Mai martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Hadejia ya bude karatun tafsir na watan Ramadan a gidan kurkuku na Mawadaci. A jawabinsa mai martaba sarki ya bukaci masu abin hannu dasu tallafawa wadanda suke zaune a gidaje yari domin tallafawa rayuwarsu Ya ce mazauan gidajen yari suna bukatar tallafi Sarkin ya kuma duba irin kayayyakin da daurarru suke sarrafawa.
A jawabinsa wakilin shugaban gidan yari na jiha ASP Adam Muhammad Bello ya yabawa sarkin bisa damuwarsa ga gidan yarin.
Wannan ziyarar zata iya zama ta farko a cikin wannan shekara ta 2017, Idan bamu manta ba An bude Prison din Hadejia a watan maris cikin shekarar 1908 A zamanin Sarkin Hadejia Abdulkadir bayan an dauketa daga Lungun Galamu kenan. A watan Janairu na 2016, hukumar gidan yari ta kasa ta mallakawa Masarautar Hadejia wannan Tsohuwar prison dake Kofar Gwani a Hadejia.
Ismaila A Sabo