Tuesday, 31 December 2019

GALADIMAN HADEJIA ALH. YUSUF USMAN, MON

An haifihi a garin Hadejia a Shekarar 1902 ya fara karatun Allo yana dan shekara 4 domin samun ilimin Addini. Lokacin da ya cika shekara 6 an sashi a (Dallah Elementary) a Shekarar 19010 domin samun ilimin Boko. Ya kammala wannan makaranta a Shekarar 1914. Bai tsaya a nan ba ya cigaba da karatunsa ya halarci (Provincial School Kano). Bayan kammala wannan makaranta, sabida jajircewa irin tasa ya sake halartar (Councilors Course Institute of Administration, Zaria) ya halarci Kwasa-Kwasai na karawa juna Ilimi masu tarinyawa.

*  Ya zama Malamin Makaranta a (Dallah Elementary a Shekarar 1915
* An bashi Mukamin Wakilin Sana'a a Ashekarar 1918 zuwa 1945
* An Nadashi Sarautar Sarkin Ban Hadejia Hakimin Kafin-Hausa a Shekarar 1945. Wanda Sarkin Hadejia Usman ya Nadashi.
* An Nadashi Galadiman Hadejia a Shekarar 1949 Wanda Sarkin Hadejia Usman ya Nadashi
* An Zabe shi a karo na Farko a Matsayin Dan Majalissa wato (Member House of Assembly) Mai Wakiltar Hadejia (North East) a Shekarar 1956 a karkashin Tutar Jam'iyyar N.P.C Ya fara zamansa na Majalissa a Jihar Lagos kana daga bisani aka dawo Kaduna.
* An sake Zabarsa a karo na Biyu a Matsayin Dan Majalissa (Member House of Assembly) Mai Wakiltar Hadejia (North East) a Shekarar 1961 a karkashin Tutar Jam'iyyar N.P.C sabi da irin aikin da ya yi a Hadejia wannan ta sake bashi dama jama'a suka sake zabarsa a karo na biyu.
A wannan lokacin an bashi Matsayin N.A Councilor) mai kula da Lafiya (Hospital), Gidan Yari (Prison), 'Yan Doka (Police) Sannan kuma shine Wakilin Ayyuka wato (Supervisor of Works and Districk Head) duk wannan suna karkashin ikonsa.
* An bashi Lambar Girma ta Kasa wato MON wacce Turawa suka bashi a Jihar Kaduna. Lambar na dauke da wannan rubutun (Civil Service) Federal Republic of Nigeria Alhaji Yusuf Usman For Distinguished Public Service.
* Ya yi Sarauta da Sarakuna guda biyu Sarkin Hadejia Usman da Sarkin Hadejia Alhaji Haruna.
* Allah ya masa rasuwa a Shekarar 1974 Allah ya ji kansa da rahama Allah ya gafarta masa zunubansa, Allah ya sa Aljanna ce makoma a gareshi. Allah ya kara daukaka zuri'arsa baki daya. 

Mu hadu a Kashu na Biyu