Kalmar Ma'aji a kasar Hadejia tsohuwar kalmace wacce aka dade ana amfani da ita, wannan kalma tana nufin Ajiya, a lokacin yake-yake a kasar Hadejia Sarakunan Hadejia suna fita yake-yake kuma su kama bayi. A duk lokacin da suka fita irin wannan yake-yake suna tahowa da bayi masu yawan gaske wanda suka hada maza da mata ga kuma ganima mai tarin yawa. Suleiman Ginsau
A wannan lokaci Sarakuna sai su sami wani amintacce daga cikin Yaransu sai su bashi Ajiyar wannan bayi da aka kama a wajen yaki domin yana kula da su wajen Ci da Sha da kuma aikace-aikace da-ban-da-ban to wannan mutumin da aka bawa Ajiyar wannan bayi sai mutane suke masa lakabi da sunan Ma'aji. To a wannan zamani shi wannan Ma'aji bashi da wani gida ko wani waje da inda zai wannan bayi ya kulle sai da kawai ya taho dasu Unguwar da yake ya dauresu a bakin kofar gidansa wasu kuma ya daure su a wurare da ban a cikin Unguwa. Ta hake ne aka samu sunan Unguwar Ma'aji a Hadejia. Wannan Unguwa a halin yanzu tayi rassa wanda hakan yasa aka samu wasu Unguwanni a jikinta kamar irinsu:-
Unguwar Sabon Garu
Unguwar Dukawa
Unguwar Maga Hudu
Unguwar Madaki
Da dai sauransu kuma duk wadannan uguwanni suna da tarihi na abin mamaki.
Amma bayan zuwan Turawan mulkin mallaka sai suka karawa abin armashi sannan suka sake fitowa da wani sabon tsari na MATAWALLE. Yana da mutukar alfanu a fadi aiyukan Ma'aji da aiyukan Matawalle sannan a fadi ban-banci tsakanin Ma'aji da Matawalle. Sai babu lokaci. Ga sunayen wasu daga cikin Ma'aji:-
1. Ma'aji na Farko a Hadejia (Mal. Hassan)
2. Ma'aji na Biyu a Hadejia (Mal. Khaila)
3. Ma'aji na Uku (Mal. Kasim)
MATAWALLE.
1. Mal. Usman
2. Mal. Amadu
3. Mal. Saleh
Suleiman Ginsau