarily = A son-rai

All = Duka
Alliance = Ƙawance
Altogether = Gabaɗaya
Combination = Haɗaka
Concentration = Cincirundo
Crowd = Cikowa
Entire = Ɗaukacin
Entirety = Rankatakaf
Mass = Dandazo
Multiple = Mamako
Multitude = Tari
Thousands = Dubun dubata
Total = Jimilla
Totality = Kafatani
Union =Gamayya

Currently = A halin yanzu
Evenly = Daidai wadaida
Indirectly = A kaikaice
Preferably = Zai fi dacewa
Provisionally = Ƙwaryakwarya
Rarely =Da wuya
Regularly = A kai a kai
Respectively = Bi da bi
Separately = A rarrabe
Similarly = Hakazalika
Thereby = Wato kenen
Typically = Yawanci

Immediately = Nan da nan
Inevitably = Babu makawa
Instantly = Yanzun nan
Luckily = Sa'ar lamarin
Mostly = Galibi
Normally = A yadda aka saba
Obviously = Babu shakka
Periodically = Lokaci-lokaci
Permanently = Dindindin
Possibly = Mai yiwuwa
Practically = A aikace

Accordingly = Dangane da haka
Actually = A zahiri
Alternatively = A madadin haka
Carefully = Da takatsantsan
Efficiently = Cikin ƙwarewa
Entirely = Ɗaukacin
Equally = Hakanan
Exclusively = A ƙeɓance
Generally = A bai-ɗaya
Hardly = Da wuya
Honestly = a ƙashin gaskiya

Already = Ya rigaya
As soon as/Once = Da zarar
Besides = Kuma ma
But = Amma/Sai dai
By the way = Af
Even = Hatta
If = Idan
Not even = Balantana
Often = Galibi/Sau da yawa
Since = Tun da
So long = Matuƙar
Therefore = Sabili da haka
To be sure = Duk da dai
Yet = Duk da haka, Tukuna

Commute = Je-ka-ka-dawo
Ferry = Fito
Haulage = Dako
Import-Export = Shige-fice
Journey = Bulaguro
Shipping = Dakon kaya
Shuttle = Kai-komo
Tour = Zagaye
Trafficking = Safara
Transit = Jigila
Transport = Sufuri
Travel = Tafiya
Trek = Tattaki
Visit = Ziyara

Source : Hausa Language Hub